Filtra per genere

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau

Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim

Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.

679 - Yadda Za A Kauce Wa Gadon Ciwon Suga
0:00 / 0:00
1x
  • 679 - Yadda Za A Kauce Wa Gadon Ciwon Suga

    Send us a textWani bincike da aka gudanar ya nuna cewa akalla ’yan Najeriya miliyan biyar ne suke cikin hadarin kamuwa da ciwon suga nan da shekarar 2030.Yaduwar lalurar a tsakanin wadanda iyayensu suke fama da ita tana cikin hanyoyin da suke taimakawa wajen karuwar ta. Albarkacin Ranar Ciwon Suga ta Duniya, shirin Najeriya A Yau zai tattauna a kan hanyoyin da wadanda suke fuskantar barazanar kamuwa da lalurar za su bi don kauce mata.

    Thu, 14 Nov 2024
  • 678 - Hanyoyin Hana Lalata Turakun Rarraba Wutar Lantarki.

    Send us a textBarnata kayan gwamnati ba sabon abu ba ne a Najeriya; sai dai a wannan karon barnar ba gwamnati kadai ta shafa ba har ma da alummar gari.A kwanakin baya ne wasu yankuna na Arewacin Najeriya suka fuskanci rashin wutar lantarki na tsawon kusan kwanaki goma.A cewar hukumomin da abin ya shafa dai hakan ya faru ne saboda ’yan ta’adda sun kai wa turakun wutar lantarki hari.Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba ne a kan abin da ya hana kawo karshen barnar da ake yi wa layu...

    Tue, 12 Nov 2024
  • 677 - Dalilan Durkushewar Kananan Sana’o’i Da Hanyoyin Magance Su

    Send us a textKanana da matsakaitan masana’antu, kamar yadda masana tattalin arziki suka bayyana suna taka muhimmiyar rawa wajen karuwar arziki a kowace kasa.Galibi irin wadannan masana’antu matasa suke kafa su don samun abun sakawa a bakin salati.Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan dalilan durkushewar kanana da matsakaitan sana’oi a Najeriya.

    Mon, 11 Nov 2024
  • 676 - Me Zai Faru Bayan Cikar Wa’adin Da Lakurawa Suka Bai Wa Sakkwatawa?

    Send us a textA yau Juma’a wa’adin da wata sabuwar kungiya mai suna Mujahidin – wadda aka fi sani da Lukarawa - ta bai wa al’ummar wasu yankunan Jihar Sakkwato ya zo karshe.Kungiyar dai ta bai wa al’ummar yankunan zuwa yau Juma’a su girbe amfanin gonarsu, amma a cewar wani mazaunin daya cikin yankunan ya ce ai ba su bari wa’din ya cika na suka dauki mataki.Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba ne a kan wannan kungiya da manufofinta.

    Fri, 08 Nov 2024
  • 675 - Me Nasarar Shugaban Amurka Donald Trump Yake Nufi Ga Najeriya?

    Send us a textTun bayan dawowar Najeriya mulkin demokaradiyya a shekarar 1999 ne dai ake gudanar da zaben shuwagabanni a duk lokacin da aka ce wa’adin shugaba ya kawo karshe.Toh sai dai tun dawowar mulkin demokradiyyar ne ake samun korafe korafe kan yadda ake gudanar da zabuka da ma irin rawar da shugabancin wanda da ya lashe zabe a Amurka ke tasiri kan Najeriya.Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zaiyi Nazari ne kan wadannan batutuwa.

    Thu, 07 Nov 2024
Mostra altri episodi