Nach Genre filtern
RUMFAR AFRIKA | TARE DA DR. SANI MOUSSA MAGAWATA
- 37 - 36 | MULKIN TRUMP DA NAHIYAR AFRIKA | DR. RIYA'UDDEEN ZUBAIR MAITAMA | RUMFAR AFRIKA PODCAST HAUSAMon, 25 Nov 2024 - 2h 36min
- 36 - 35 | KOMAI DA RUWANKA | SHEIKH MUSA YUSUF ASADUSSUNNAH | RUMFAR AFRIKA PODCAST HAUSASun, 13 Oct 2024 - 3h 40min
- 35 - 34 | ABINDA BAKU SANI BA GAME DA RAYUWAR SHEIKH UTHMAN ABUBAKAR ABUL-HUSNAIN | RUMFAR AFRICA PODCAST
WANNAN TATTANAWA ITACE IRINTA TA FARKO A SHIRIN RUMFAR AFRIKA PODCAST DA KOWANE ZAI SAMU BANGAREN DA YA DACE DA SHI A FANNI DABAN-DABAN NA RAYUWA, IYAYE MATA DA MAZA (TARBIYYA), MALLAMAN ADDINI, MALAMAN ISLAMIYYA, DALIBAN ILIMI, ‘YAN BOKO, MATASA, DA KUMA KUNGIYOYIN ADDINI (IZALA), BABBAN BAKON YA SHAHARA WAJAN BADA LAKANIN ADDU’A KO ME YASA YAKE YAWAN YIN HAKA? BABBAN BAKONMU SHI NE: SHEIKH UTHMAN ABUBAKAR ABUL-HUSNAIN, MALAMAIN ADDNIN A KADUNA NAJERIYA, TARE DA MAI GABATARWA: DR. SANI MOUSSA MAGAWATA. #podcast #hausa #kaduna #izala BATUTUWAN SHIRIN:- 00:00 BUDE SHIRIN 01:56 GABATARWA 06:09 WANE NE MALAM SANI A MAJALINSIN MALAM? 27:45 A INA MALAM YA FARA KARATU, A INA YA TASO, ALAKARSA DA IYAYENSA? 01:06:21 BOKO DA KARATUN ADDINI 01:10:58 ZUWANA JAMI’AR AZHAR DA MAHAIFINA 01:20:48 MALAMAIN ADDINI BAYAN BOKO MAI ZURFI 01:23:09 ABIN DA YASA BAN DAMU DA KWALIN SHAHADA BA TA KARTUN ADDNI 01:26:24 FANNIN DA NAFI SO DA KWAREWA A ILIMIN ADDINI 01:30:00 MALAMAINA NA ZAURE DA NA YI KARATU SOSAI A WAJAN SU 01:36:17 MALAMAINA NA ZAURE DA NA TASIRANTU DA SU, WANE NE MALAM ALGARKAWI? 01:48:46 LITTAFIN DA NAFI SHAKUWA DA SHI 01:53:14 TUSHEN GINA INGANTACCIYAR TARBIYYA 02:02:38 MANHAJINA NA KOYARWA DA NA DA’AWA 02:06:56 SHAWARA GA KUNGIYOYI MASU FITA WA’AZIN KASA A GARURUWA 02:13:10 LITATAFAN DA MUKA SAUKE 02:15:55 WANE NE MAGAJIN MALAM A KARANTARWA? 02:24:51 KARANTARWA DA YI A AIKACE (ATTATBEEK) 02:27:23 USLUBIN BADA LABARAI A KARANTARWATA 02:35:03 ABIN DA YASA NAKE BADA LAKANIN ADDU’A 02:42:46 AYUKKAN DA MUKE YI A CIBIYARMU BAYAN KARANTARWA 02:44:37 TAMBAYAR DA TA GIRGIZANI 02:46:38 ALAKAR MALAMAI DA AL’UMMA 02:51:46 RUFE SHIRIN
Sun, 29 Sep 2024 - 2h 54min - 34 - 33 | DALILIN DA YASA NA BAR IZALAR JOS BAYAN NA DAWO DAGA MADINA | DR. MUH'D TUKUR ADAM AL-MANAR | RUMFAR AFRIKA PODCAST
SHIRIN RUMFAR AFRIKA PODCAST HAUSA "TARE DA DR. MUHAMMAD TUKUR ADAM AL-MANAR", KU BIYO MU DON JI DA GANIN TATTAUNAWAR DA MUKA YI DA BABBAN BAKON NAMU A BANGARORI DABAN-DABAN NA RAYUWA KAMAR HAKA:- - ALAKAR KIWO DA JAGORANCIN MUTANE. - MATSALAR MANOMA DA MAKIYAYA. - HIJIRAR MALAMAI ZUWA WASU JAHOHIN DAGA JAHOHINSU NA ASALI. - ALAKAR SHI DA TSOHON GWAMNAN JIHAR KADUNA MALAM NASIRU EL-RUFA'I. - ALAKARSA DA KUNGIYAR IZALA TA JOS, ME YASA YA BAR GUNGIYAR DUK DA ITA TA RENE SHI? - MATSALAR AL-UMMA DA MASU JAGORANCI NA SIYASA. - MANHAJINSA NA KOYARWA DA KUMA DA'AWA. - AL-UMMA DA MALAMAI SUWAYE MASU LAIFI? - CIBIYAR AL-MANAR DA TASIRINTA A CIKIN JIHAR KADUNA…DS
#podcast #hausa #kaduna #izala
BUTUTUWAN SHIRIN:
00:00 BUDE SHIRIN
01:50 GABATARWA
04:31 YANAYIN ZAFI DA SANYI DA DAMANA, TASIRINSU A KARANTAWAR DA DA’AWA
10:30 KIWON DABBOBI, YA KARA MIN IYA JAGORANCIN MUTANE
38:00 ALAKAR MANOMI DA MAKIYAYI
48:20 HJIRAR MALAMAI DAGA JIHOHINSU ZUWA WASU JIHOHI, AMFANINSA DA ILLARSA
52:13 DALILIN DA YASA NA BAR IZALAR JOS...
01:05:01 A HAKA NAJE JAMI’AR MADINA DAGA JOS, DA KUMA RAYUWATA A MADINA
01:25:26 ASALIN SUNAN CIBIYAR AL-MANAR DA TARHIN KAFATA DA KUMA AYYUKANTA A KADUNA
01:30:27 TSARIN DA NA DAUKO NA GAYYATAR MALAMAI DUK WATA A CIBIYAR AL-MANAR
01:35:06 ALAKATA DA TSOHON GWAMAN MALAM EL’RUFA’I
01:38:25 ABINDA MINBIRI YAKE NUFI A WAJENA
01:39:27 ALAKAR MUTANE DA MALAMAI SUWAYE MASU LAIFI?
01:43:35 SHIN MALAM YANADA RUBUCE-RUBUCE
01:44:05 NASIHA ZUWA GA DALIBAN ILIMI
01:45:18 NASIHA ZUWA GA IYAYE
01:45:45 NASIHA ZUWA GA MAHUKUNTA ‘YAN SIYASA
01:46:34 RUFE SHIRIN
Sun, 08 Sep 2024 - 1h 47min - 33 - SHIRI NA MUSAMMAN MATSALAR MAL. MAGAWATA A SHIRIN RUMFAR AFRIKA PODCAST HAUSA
SHIRIN NA SAMMAN YA TATTAUNA IRIN WAINAR DA AKE TOYAWA A BAYAN FAGEN SHIRIN RUMFAR AFRIKA PODCAST, DA AMSA WASU DAGA CIKIN TAMBAYOYIN MASU KALLO A DANDALINMU NA YOUTUBE.#podcast #hausa #africa BATUTUWAN SHIRIN: 00:00 BUDE SHIRIN
01:08 MANUFAR SHIRIN RUMFAR AFRIKA
07:36 YADDA AKE SHIRYA SHI, DA KUMA ZABEN BAKIN SHIRIN
08:50 TSARIN GUDANAR DA TATTAUNAWA DA BAKI A CIKIN SHIRIN12:24 YADDA AKE SAMUN BAKI
14:32 ME YASA KAKE TAMBAYOYIN KEKE-DA-KEKE?16:24 BANBANCIN TATTAUNAWA DA BAKI MALAMAI
17:23 NAU’UKAN TATTAUNAWA DA BAKI
18:48 MALAM MAGAWATA KA RAGE WASA, AMMA SHIRIN YANA KYAU
19:45 DALILIN SAKA RAHA A CIKIN SHIRIN RUMFAR AFRIKA
22:56 SOJOJIN BOYE A CIKIN SHIRIN RUMFAR AFRIKA
24:47 KALUBALEN BAYAN NADAN SHIRIN
28:33 ABUBUWAN DA AKE BUKATA DAGA MASU KALLO KO SAURAREN SHIRIN
32:18 HANYA MAFI SAUKI NA KALLO KO SAURAREN SHIRIN RUMFAR AFRIKA
33:47 FADIN RA’AYINKA BA TARE DA CIN MUTUNCI BA
36:34 MASU CI DA GUMIN RUMFAR AFRIKA A SOCIAL MEDIA
39:29 MUNA MARABA DA SHAWARWARINKU
41:06 TUSHEN PODCAST
43:00 GODIYA GA HUKUMAR AFRICA TV3
43:52 GODIYA TA MUSAMMAN GA BAKIN SHIRIN RUMFAR AFRIKA
45:27 MALAM MAGAWATA YANA GODIYA
49:44 SHIRIN DA YAFI JAN HANKALI
51:06 JERIN BAKIN SHIRIN RUMFAR AFRIKA A ZANGO NA 1 DA NA 2
54:38 SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA DA MANHAJAR SAURAREN SAUTI
56:41 LAMBAR YABON DA RUFE SHIRIN
Mon, 02 Sep 2024 - 58min - 32 - 32 | BAN TABA SAMUN HAWAN JINI BA, SAI DA NAZO MASALLACIN SULTAN BELLO | DR. MUH'D SULAIMAN ADAM | RUMFAR AFRIKA PODCAST
MUN TATTAUNA BUTUTUWA MASU MAHIMMANCI DA SUKA SHAFI, GWAGWARMAYAR NEMAN ILIMI DA TA RAYUWA, MALAMAN JAMI’AR MADINA JIYA DA YAU, MALAMAN KAFOFIN SADA ZUMUNTA, ILIMI DA TARBIYYA, MU’AMALA DA WANDA KUKA SABA AKIDA KO ADDINI KO MAZAHABA, MALAMAI DA SIYASA DA ‘YAN SIYASA, ‘YAN SIYASA DA JAGORANCI NA GARI, MAFI GIRMAN MATSALOLIN ZAMNATAKEWAR AURE, MATSALAR TSARO A MAHANGAR MALAMAI, MASALLACIN SULTAN BELLO (TARIHINSA, TSARIN GUDANARWA, DA KUMA TASIRINSA A CIKIN AL’UMAR MUSULMI DAMA NAJERIYA DA YAMMACIN AFRIKA. #podcast #arewa #interview #kaduna #islam #hausa BATUTUWAN SHIRIN: 00:00 BUDE SHIRIN 01:40 SHINFIDA 06:06 TAKAITACCEN TARIHIN MALAM DA GWAGWARMAYAR NEMAN ILIMI, DA NA RAYUWA 56:05 TASIRIN JAMI’IAR MUSULUNCI TA MADINA A AL'UMMAR NAJERIYA 01:12:33 ASALIN KAFA MAKARANTAR ALBAYAN A JOS, SAU NAWA AKE KONA TA? 01:25:38 TASIRIN MALAMAN DA SUKA YI JAMI’AR MADINA JIYA DA YAU 01:32:47 MALAMAI DA MALUM-MALUM A SOSHIYAL MEDIYA 01:39:47 MATSALAR TARBIYYA DA ILIMI A KOYARWAR MALAMAI 01:42:25 YAUSHE ZAN YI MU’AMALA DA WANDA MUKA SABA DA SHI A ADDINI DA AKIDA DA MAZAHABA? 01:51:25 A WANE LOKACI NE MUSULMI ZAI YI WA DAN UWANSA MUSULMI INKARI KO RADDI? 02:04:13 YAUSHE MALAMI ZAI YI UZULA (YA KEBE) YA DENA MAGANA A KAN ABIN DA YA SHIFI AL’UMMAR MUSULMI 02:07:08 YAUSHE NE MALAMI ZAI KASANCE MAI FADA A JI A CIKIN AL’UMMA? 02:08:31 MAFI GIRMAN MATSALOLIN AL’UMMA A YAU TA BANGAREN ZAMANTAKEWAR AURE 02:26:10 HANYOYIN MAGNECE MATSALAR AURE BA TARE DA WANI NA 3 YA SHIGO BA 02:32:14 BUKUKUWAN AURENMU DA AL’ADUN TURAWA, DA TASIRINSU GA TARBIYYAR YARA DA AL’UMMA 02:40:17 HANYAR AMFANI DA WAYA DON SAMUN ZAMAN LAFIYA TSAKANIN MA’AURATA 02:45:02 MALAMAI DA SIYASA DA ‘YAN SIYASA 02:58:20 JAN HANKALI GA ‘YAN SIYASA, DON YIN JAGORANCI NA GARI 03:13:50 MATSALAR TSARO A MAHAGAR MALAMAI 03:22:21 MASALLACIN SULTAN BELLO, (TARIHI, TSARIN GUDANARWA DA KUMA TASIRINSA A CIKIN AL’UMAR MUSULMI DAMA NAJERIYA GABADAYA DA KUMA YANKIN YAMMACIN AFRIKA) 04:23:23 RUFE SHIRIN
Sat, 10 Aug 2024 - 4h 27min - 31 - 31 | ILLAR UBAN GIDA GA SIYARSA MATASA | HON. HAYATUDDEN LAWAL MAKARFI | RUMAFAR AFRIKA PODCAST
MU TATTAUNA DA BABBAN BAKON NAMU A KAN BATUTUWA MASU MAHIMMANCI DA SUKA SHAFI SIYASAR MATASA A YAU, DA KUMA HANYOYIN CIGABAN MATASA DON IYA JAGORANCI NA GARI, HAKA MUN TATTAUNA DA BAKON NAMU A KAN KALUBALEN DA YA HADU DA SHI, DA NASARORIN DA YA SAMU A LOKACINDA YA TSAYA TAKARAR GWAMNA A JIHAR KADUNA A 2023, DA KUMA ILLAR SIYASAR UBAN GIDA GA MATASA.
------------------------
BATUTUWAN SHIRIN:
00:00 BUDE SHIRIN
00:02 MUKADDIMA
00:05 TAKAITACCEN TARIHIN BAKON SHIRIN
00:22 INDA NA YI KARATUN ADDINI
00:24 ME YASA MALAMAI BASA MARAWA ‘YAN UWANSU MALAMAI A SIYASA?
00:27 MATSALOLIN DA NA GANI A MA’AIKATUN DA NA RIKE NA GWAMNATI, MU SAMMAN HUKUMAR YAKI DA RASHAWA
00:50 DAMAR DA NA SAMU TA TSAYAWA TAKARAR GWAMANA
00:54 SABANIN DA MUKA SAMU DA MALAM NASIR AL’RUFA’I
01:01:20 ABINDA YA SA MUKA ZABI JAM’IYYAR PRP, 01:02:24 MANUFOFIN YAKIN NEMAN ZABENA
01:10:53 MASU TALLAFI MIN TA BAYAN FAGE
01:15:41 MATASA A YAKIN NEMAN ZABENA
01:20:10 MATSALAR SIYASAR MATASA DA JAGORANCIN AL’UMMA
01:30:38 SHAWARATA GA MASU ZANGA-ZANGA
01:35:25 MATSALAR ‘YAN SIYASA IDAN SUN SAMU MULKI
01:37:54 YAUSHE YA KAMATA MALAMAI SU NUNA WANDA YA KAMATA A ZABA?
01:43:03 ABIN DA YASA NA ZABI MATAIMAKI WANDA BA MUSULMI BA
01:47:55 SIYASAR UBAN GIDA AMFANINTA DA ILLOLINTA GA MATASA
02:06:03 DAN TAKARA DA BUKATUN MASU TALLAFA MASA
02:08:51 GA MANUFA MAI KYAU, AMMA HANYAR SAMUN TA BA TADA KYAU
02:11:03 SHIN MALAMAI ZA SU IYA JAGORANCI JAM’IYYA TA SIYASA?
02:13:33 ABUBUWAN DA NA KARU DA SU A TSAYAWA TA TAKARA
02:19:20 SHEKARA 25 DA KAFA DIMOKARADIYYA A NAJERIYA
02:22:19 MATAKAN MAGANCE MATSALAR TSARO IDAN NA ZAMA GWAMAN
02:28:18 RUFE SHIRIN
Sun, 28 Jul 2024 - 2h 31min - 30 - 30 | TAKIN KASHIN MUTANE YAFI INGANCI (2) | DR. ABDULMUDDALIB MUH’D AUWAL GUSAU (RSS) | RUMFAR AFRICA PODCAST
"TAKIN KASHIN MUTANE YAFI INGANCI A NOMA" Ku kasance tare da mu a cikin Shirin Rumfar Africa Podcast na wannan makon tare da babban bako matashi masani akan Noma da Kiwo na zamani, mai bada shawara akan harkar Noma ga Ciboyoyin gwamnati da masu zaman kansu da Ɗai-daikun Mutane.
Mun tattauna batutuwa masu mahimmaci akan dukkanin abin da ya shafi Noma da Kiwo, don samun dubaru da shawarwari sai ku biya mu don jin tattaunawarmu tare da bakon namu, DR. ABDULMUDDALIB MUH’D AUWAL GUSAU (RSS).
Sun, 11 Feb 2024 - 2h 46min - 29 - 29 | ABIN DA NAYI A NOMA NA SAMU KUƊI | DR. ABDULMUDDALIB MUH’D AUWAL GUSAU (RSS) | RUMFAR AFRICA PODCAST
"Abin da nayi a Noma, Na samu Kuɗi" Ku kasance tare da mu a cikin Shirin Rumfar Africa Podcast na wannan makon tare da babban bako matashi masani akan Noma da Kiwo na zamani, mai bada shawara akan harkar Noma ga Ciboyoyin gwamnati da masu zaman kansu da Ɗai-daikun Mutane.
Mun tattauna batutuwa masu mahimmaci akan dukkanin abin da ya shafi Noma da Kiwo, don samun dubaru da shawarwari sai ku biya mu don jin tattaunawarmu tare da bakon namu, DR. ABDULMUDDALIB MUH’D AUWAL GUSAU (RSS).
Tue, 06 Feb 2024 - 2h 15min - 28 - 28 | TASKAR MNI | PROF. MANSUR IBRAHIM SOKOTO (MNI) | RUMFAR AFRICA PODCAST
"TASKAR MNI"Prof. Mansur Ibrahim Sokoto (MNI) Babban bakonmu na wannan makon a cikin shirin Rumfar Africa Podcast Hausa.Mun tattauna batutuwa masu mahimmaci ga Malamai, Ɗaliban ilimi Matasa, Mahukunta, Jagorori da kuma Al'umma baki ɗaya, haka mun tattauna bututuwa kamar haka:-- Me ake nufi da MNI? - Zangon karatunsa a Sudan da Madina.- Gwagwarmayarsa da 'Yan shi'a, - Mahimmacin Minbarin Juma'a ga Al'umma.- Mahimmacin majalisin karantarwa.- Gadadda Ililmi ga matsa masu tasowa.- Alakar Malamai da 'Yan Siyasa da shiga Siyasa. - Mahimmacin rubuce-rubuce ga Malamai.- Jan hankali ga masu Mulki da waɗan ake mulka, da wasu batutuwa da dama da suka shafi rayuwarmu ta yau da kullum.#podcast #nigerian #sokoto #mansursokoto #Hausa #adplushausa
Sun, 21 Jan 2024 - 3h 04min - 27 - 27 | USLUBI A DA'AWA GA MATASA MALAMAI | DR. JABIR SANI MAIHULA | RUMFAR AFRICA PODCAST
"USLUBI A DA’AWA YANA DA MAHIMMANCI A WAJAN GYARA DA ISAR DA SAƘO",
DR. JABIR SANI MAIHULA (MALAMIN ADDINI, KWAMISHINAN ADDINI A JAHAR SOKOTO) BABBAN BAKONMU NA WANNAN MAKON A CIKIN SHIRIN RUMFAR AFRICA PODCAST HAUSA.
MUN TATTAUNA BATUTUWA MASU MAHIMMACI GA MALAMAI MATASA A BANGARORI DA DAMA MUSAMMAN BANGAREN NEMAN ILIMI, KARANTARWA, DA'AWA DA KUMA SANIN HALAYYAR MUTANE DA IYA MU'AMALA DA SU, MUN TAƁO ZANGON KARATUNSA A ƘASAR INGILA INDA YA HAƊU DA MUTANE MABANBANTA JINSI, ADDINI, YARE, ƘASA, DA KUMA LAUNI, WANNAN ZANGON CIKE YAKE DA LABARAI MASU BAN MAMAKI, TAUSAYI, DARIYA, DA KUMA DARUSSA MASU YAWA.
Sun, 14 Jan 2024 - 2h 48min - 26 - 26 | DAGA KORA DA HALI ZUWA GWAMNA | MALAM IBRAHIM SHEKARAU | RUMFAR AFRICA PODCAST
"DAGA KORA DA HALI, ZUWA GWAMNA" BAKONMU A CIKIN SHIRIN RUMAFAR AFRICA PODCAST TARE DA SARDAUNAN KANO MALAM IBRAHIM SHEKARAU, TSOHON GWAMAN JIHAR KANO, SHIRIN CIKE YAKE DA BATUTUWA MASU MAHIMMANCI A KOWANE BANGARE NA RAYUWAR BABBAN BAKON NAMU (SIYASA, MALAMIN MAKARANTA, ZAMANTAKEWA, TARBIYYA, MA'AIKACIN GWAMNATI, JAGORANCI...), SHIRIN YAYI KOKARIN FITO DA DARUSSA A RAYUWAR BAKON NAMU MUSAMMAN A BANGAREN IYA JAGORANCI DA TAFIYAR DA HARKOKIN MULKI.
Sun, 07 Jan 2024 - 3h 18min - 25 - 25 | ABIN DA BAKU SANI BA GAME DA FALASDINU | DR. SA'ID AHMAD DUKAWA | RUMFAR AFRICA PODCAST
SHIRIN YA TATTAUNA BATUTUWA DA DAMA AKAN ƘASAR FALASƊINU, TAKAITACCEN TARIHINTA, ASALIN SAMUWAR YAHUDAWA A FALASƊINU, DAULAR USMANIYYA DA FALASƊINU, ME AKE NUFIN DA ALKAWARIN BALFOUR GA YAHUDAWA?, YAUSHE AKA KAFA ISRA'ILA?, YAKE-YAKEN ISRA'ILA AKAN ZIRIN GAZA, MATSAYIN KASASHEN LARABAWA DA MUSLMI, MATSAYIN KASASHEN AFRIKA AKAN RIKICIN, ME YASA KASASHEN YAMMA SUKE MARAWA ISRA'ILA BAYA?, ME YASA MAJALISAR ƊINKIN DUNIYA TA KASA HUKUNTA ISRA'ILA AKAN LAIFUKAN YAƘI?, KUNGIYAR YAHUDAWA TA DUNIYA (ZIONISTS), HARIN (7 GA WATAN OKTOBA) AKAN YAKIN ISRA'ILA, SHIN SHINE MAFARIN RIKINCIN ISRA'ILA DA FALASƊINAWA? DA WASU BUTUWA MASU MAHIMMACI AKAN RIKICIN. BAKON SHIRIN, DR. SA'ID AHMAD DUKAWA, MALAMI A JAMI'AR BUK, KANO, MAI FASHIN BAKIN AKAN AL’AMURRAN YAU DA KULLUM.
Tue, 02 Jan 2024 - 2h 06min - 24 - 24 | SIRRIN HAƁAKAR KASUWANCI I ALHAJI IBRAHIM DANYARO | RUMFAR AFRICA PODCAST
DON SANIN YA YANAYIN KASUWA YAKE, TA INA ZAKA FARA? ME YAKE KAWO HAUHAWAR FARASHIN KAYAN MASARUFI?, TASHIN DALA DA TSADAR KAYA, ALAKAR KASUWA DA MAHALLI, ALAKAR ƳAN KASUWA DA MASU SAYE DON AMFANIN YAU DA KULLUM, SHAWARWARI GA MATASA DA MATA MASU SON FARA KASUWANCI, MEKE RUSA KASUWANCI?, FATAUCI DA FATAKE TSAKANIN ƘASA DA ƘASA, ALAKAR MANYAN ƳAN KASUWA DA KANANAN ƳAN KASUWA, TASRIN SANIN ADDININ A KASUWANCI, GUDUMUWAR GWAMNATI GA ƳAN KASUWA, DA WASU BATUTUTUWA MASU MAHIMMACI.
BABBAN BAKON SHIRIN: ALHAJI IBRAHIM DANYARO, BABBAN DAN KASUWA A JIHAR, NAJERIYA, TARE DA NI MAI GABATARWA NAKU, SANI MOUSSA MAGAWATA MATANKARI.
Facebookfacebook.com/ADPlusHause
Instegraminstagram.com/adplushausa
Apple Podcastpodcasts.apple.com/us/podcast/adplus-hausa/id1649613259
GooglePodcastpodcasts.google.com/feed/aHR0cHM6Ly9hbmNob3IuZm0vcy9iZDQ5NmE3MC9wb2RjYXN0L3Jzcw
Twittertwitter.com/ADPlusHausa
Sun, 03 Dec 2023 - 2h 35min - 23 - 23 | WANNAN SHINE DAURAWA | MALAM AMINU IBRAHIM DAURAWA | RUMFAR AFRICA PODCAST
A WANNAN SHIRIN ZAKU KASANCE TARE BABBAN BAKO MALAM AMINU IBRAHIM DAURAWA, BABBAN MALAMIN ADDINI, KUMA SHUGABAN HUKUMAR HISBAH TA JIHAR KANO, NAJERIYA. MUN TATTAUNA BATUTUWA MASU MAHIMMMACI DA SUKA SHAFI RAYUWARSA, KARATUNSA, TSARIN AIKIN DA'AWARSA DA KOYARWARSA, AIKINSA NA HUKUMAR HISBAH, DA KUMA WASU BABUTUWA DA SUKA SHAFI AL'UMMA NA YAU DA KULLUM. #nigeria #hausa #podcast #niger #ghana #hisba #daurawa
Wed, 29 Nov 2023 - 2h 37min - 22 - 22 | HANYOYIN DOGARO DA KAI GA MATASA NA ZAMANI (2) | ENGR. MUSTAPHA HABU RINGIM | RUMFAR AFRICA PODCAST
RUMFAR AFRICA PODCAST HAUSA | KASHI NA 22 | TARE DA MATASHI NA MATASA GATAN MATASA, MAI INGANTA RAYUWAR MATASA, TA HANYAR KOYAR DA SU SANA'O'I NA ZAMANI DON DOGARO DA KAI, A WANNAN TATTANAWA A ZANGO NA 2, INDA MUKA TATTAUNA AKAN CIBIYAR ENGAUSA, MANUFAR KAFATA, TSARIN GUDANARWA, HANYOYIN DAUKAR DALIBAI, TSARIN KOYARWA DA ABUBUWAN DA AKE KOYARWA, DA SAURAN BATUTUWA MASU MAHIMMACI. BABBAN BAKONMU ENGR. MUSTAPHA HABU RINGIM, SHUBAGABA KUMA WANDA YA KAFA CIBIYAR ENGAUSA GLOBAL TECH HUB, MAI AIKIN KOYARDA FASAHAR KIRKIRE-KIRKIRE NA ZAMANI GA MATASA, KANO, NAJERIYA. --------
KU BIYO MU A:- FACEBOOK https://www.facebook.com/ADPlusHause INSTAGRAM: ADPlus Hausa (@adplushausa) • Instagram photos and videos DON SAURAREN SAUTI KADAI:- Spotify Podcast RUMFAR AFRICA | ADPlus Hausa • A podcast on Spotify for Podcasters Google Podcast RUMFAR AFRICA | ADPlus Hausa (google.com) Apple Podcasts RUMFAR AFRICA | ADPlus Hausa on Apple Podcasts Castbox: RUMFAR AFRICA | ADPlus Hausa (castbox.fm)
Tue, 14 Nov 2023 - 3h 48min - 21 - 21 | HANYAR DOGARO DA KAI GA MATASA | ENG. MUSTAPHA HABU RINGIM | RUMFAR AFRICA PODACAST
SHIRIN YATATTAUNA BATUN GWAGWARMAYAR BAKON SHIRIN A RAYUWA DA IRIN KALUBALEN DA HADU DA SHI, WANDA SHINE DALILIN DA YASA YA GANO HANYOYI NA ZAMANI DA ZAI IYA GINA RAYUWARSA YA KUMA DOGARA DA KAN SA, HAKAN YASA YAYIWA MATASA TASIRI SOSAI INDA YA JAWO SU SABODA YA DORA SU A KAN TURBAR SANIN YA KAMATA, MUN TATTAUNA LABARAI MASU TASIRI DA CANZA RAYUWAR MATASA, DA WASU BATUTUWA MASU MAHAMMANCI GA MATSA DA KUMA AL-UMARMU, BABBAN BAKONMU ENG. MUSTAPHA HABU RINGIM, SHUBAGABA KUMA WANDA YA KAFA CIBIYAR ENGAUSA GLOBAL TECH HUB, MAI AIKIN KOYARDA FASAHAR KIRKIRE-KIRKIRE NA ZAMANI GA MATASA, KANO, NAJERIYA.
Tue, 14 Nov 2023 - 3h 22min - 20 - 20 | WANI BANGARE NA RAYUWAR MALAM IBRAHIM KHALIL | MAL. IBRAHIM KHALIL | RUMFAR AFRICA PODCAST
SHIRIN YA TATTAUNA WANI BANGARE NA RAYUWAR MALAM IBARAHIM KAHALIL, A ADDINANCE, SIYASA DA KUMA ZAMANTAKEWA, DA WASU BATUTUWA DA AKE CECEKUCE AKAN SU GAME DA BAKON SHIRIN, BABBABAN BAKON SHIRIN SHINE: MAL. IBRAHIM KHALIL, BABBAN MALAMIN ADDININ MUSULUNCIN, KUMA DAN SIYASA DA YAKE DA GOGEWA A HARAKOKIN YAU DA KULLUM NA RAYUWA, YAYI TAKARAR GWAMNA A 2023 A JIHAR KANO, NAJERIYA.
Sun, 08 Oct 2023 - 3h 29min - 19 - 19 | FINA-FINAN HAUSA A MIZANI | ALI RABI'U ALI (DADDY) | RUMFAR AFRICA PODCAST
SHIRIN YA TATTAUNA BATUN SHIRYA FINA-FINAN HAUSA, MATSALAR JAGORANCI, INGANTA AIKI, JARUMAI MASU TAKA RAWA A FINA-FINAI, JARUMAI DA SHIGA SIYASA, INGANCI DA KARFIN TASIRIN LABARI, KARFIN FADA AJI NA HUKAMAR TACE FINA-FINAI HAUSA, SHAWARWARIN JARUMIN GA ABOKAN AIKIN SA, DAMA WASU BATUTUWA DA AKA TATTAUNA A CIKIN SHIRIN, TARE BAKON SHIRIN: ALI RABI’U ALI (DADDY) JARUMI, MAI DAUKAR NAUYI A MASANA’ANTAR SHIRYA FINA-FINAI TA KANNYWOOD, TARE DA NI MAI GABATARWA: DR. SANI MOUSSA MAGAWATA MATANKARI.#hausa #podcast #kannywood
Tue, 06 Feb 2024 - 2h 33min - 18 - 18 | RITAYA BATA TABA RAZANA NI BA, SABODA DALILAI... | RUMFAR AFRICA PODCAST
SHIRIN YA TATTAUNA BATUN RITAYA DAGA AIKI, MAHAMMINCIN SHIRI KAFIN LOKACIN YAZO, LOKACIN DA YA DACE MUTUM YA YI RITAYA, MAHIMMACIN SAN’A GA MA’AIKACI DON RAGE DOGARO DA ALNASHI, SANNAN BAKON YA YI BAYANIN YADDA YA KAMATA RAYUWA TA KASANCE BAYAN RITAYA. BAKON SHIRIN: PROF. MUNIR ABDULLAHI KAMBA, MALAMI A JAMI’AR BUKI, KANO NAJERIYA, TARE DA NI NAKU DR. SANI MOUSSA MAGAWATA MATANKARI MAI GABATARWA.
00:00 SHINFIDA
01:18 BUDE SHIRIN
05:48 KUDI DA ARZIKI
09:38 ME AKE NUFI DA RITAYA?
13:27 HANYOYIN SAMUN KARIN ALBASHI
15:58 MAFI YAWAN MA’AIKATA DA ABASHI SUKE FARA AIKI
17:12 DUBARUN BUNKASA ALBASHI
21:32 MA’AIKATU MASU ZAMAN KASU DA MA’AIKACI
26:27 MA’AIKATAN GWAMNATI DA KUDIN FENSHO
31:04 DABARUN JUYA ALBASHI DON BUNKASA SHI
37:11 HADA AIKI BIYU GA MA’AIKACI DON RAGE YAWAN CIN BASHI
41:35 MAHIMMANCIN KOYAWA IYALI SANA’A GA MA’AIKACI
42:46 FARGABAR ZUWAN RITAYA GA MA’AIKATA
44:58 SHIN MA’AIKACI A MATSAYIN BAWA YAKE?
48:44 RASHIN ALBASHI MAI KYAU, SHI KE KAWO RASHIN GASKIYA
53:40 BIYAN BASHI KO AMFANI DA ALBASHI TA HANYAR SARRAFA SHI
01:00:47 SHAWAR GA MA’AIKATAN KAMFANI MASU ZAMAN KAN SU
01:06:39 MATSAYIN FENSHO GA MA’AIKICI
01:09:16 MATSAYIN MA’AIKACIN DA YA RASU
01:10:29 KAR KA JIRA KUDIN RITAYA DON FARA KASUWANCI
01:12:05 TSARI MAFI KYAU DON INGANTA RAYUWAR MA’AIKACI
01:15:43 RAYUWA BAYAN RITAYA
01:20:16 MATSALAR RASHIN BAYAR DA KUDIN FENSHO CIKIN LOKACI
01:22:42 BABBAR SHAWAR GA MA’IKATA
01:25:55 RUFE SHIRIN
Tue, 06 Feb 2024 - 1h 28min - 17 - 17 | NIGER DA ECOWAS GA MAFITA | DR. SA’ID AHMAD DUKAWA | RUMFAR AFRICA
SHIRIN YA YI SHARHI NE DA FASHIN BAKI AKAN ABUBUWAN DA SUKE FARUWA A KASAR NIJAR TUN BAYAN JUYIN MULKIN RANAR 26,07,2023 WANDA YAYI SANADIYYAR HAMBARAR DA ZABABBEN SHUGABA MOHAMED BAZOUM, DALILAN DA SUKA SA DUNIYA TA DAMU DA JUYIN MULKIN NIJAR, JUYIN MULKI ILLAR SHI DA AMFANIN SHI, SHUGABANCI NA GARI DA DIMOKARASIYYA, A KAN ABIN DA AKA KAFA KUNGIYAR ECOWAS, SHIN NAJERIYA CE ZATA YAKI NIJAR, HASASHEN ABIN ZAI IYA FARUWA NAN GABA TSAKANIN NIJAR DA EOWAS, DA SAURAN BATUTUWA, BAKON SHIRIN: DR. SA’ID AHMAD DUKAWA, MALAMI A JAMI’AR BUK KUMA MAI SHARHI DA FASHIN BAKI AKAN AL-AMURRAN SIYASA, TARE DA NI NAKU MAI GABATARWA DR. SANI MOUSSA MAGAWATA MATANKARI.
00:00 SHINFIDA 00:02 BUDE SHIRIN 00:08 MAHIMMANCIN NIGER A IDON DUNIYA DA AFRICA 00:34 TASIRIN KASAR RASHA A AFRICA 00:46 ME YASA MULKIN DIMOKARASIYYA YA NA MULIKN SOJA? 00:51 MULKIN DIMOKARASIYYA DA NA SOJA WANE YAFI KAWO CIGABAN KASA 00:53 ABINDA SOJA ZAI DON INGANTA SHUGABANCIN FARAR HULA 00:56 GUDUMMAWAR 'YAN SIYASA A JUYINMULKI 01:05:55 GUDUMMAWAR ‘YAN KASA WAJAN TATTABATAR DA MULKIN DIMOKARASIYYA KO KUMA MULKIN SOJI 01:15:10 AKAN ME AKA GINA KUNGIYAR ECOWAS 01:30:54 SHIN NAJERIYA CE ZATA YAKI NIJAR? 01:38:05 ‘YAN SOCIAL MEDIA DA YADA LABARN KARYA DAN HADDASA FITINA 01:41:09 SOJOJIN TURAWA A AFRICA DA MATSALAR TSARO 01:33:19 DIFLOMASIYYAR MALAMAI A MATSALAR NIJAR 01:47:56 HASASHEN ABINDA ZAI FARU IDAN KOWANNE TSAYA AKAN KUDIRIN SA (NIGER DA ECOWAS) 01:50:06 SHAWARA GA ‘YAN SIYASA DON GINA SHUGABANCI NA GARI 01:51:23 RUFE SHIRIN
Mon, 28 Aug 2023 - 1h 54min - 16 - 10 | MUSULUNCI DA MUSULMI A NIJAR | SH. MUH'D ABDURRAHMAN SADIS | RUMFAR AFRICA
SHIRIN YA TATTAUNA BATUN CIGABAN MUSULUNCI A NIJAR, DA CIGABAN DA’AWA DA KALUBALEN DA MASU DA’AWA SUKE FUSKANTA DA HANYOYIN WAR-WARE SU, HADARIN KABILANCI, HADARIN SHI’A, TSARIN MAKARATUN ISLAMIYYA DA NA BOKO, TSARIN BADA FATAWA, ABUBUWAN DA AKE KARE MARTABA DA KIMAR MALAMI A CIKIN AL-UMMA, MATSAYIN MIMBARI DA MAI DA’AWA, TSARIN GUDANARWA NA KUNGIYOYIN ADDNIN MUSULUNCI A NIJAR. BAKON SHIRIN: SH. MUH’D ABDURRAHAMAN SADIS, BABBAN LIMAMIN MASALLACIN AMIR SULTAN A NIJAR, MAI GABATARWA: DR. SANI MOUSSA MAGAWATA MATANKARI
Mon, 24 Jul 2023 - 2h 59min - 15 - 16 | RUMFAR AFRICA | SIRRIN AIKIN HAJJI | SH, ABDULLAH MUH'D 'YANKABA | PODCASMon, 24 Jul 2023 - 2h 29min
- 14 - 15 | WAKA DA MAWAKA | MAL. ABUBAKAR IBRAHIM KANTAMA | RUMFAR AFRICA | PODCAST
SHIRIN YA TATTAUNA TAKAITACCEN TARIHIN BAKON SHIRIN, ZAMAN SA A KASAR SUDAN, WAKA BAIWACE KO KOYO NE, ZAMAN KAUYE DA BIRNI DA TASIRIN SU GA MAWAKI, KALUBALEN MAWAKAN ADDININ MUSULUNCI, HANYOYIN SAMUN KUDADEN SHIGA, NAZARIN WASU DAGA WAKOKIN BAKON SHIRN, MATAKAN ZAMA MAWAKI, DA SAURAN BATUTUWA MASU MAHAMMANCI DA MUKA TATTAUNA A CIKIN SHIRIN. BAKON SHIRIN: MAL. ABUBAKAR IBARAHIM KANTAMA, BABBAN MAWAKAIN ADDININ MUSULUNCI A NAJERIYA, TARE DA MAI GABATARWA DR. SANI MOUSSA MAGAWATA MATANKARI. #hausa #podcast #waka #mawaka #rumfa #nigeria #niger #ghana
Sat, 25 Mar 2023 - 2h 36min - 13 - 14 | MULKI DA JAGORANCI | SH. ABUBAKAR ABDUSSALAM MUH'D (BABAN GWALE) | RUMFAR AFRICA | PODCAST
SHIRIN YA TATTAUNA BATUN MLKI, SHUGABANCI DA JAGORANCIN MUTANE DA SANIN HARKOKIN TAFIYAR MULKI A MAHANGAR MUSULUNCI, HAKA KUMA SHIRIN YA TATTAUNA BATUN SIYASA, DAMOKARADIYYA, SHURA DA KUMA HANYOYIN ZABAR SHUGABA KO HAWA KAN KARAGAR MULKI, HAKA KUMA SHIRIN YA DUBA BATUN SHARUDDAN DA HALASTACCIYAR SIYASA TA GINU AKAN SU, HAKA SHIRIN YA TATTAUN HAKKIN SHUGABA AKAN TALAKA DA KUMA HAKKIN TALAKA AKAN SHUGABA, A KARSHE MUN TATTAU BATUN SHUGABANCI DA JAGORANCIN 'YA MACE A MAHANGAR MUSULUNCI, BAKON SHIRN MAL. ABUBAKAR ABDUSSALAM MUHAMMAD BABAN (GWALE), MALAMIN ADDANIN MUSULUNCI MAI KOYARWA A KWALEJIN SA'ADATU RIMI, KANO NAJERIA, TARE DA DR, SANI MOUSSA MAGAWATA MATANKARI, MAI GABATARWA. #hausa #mulki #podcast #nigeria #niger #ghana #mata
Mon, 06 Mar 2023 - 3h 28min - 12 - 13 | DUNIYAR ALJANU | SH, DR. AHMAD MUSA ABDULLAH | RUMFAR AFRICA | PODCAST
SHIRIN YA TATTAUNA BATUN ALAKAR MUTUM DA ALJANI, WANENE ALJANI? ABINDA KE SA ALJANI YA SHIGA CIKIN MUTUM YA CUTAR DA SHI, HANYOYIN KARIYA DAGA ALJANI, ABINDA AL-KUR'ANI DA SUNNA SUKA CE GAME DA ALJANI DA MUTUM, SOYAYYA KO KIYAYYA TSAKANIN ALJANI DA MUTUM, MASU AIKIN ILAJI DA ALJANU, LABARAN BAKON SHIRIN DA ALJANU, MUN TATTAUNA WADANNAN BATUTUWA NE TARE DA MASANI AKAN DUNIYAR ALJANU SH, DR. AHMAD MUSA ABDULLAHI, TARE DA DR. SANI MOUSSA MAGAWATA MATANKARI MAI GABATARWA.
Thu, 16 Feb 2023 - 1h 53min - 11 - 12 | KIMIYYAR NEMAN KUDI | PROF. MUNIR ABDULLAHI KAMBA | RUMFAR AFRICA
SHIRIN YA TATTAUNA BANGARE GUDA BIYU NA FARKO: MAHIMMANCIN SANIN ILIMIN KIMIYYAR DAKIN KARATU DA KUMA AMFANIN SA GA AL-UMMA, BANGARE NA BUYU SHI NE: HANYOYIN SAMUN KUDI DA SARRAFA SU DA KUMA TASKACE SU, HAKA MUN TATTAUNA BATUN AMFANI DA KIMIYYA DA FASAHA DON SMUN KUDI, SAI KUMA HANYOYIN SAMUN ‘YANCIN SAMUN KUDADEN SHIGA GA MA’AIKACE BA TARE DA YA DOGARA DA ALBASHI BA, MUN TATTAUNA WADANNAN BUTUTUWAN NE TARE DA BABBAN MASANI KUMA KWARARRE AKAN KIMIYYAR SADARWA TA BANGAREN DAKIN KARATU, DA KUMA TATTALIN ARZIKI, PROF. MUNIR ABDULLAHI KAMBA, MALAMI A JAMI’AR BUK KANO, NAJERIYA. TARE DA DR. SANI MOUSSA MAGAWATA MATANKARI, MAI GABATARWA.
Wed, 15 Feb 2023 - 1h 31min - 10 - 11 | ZUMUDIN NEMAN SHUHURA | DR. ABDULKADIR ISMA'IL KABARA | RUMFAR AFRICA | PODCAST
SHIRIN YA TATTAUNA BATUN ZUMUDIN NEMAN SHUHURA AKAFAFEN SADA ZUMUNTA, ASALIN SHUHURA A MAHANGAR MUSULUNCI, NAUYI DA KAIDOJIN DAKE KAN MASHAHURAI, AL’UMMA DA BIBIYAR ABINDA BAYA AMFANAR DASU KOMAI A RAYUWA, TASIRIN SHUHURA MAI KYAU DA MARAR KYAU, AMFANI DA YARA KANANA DON NEMAN SHUHURA, IYAYE DA ‘YA’YANSU MASU NEMAN SHUHURA, MALAMAI DA NEMAN SHUHURA, SAI KUMA SHIRIN YA RUFE DA TATTAUNA BATUN KAFEN YADA LABARAI DA MASU NEMAN SHUHURA, SAI JAN HANKALIN GWANATI, IYAYE, DA KUMA MATASA, MUN TATTAUNA WADANNAN BUTUTUWAN DA BABBAN BAKO DR. ABDULKADIR ISMA’IL KABARA, MALAMI A JAMI’AR BUK KANO, NAJERIYA, TARE DA DR. SANI MOUSSA MAGAWATA MAI GABATARWA.
Thu, 26 Jan 2023 - 1h 55min - 9 - 09 | ZAMAN LAFIYA, YAFI ZAMA DAN SARKI | SH. SALISU GARBA DIFFA | DR. SANI MOUSSA MAGAWATA | RUMFAR AFRICA | PODCASTSun, 08 Jan 2023 - 1h 12min
- 8 - 08 | AIKIN JARIDA TSAKANIN AFRIKA DA TURAI | ABDOULAYE MAMANE WADATA | DR. SANI MOUSSA MAGAWATA | RUMFAR AFRICA | PODCAST
SHIRIN YA TATTAUNA BATUN AIKIN JARIDA TSAKANIN NAHIYAR AFRIKA DA NAHIYAR TURAI, YANAYIN CIGABA DA GUDANAR DA AIKIN JARIDA, ALAKAR DAN JARIDA DA MUTANEN GARI DA MAHUKUNTA, KA’IDOJIN AIKIN JARIDA, SHIN ALFARMA DA SANAYYA SUNA DA TASIRI A AIKIN JARIDA A NAHIYAR TURAI? DA SAURAN BAUTUWA MASU ALAKA DA SHIRIN, TARE DA BABBAN DAN JIRADA MA’AIKACI A GIDAN RADIO DW HAUSA DAKE JAMUS A NAHIYAR TURAI
Mon, 02 Jan 2023 - 1h 37min - 7 - 06 RUMFAR AFRICA | KAFOFIN YADA LABARAN KASAR NIJAR, SHIN NUNA GINA AL-UMMA? | | PODCAST
RUMFARA AFRICA PODCAST HAUSA| KAFOFIN YADA LABARAN KASAR NIJAR, SHIN NUNA GINA AL-UMMA? | MAL. CHAIBOU MAHAMANE
Kuna iya sauraron shirin ta hanyar dandamalinmu na podcast ta wayar hannu. Muna ba da shawarar sauraron Podcast din ta hanyar manhajar Apple Podcasts akan iPhone, da manhajar Google Podcasts akan Android. Muna son ku dinga bayyana mana ra`ayoyinku game da shirye-shiryen, za kuma ku iya ba mu maki game da Podcast din akan Apple Podcast. Hakanan kuma kuna iya ba da shawarar baƙon da za mu tattauna da shi a podcast din (RUMFAR AFRICA) ta hanyar aiko mana da imel a: hausaadp@gmail.com
Mon, 19 Dec 2022 - 1h 44min - 6 - 05 | GOBARAR FUSHI DA RUWAN KASHE TA | DR. AMINU ISMA'IL SAGAGI | RUMFAR AFRICA | PODCAST
SHIRIN YA TATTAUNA NE AKAN FUSHI DA KUMA TASIRIN SA A RAYUWAR MU TA YAU DA KULLUM, HAKA YA TATTAUNA MAFRIN FUSHI, RABE-RABEN SA (MAI LINZAMI DA MARAR LINZAMI), HAKA YAYI DUBIYA AKAN HANYOYIN SARRAFA FUSHI, DA KUMA AMFANIN FUSHI (CI GABAN MUTUM), DA ILLOLINSA GA MUTUM TA BANGAREN: (SHUGABANCI, JAGORANCI, TATTALIN ARZIKI, RASHIN TSARO, DA KUMA A ZAMANTAKEWAR AURE), DA KAWO MISALAI DAGA ABUBUWAN DA SUKE FARUWA A RAYUWAR MU TA YAU DA KULLUM.
Wed, 16 Nov 2022 - 2h 37min - 5 - E04 RUMFAR AFRICA | HONYOYIN INGANTA JIMA'I | DR. ADAM AHMAD BUNKAU | PODCAST
E04 RUMFAR AFRICA | HANYOYIN INGANTA JIMM'A | DR. ADAM AHMED | PODCAST
SHIRIN YA TATTAUNA BATUN TASIRIN INGANTANCEN JIMA'I (SADUWA) TSAKANIN MA'AURATA DA SAMUN ZAMAN LAFIYA DA KYAUTATA ZAMANTAKEWAR AURE (MUTU KA RABA), WANE LOKACI YA DACE A KOYI ILMIN JIMA'I?, SHIN DAN ADAM YANA BUKATAR SAI AN KOYA MASA YADDA ZAI YI SADUWA?, HAKA AN TATTAUNA BATUN SHAN MAGANIN KARIN KARFIN JIMA'I GA MATA DA MAZA ILLARSA DA AMFANIN SA, ALAKAR AUREN DOLE DA NA SOYAYYA A WAJAN SAMUN INGANTACCEN JIMA'I, DA SAURAN BATUTUWA MASU MAHIMMACI KAN ILIMI JIMA'I, TARE DA MASANI KUMA KWARARRE A HARKOKIN ZAMANTAKEWAR AURE, DR. ADAM AHMAD BUNKAU
Sun, 06 Nov 2022 - 2h 25min - 4 - 03 | KAFOFIN SADARWA NA MUSULUNCI, NASARA DA KALUBALE | DR. HABIB TIJJANI | RUMFAR AFRICA | PODCAST
SHIRIN YA TATTAUANA BATUN MAHIMMANCIN KAFOFIN SADARWA MASU MANUFAR YADA ADDININ MUSULUNCI DA HARSHEN HAUSA A NAHIYAR YAMMACIN AFRICA, SHIRIN YA DUBA IRA-IREN NASARORI DA CIGABAN DA SUKA SAMAWAR AL-UMAR MUSULMI MASU MAGANA DA YAREN HAUSA, TA BANGARORI DABAN-DABAN NA RAYUWA (ADDINI, ZAMANTAKEWA, TATTALAIN ARZIKI, KIWON LAFIYA DA KUMA BANGAREN TSARO) HAKA KUMA YA TATTAUNA KALUBALEN DA KAFOFIN SUKE FUSKANTA, KAMAR HANYOYIN SAMU KUDADEN SHIGA DON CIGABA DA GUDANAR DA TASHOSHIN BA TARE DA SAMUN CIKAS BA, DA DAI SAURARAN BATUTUWA.
SOUNDCLOUD:
Kuna iya sauraron shirin ta hanyar dandamalinmu na podcast ta wayar hannu. Muna ba da shawarar sauraron Podcast din ta hanyar manhajar Apple Podcasts akan iPhone, da manhajar Google Podcasts akan Android. Muna son ku dinga bayyana mana ra`ayoyinku game da shirye-shiryen, za kuma ku iya ba mu maki game da Podcast din akan Apple Podcast. Hakanan kuma kuna iya ba da shawarar baƙon da za mu tattauna da shi a podcast din (RUMFAR AFRICA) ta hanyar aiko mana da imel a: hausaadp@gmail.com
Sun, 30 Oct 2022 - 1h 12min - 3 - 02 | MUSULMIN KASAR GHANA DA TASIRIN SU A KASAR | Sh.Yusuf Umar Jalo | RUMFAR AFRICA | PODCAST
SHIRIN YA TATTAUNA TASIRIN MUSULMI A KASAR GHANA TA BANGARORI DABAN-DABAN NA RAYUWA, ADDINI, ILIMI, SIYASA, ZAMANTAKEWA, AL`ADU, TSARO, HARKAR SADARWA, MOTSA JIKI, DA KUMA HARKAR KASUWANCI.Kuna iya sauraron shirin ta hanyar dandamalinmu na podcast ta wayar hannu. Muna ba da shawarar sauraron Podcast din ta hanyar manhajar Apple Podcasts akan iPhone, da manhajar Google Podcasts akan Android.Muna son ku dinga bayyana mana ra`ayoyinku game da shirye-shiryen, za kuma ku iya ba mu maki game da Podcast din akan Apple Podcast. Hakanan kuma kuna iya ba da shawarar baƙon da za mu tattauna da shi a podcast din (RUMFAR AFRICA) ta hanyar aiko mana da imel a: hausaadp@gmail.com
Sun, 23 Oct 2022 - 1h 48min - 1 - 01 | WANI BANGARE NA RAYUWAR MALAM ABUBAKAR MUKHTAR YOLA | RUMFAR AFRICA | PODCAST
Shirin ya tattauna bangarori daban-daban na rayuwar malam, Neman Iliminsa, tsari da Manhajinsa na Karantarwa da da'awa. Muhimmancin karatun Zaure wajan gina daliban Ilimi don zama Malamai Karancin salon da'awa a Duniyar Hausawa. Salon yi wa ‘yan Siyasa da shuwagabbni nasiha. Salon yin raddi tsakanin malamai. Cigaban da da'awa ta samu don tafiya da zamani. Illar cin hanci da rashawa. Auren Mata fiye da daya a mahangar Malam. wanene wawa a Mahangar Msulunci
Wed, 12 Oct 2022 - 1h 52min
Podcasts ähnlich wie RUMFAR AFRIKA | TARE DA DR. SANI MOUSSA MAGAWATA
- Global News Podcast BBC World Service
- Kriminálka Český rozhlas
- El Partidazo de COPE COPE
- Herrera en COPE COPE
- The Dan Bongino Show Cumulus Podcast Network | Dan Bongino
- Es la Mañana de Federico esRadio
- La Noche de Dieter esRadio
- Hondelatte Raconte - Christophe Hondelatte Europe 1
- Affaires sensibles France Inter
- La rosa de los vientos OndaCero
- Más de uno OndaCero
- La Zanzara Radio 24
- Espacio en blanco Radio Nacional
- Les Grosses Têtes RTL
- L'Heure Du Crime RTL
- El Larguero SER Podcast
- Nadie Sabe Nada SER Podcast
- SER Historia SER Podcast
- Todo Concostrina SER Podcast
- 安住紳一郎の日曜天国 TBS RADIO
- The Tucker Carlson Show Tucker Carlson Network
- 辛坊治郎 ズーム そこまで言うか! ニッポン放送
- 飯田浩司のOK! Cozy up! Podcast ニッポン放送
- 武田鉄矢・今朝の三枚おろし 文化放送PodcastQR