Filtrer par genre

Wasanni

Wasanni

RFI Hausa

A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.

27 - Najeriya ce zakara a wasannin sojoji na Afrika karo na biyu da aka gudanar
0:00 / 0:00
1x
  • 27 - Najeriya ce zakara a wasannin sojoji na Afrika karo na biyu da aka gudanar

    Shirin Duniyar Wasanni na wannan mako yayi duba ne kan yadda aka kammala wasanni sojoji na nahiyar Afrika. Wannan ne dai karo na biyu da tawogogin ƙasashe 20 suka fafata a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja, inda kuma tawagar ƴan wasan sojoji ta Najeriya ta zamo zakara, bayan da ta samu nasarar lashe lambar zinari 114 da azurfa 65 sai kuma tagulla 55 a jumlace ke nan ta samu lambobin yabo 234.

    Ƙasar Aljeriya ke bi mata a matsayin na 2 da lambar zinari 53 da azurfa 22 sai kuma agulla 21, a jumlace ita kuma ta samu lambobin yabo 96, Kenya ce tazo ta 3 bayan da ta lashe lambobin yabo 50.

    Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin tare da Khamis Saleh.......

    Mon, 02 Dec 2024
  • 26 - Sharhi kan yadda aka kammala wasannin zuwa gasar AFCON da za a yi a Morocco

    Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci ya yi duba ne kan yadda aka kammala wasannin neman gurbin shiga gasar lashe kofin Afrika. Kuma a tsakiyar makon daya gabata ne aka kammala wasannin neman gurbin zuwa gasar cin kofin AFCON da ke gudana tsakanin ƙasashen Afrika, gasar da Morocco za ta karɓi baƙunci a watan Disamban shekarar 2025.

    A yanzu dai dukkanin ƙasashe sun san makomarsu kuma ƙasashen 24 da za a ga haskawarsu a gasar ta baɗi sun ƙunshi ita mai masaukin baƙi Morocco da Burkina Faso da Kamaru da Algeria da Jamhuriyar Dimukaradiyar Congo da Senegal da Masar da Equatorial Guinea da Cote d’Ivoire da Uganda da Afrika ta Kudu da Gabon da Tunisia da Najeriya.

    Sauran sun ƙunshi Zambia da Mali da Zimbabwe da Tsibirin Comoros da Sudan da Benin da Tanzania da Botswana da kuma Mozambique, a wani yanayi da Bostwana ke samun tikitin gasar karon farko bayan dakon shekaru 12.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh........

    Mon, 25 Nov 2024
  • 25 - Gudummawar da cibiyoyin horar da matasa wasan kwallon ƙafa ke bayarwa a Najeriya

    Shirin Duniyar Wasanni a wannan makon ya yi duba ne kan irin gudummawar da cibiyoyin horar da matasa wasan kwallon ƙafa ke bayarwa wajen zakulo matasan ƴan wasa da horar da su a Nigeria. Wannan dai wani bangare ne na gudummawarsu ga ci gaban wasan kwallon ƙafa a Nigeria, tsofin ƴan wasan tawagar Super Eagles na ƙasar, sun fara kafa cibiyoyi masu zaman kan su, da su ke zakulowa tare da horar da matasa don yin fice a harkar ta kwallon kafa.

    Irin wadannan cibiyoyin horar da matasa wasan na kwallon kafa da a turance ake kira Football Academy, kan shiga birane da karkara don tuntubar ƙanana da matsakaitan club-club, domin samun ƴan wasan daga wajen su da za a yi rijistarsu a wannan cibiya.

    Pascal Patrick, tsohon ɗan wasan Super Eagles kuma shugaban Hukumar kwallon kafa ta NFA a jihar Bauchi kana co-odinetan tawagar Super Eagles na Nigeria, na daya daga cikin tsofaffin ƴan wasan ƙasar da suka kafa irin wannan cibiya a jihar Bauchi.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh.......

    Mon, 18 Nov 2024
  • 24 - Yadda cece-kuce ya mamaye kyautar Ballon d'Or ta 2024

    Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan makon ya yi dubi ne akan yadda aka gudanar da bikin bada kyautar Ballon d’Or ta shekarar 2024.

    Mon, 04 Nov 2024
  • 23 - Hukuncin da CAF ta yi kan danbarwar Najeriya da Libya da kuma wasan El-Clasico

    Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon yayi duba ne kan yadda wasan El-Clasico ya gudana da kuma hukuncin da Hukumar Kwallon Ƙafar Afrika CAF tayi kan danbarwar Najeriya da Libya. A ƙarshen mako ne dai kwamin ladaftarwa na hukumar CAF, ya zartar da hukuncin cewa Najeriya ce tayi nasara da ci 3 da nema kan Libya, tare da tarar dala dubu 50.

    Haka nan shirin ya duba yadda wasan El-Clasico ya gudana tsakanin Real Madrid da Barcelona da aka yi a ƙarshen mako.

    Mon, 28 Oct 2024
Afficher plus d'épisodes