Filtrar por gênero
- 679 - Yadda Za A Kauce Wa Gadon Ciwon Suga
Send us a textWani bincike da aka gudanar ya nuna cewa akalla ’yan Najeriya miliyan biyar ne suke cikin hadarin kamuwa da ciwon suga nan da shekarar 2030.Yaduwar lalurar a tsakanin wadanda iyayensu suke fama da ita tana cikin hanyoyin da suke taimakawa wajen karuwar ta. Albarkacin Ranar Ciwon Suga ta Duniya, shirin Najeriya A Yau zai tattauna a kan hanyoyin da wadanda suke fuskantar barazanar kamuwa da lalurar za su bi don kauce mata.
Thu, 14 Nov 2024 - 678 - Hanyoyin Hana Lalata Turakun Rarraba Wutar Lantarki.
Send us a textBarnata kayan gwamnati ba sabon abu ba ne a Najeriya; sai dai a wannan karon barnar ba gwamnati kadai ta shafa ba har ma da alummar gari.A kwanakin baya ne wasu yankuna na Arewacin Najeriya suka fuskanci rashin wutar lantarki na tsawon kusan kwanaki goma.A cewar hukumomin da abin ya shafa dai hakan ya faru ne saboda ’yan ta’adda sun kai wa turakun wutar lantarki hari.Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba ne a kan abin da ya hana kawo karshen barnar da ake yi wa layu...
Tue, 12 Nov 2024 - 677 - Dalilan Durkushewar Kananan Sana’o’i Da Hanyoyin Magance Su
Send us a textKanana da matsakaitan masana’antu, kamar yadda masana tattalin arziki suka bayyana suna taka muhimmiyar rawa wajen karuwar arziki a kowace kasa.Galibi irin wadannan masana’antu matasa suke kafa su don samun abun sakawa a bakin salati.Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan dalilan durkushewar kanana da matsakaitan sana’oi a Najeriya.
Mon, 11 Nov 2024 - 676 - Me Zai Faru Bayan Cikar Wa’adin Da Lakurawa Suka Bai Wa Sakkwatawa?
Send us a textA yau Juma’a wa’adin da wata sabuwar kungiya mai suna Mujahidin – wadda aka fi sani da Lukarawa - ta bai wa al’ummar wasu yankunan Jihar Sakkwato ya zo karshe.Kungiyar dai ta bai wa al’ummar yankunan zuwa yau Juma’a su girbe amfanin gonarsu, amma a cewar wani mazaunin daya cikin yankunan ya ce ai ba su bari wa’din ya cika na suka dauki mataki.Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba ne a kan wannan kungiya da manufofinta.
Fri, 08 Nov 2024 - 675 - Me Nasarar Shugaban Amurka Donald Trump Yake Nufi Ga Najeriya?
Send us a textTun bayan dawowar Najeriya mulkin demokaradiyya a shekarar 1999 ne dai ake gudanar da zaben shuwagabanni a duk lokacin da aka ce wa’adin shugaba ya kawo karshe.Toh sai dai tun dawowar mulkin demokradiyyar ne ake samun korafe korafe kan yadda ake gudanar da zabuka da ma irin rawar da shugabancin wanda da ya lashe zabe a Amurka ke tasiri kan Najeriya.Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zaiyi Nazari ne kan wadannan batutuwa.
Thu, 07 Nov 2024 - 674 - Shin Addu’oi Kadai Najeriya Take Bukata Don Ficewa Daga Matsaloli?
Send us a textGalibin ’yan Najeriya dai sun yarda cewa Allah ne mai bayarwa, Shi ne kuma mai hanawa.Mai yiwuwa hakan ne kan sa a rika yin kira, musamman ga mabiya addianai mafiya rinjaye na Musulunci da Kiristanci, da su yi addu’oi don samun waraka daga matsalolin da aka fama da su.Sai dai kuma wasu ’yan kasa suna ganin fadar haka alama ce da take nuna cewa siukuwa ta kare saura zamiya.Shirin Najeriya A Yau zai yi Nazari ne kan wannan batu.
Tue, 05 Nov 2024 - 673 - Abin Da Ya Kamata A Yi Da Kananan Yara Masu Zanga-Zanga
Send us a textGurfanar da yaran nan da aka kama watanni uku da suka gabata yayin zanga-zangar ‘#EndBadGovernance’ na ci gaba da yamutsa hazo a Najeriya.Mutane da dama dai, musamman a Arewa, suna ta tofin Allah-tsine a kan kamen yaran, wadanda wasu suke cewa kanana ne, shekarunsu ba su kai a kama su ba ballantana a kai su gaban kotu.Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai tattauna ne kan tanadin doka game da kamen kananan yara, da kulle su, da kuma gurfanar da su gaban kuliya.
Mon, 04 Nov 2024 - 672 - Yadda Dawo Da Wutar Lantarki Zai Sauya Wasu Sassan Arewa
Send us a textA wasu sassan Arewa, mutane sun cika da farin ciki da annashuwa bayan da wutar lantarki ta dawo a yankunansu.Yankin na Arewa dai ya tsinci kansa cikin rashin wutar lantarki na kusan kwanaki goma bayan da babban layin dakon wutar lantarkin ya durkushe.Shirin Najeriya A Yau zai duba tasirin dawowar lantrakin a yankin na Arewa.
Fri, 01 Nov 2024 - 671 - “Matsin Tattalin Arziki Ya Sa Ba Na Iya Aikina Yadda Ya Kamata”
Send us a textAlamu sun nuna cewa sakamakon kuncin rayuwa da ake fama da shi a Najeriya, ingnacin aikin da ma’aikata suke yi yana raguwa.Aiki yana ingnatuwa ne dai da samun wasu abubuwa da suka hada da kyakkyawan yanayin wurin aiki da isasshen hutu da kwanciyar hankali da kuma biyan bukatar ma’aikaci a dukkan lokaci.Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai tattauna ne kan yadda matsin tattalin arziki ke shafar ayyukan ma’aikata da ma masu aikin hannu a Najeriya.
Thu, 31 Oct 2024 - 670 - Dalilan Da Ake Cin Zarafin ‘Yan Najeriya
Send us a textCin zarafi da daidaikun alumma ke fuskanta a Najeriya yayin da suke gudanar da ayyukan su na yau da kullum ba sabon abu bane, musamman la’akari da cewa mutanen biyu a mafi akasarin lokaci basu san abun da doka ta tanada game da cin zarafi ba.A wasu lokuta ma, cin zarafin nan na fito wa ne daga wadanda suke rike da madafun iko, inda zaka ga suna bayyana cewar ‘’zan keta maka haddi kuma babu abun da zai faru’’.Shirin Najeriya A Yau zai yi duba ne kan wannan batu na Cin Zarafi.
Tue, 29 Oct 2024 - 669 - Ko Wadanne Dalilai Ne Ke Sanya Wasu ‘Yan Najeriya Ajiye Ababen Hawan Su?
Send us a textTsadar man fetur a Najeriya ya tilastawa da yawa daga cikin ‘yan kasa ajiye ababen hawan su inda suka koma bin na haya don zuwa wuraren aiki, Ziyara da sauran zirga-zirgar su ta yau da kullum.A baya manyan biranen Najeriya su kan cika su batse da ababen hawa da kan yi zirga-zirga da kai kawo, wanda wasu suke ganin wadata da fin karfin bukatun yau da kullum ne ke sanya hakan.Shirin Najeriya A Yau na wannan rana yayi duba ne kan yanda wasu ‘yan Najeriya suke ajiye ababen hawan su ...
Mon, 28 Oct 2024 - 668 - Kuncin Da Arewa Ta Shiga Sakamakon Rashin Wutan Lantarki
Send us a textFiye da mako guda ke nan wasu sassan arewacin Najeriya suna fama da rashin wutar lantarki.Hakan ya haddasa gagarumar matsala a rayuwar mutane da dama.Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai duba irin halin matsi da mazauna yankin suka shiga sakamakon daukewar wutar lantarkin.
Fri, 25 Oct 2024 - 667 - Ko Garambawul Din Da Tinubu Ya Yi Zai Kawo Wa ’Yan Najeriya Sauki?
Send us a textA karon farko tun bayan rantsar da shi, Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi sauye-sauye ga Majalisar Ministocinsa.’Yan Najeriya dai sun dade suna jiran wannan garambawul din na Shugaban Kasa; said ai abin tambaya shi ne: mene ne zai biyo bayan wannan garambawul din?A kan wannan batu shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari.
Thu, 24 Oct 2024 - 666 - Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da CNG
Send us a textGalibin ’yan Najeriya ba su san amfanin da sauya ababen hawansu daga masu amfani da man fetur zuwa masu amfani da iskar gas ta CNG ke da shi ba, musamman a wannan lokaci da ake fama da tsadar man fetur.’Yan Najeriya da dama dai suna amfani da man fetur ne saboda karancin wuraren sauya ababen hawan da sauran dalilai.Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kan irin abubuwan da ya kamata ’yan Najeriya, musamman masu ababen hawa, su sani game da iskar gas din ta CNG.
Tue, 22 Oct 2024 - 665 - Sai Da Kudi Mai Yawa Za Ku Iya Cin Abinci Mai Gina Jiki?
Send us a textGalibin ’yan Najeriya sun koma cin abin da suka samu ba tare da sun yi la’akari da abin da zai gina musu jiki ba, musamman a wannan lokaci da suke fama da matsin tattalin arziki.Sai dai masana sun ce ba sai mutum ya kashe kudi mai yawa ba zai iya cin abincin da zai gina mishi jiki ba.Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi duba a kan irin abincin da mutane za su iya ci da kudi kalilan kuma su samu abin da suke bukata.
Mon, 21 Oct 2024 - 664 - Faduwar Tanka A Jigawa: “Mun Kasa Cin Abinci Tun Da Abin Ya Faru”.
Send us a textAl’ummar Majiya a Jihar Jigawa na ci gaba da jimamin mutuwar mutum sama da dari sakamakon hadarin tankar mai.Saboda tashin hankalin da suke ciki, wasu daga cikin mazauna garin sun ma ce sun kasa cin abinci.Shirin Najeriya a Yau zai tattauna da wasu daga cikin ’yan uwan wadanda abin ya shafa game da yadda suka ji da faruwar wannan lamari.
Thu, 17 Oct 2024 - 663 - Fashewar Tankar Mai: Asarar Da Al’ummar Majiya Suka Tafka
Send us a textGalibin waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon fashewar tankar man da ta yi ajalin sama da mutum 150 a garin Majiya na Jihar Jigawa matasa ne.Ɗaya daga cikinsu, Hassan Hamza, matashi ne da ya yi karatu a fannin Harhaɗa Magunguna, karatun da ake matuƙar buƙatar masu yinsa a tsakanin al’umma.A shirin Najeriya a Yau na lokacin za mu yi nazari ne a kan girman asarar da al'ummar Jami’ar Jihar Jigawa ta tafka.
Fri, 18 Oct 2024 - 662 - Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Ganin Tasirin Cire VAT Kan Kayan Abinci
Send us a textDaya daga cikin nau’ukan harajin da gwamnatoci suke karba shi ne harajin VAT wanda akan dora a kan kayayyaki ko hidimomi.Tasirin wannan haraji a kan farashin kayayyaki ya sa gwanatin Najeriya dauke harajin a kan wasu kayan abinci.Amma bayan watanni da daukar wannan mataki, ’yan Najeriya ba su ga tasirin yin hakan ba.Shirin Najeriya A Yau zai bincika dalilan da suka sa hakan.
Tue, 15 Oct 2024 - 661 - Shin Cire Tallafin Mai Ne Ya Jefa ’Yan Najeriya Cikin Kunci?
Send us a textGalibin Najeriya suna rataya alhakin kuncin rayuwar da suke fama da shi kacokan a kan janye tallafin man fetur.Sai dai wasu masan suna ganin idan ma janye tallafin yana taka rawa, to akwai wasu matakan da suke bayar da gudunmawa mai tsoka.Ko wadanne matakai ne wadannan?Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci za iyi kokarin warware zare da abawa.
Mon, 14 Oct 2024 - 660 - Me Ya Sa ’Yan Najeriya Suka Fara Yanke Kauna Da Samun Sa’ida?
Send us a textMuhawara ta barke a Najeriya bayan sanar da aka sanar da karin farashin man fetur a gidan gidajen mai na NNPC a kan wane ne zai kare muradun ’yan kasa, ya hana a yi musu hawan kawara?’Yan kasa da dama dai na ganin wannan kari a matsayin wani karin mataki na takura wa rayuwarsu, wadda tuni dama take cikin wani yanayi na tsaka-mai-wuya.
Fri, 11 Oct 2024 - 659 - Alakar Lafiyar Kwakwalwa Da Sakamako Mai Kyau A Wurin Aiki
Send us a textMajalisar Dinkin Duniya ta ayyana ranar 10 ga watan Oktoba a duk shekara a matsayin Ranar Lafiyar Kwakwalwa ta Duniya.Taken bikin a bana dai shi ne “Kulawa Da Lafiyar Kwakwalwa A Wurin Aiki”.Don haka ne shirin Najeriya A Yau za iyi nazari a kan alakar da ke tsakanin lafiyar kwakwalwar da ingantuwar aiki.
Thu, 10 Oct 2024 - 658 - Abin Da Ke Kawo Rashin Kyautata Wa Kwastoma a Najeriya
Send us a textA makon farko na watan Oktoba a duk shekara ake bikin Makon Kwastomomi a fadin duniya. A lokuta da dama dai akan samu matsaloli da kalubale a tsakanin abokan ciniki.A kan hanyoyin warware waɗannan matsaloli shirin Najeriya a Yau na wannan lokacin zai tattauna.
Tue, 08 Oct 2024 - 657 - Yadda Kudin Crypto Ya Sanya Matasa Yin Saki-Na-Dafe
Send us a textMatasa da dama a Najeriya ne suka yi sake-reshe-kama-ganye saboda hangen Dala.Saboda tunanin zai samu kudi masu yawa ta hanyar kudin kirifto na Hamster, John Adams ya yi murabus daga aikinsa, daga karshe ya tashi ba tsuntsu ba tarko – ma’ana, babau aikin babu kudin.Shirin Najeriya A Yau zai tattauna ne a kan halin da wadannan matasa suka tsinci kan su ciki bayan mining din Hamster.
Mon, 07 Oct 2024 - 656 - Me Zai Faru Idan Aka Dawo Da Tallafin Man Fetur?
Send us a textYayin da halin kuncin da ’yan Najeriya suke fama da shi yake karuwa, yawan masu kira da a dawo da tallafin man fetur ma sai karuwa yake yi.Sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba: shin me zai faru idan da za a dawo da tallafin?Wanne hali tattalin arzikin Najeriya zai shiga?Shirin Najeriya A Yau zai yi kokarin amsa wadannan da ma wasu tambayoyin masu alaka da su.
Fri, 04 Oct 2024 - 655 - Abin Da Ya Sa Ake Yawan Samun Hadarin Kwalekwale A Neja
Send us a textJihar Neja na cikin jihohin da aka fi samun hadarin kifewar kwalekwale a Najeriya.Hadari na baya-bayan nan shi ne wanda ya auku a Karamar Hukumar Mokwa, inda wani kwalekwale mai dauke da mutum sama da 100,000 ya yi alkafura. Shirin Najeriya A Yau zai tattauna ne kan dalilan hadurran irin wannan da kuma mutanen da abin ya rutsa da su.
Thu, 03 Oct 2024 - 654 - Me Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Shaukin Ranar Samun ’Yancin Kai?
Send us a textA duk lokacin da bikin tunawa da Ranar Samun ’Yancin Kai ya zagayo, bisa al’ada, akan ga ’yan Najeriya suna farin ciki.Sai dai a wannan karon alamu na nuna abin ya sauya; ba kamar yadda aka saba gani a shekarun da suka gabata ba, mutane da dam aba su ma san ana yi ba.Shirin Najeriya A Yau zai yi duba ne kan dalilan da suka sa ’yan Najeriya ba sa shauki kamar yadda aka saba gani a da.
Tue, 01 Oct 2024 - 653 - Rawar Da Fassara Ke Takawa Wajen Habbaka Harshen Hausa
Send us a textYau ce Ranar Fassara ta Duniya wadda Majalisar Dinkin Duniya ta ware don jinjina ga ayyukan kwararrun da suke hada al'ummomi waje daya, da karfafa zaman lafiya da tsaro a duniya ta hanyar juya bayanai daga wani harshe zuwa wani. Albarkacin wannan rana, shirin Najeriya A Yau zai tattauna ne kan irin gudunmawar da fassara ke bayarwa wajen habbaka harshen Hausa.
Mon, 30 Sep 2024 - 652 - Rashin Aikin Yi Da Hanyoyin Magance Su A Najeriya.
Send us a textRashin aikin yi na daya daga cikin manyan kalubalen da najeriya ke fuskanta a wannan lokaci, musamman la’akari da yanda ake cigaba da samun matasa dake da karfi a jika amma babu aikin yi.Hukumar kididdiga ta kasa ta fitar da bayanan dake baiyana cewa rashin aikin yi ya karu a najeriya da kaso 5.3 a farkon wannan shekarar, kazalika binciken ya baiyana cewa wadanda basu yi karatu mai zurfi ba sun fi wadanda suka yi karatu mai zurfi samun aikin yi.Wadansu dalilai ne ke kara kawo ra...
Fri, 27 Sep 2024 - 651 - Shin Karin Kudin Ruwa Zai Farfado Da Tattalin Arzikin Najeriya?
Send us a textA lokuta daban-daban, Babban Bankin Najeriya (CBN) kan ƙara kuɗin ruwa, ya kuma ce yana yin hakan ne da nufin daidaita tattalin arziki. Shin wanne irin tasiri wannan mataki yakan yi a kan tattalin arziƙin da ma rayuwar ’yan Najeriya? Shirin Najeriya a Yau zai yi nazari a kan wannan batu.
Thu, 26 Sep 2024 - 650 - Hakikanin Dalilan Nasarar APC A Zaben Gwamnan Jihar Edo
Send us a textDuk da kokawa da ’yan Najeriya suke ci gaba da yi game da wahalhalun da suke sha wadanda suka zargi manufofin Gwamnatin Tarayya ta APC da haddasa musu, wasu sun ce bas u yi mamaki ba da al’ummar Jihar Edo suka zabi jam’iyyar.Sai dai kuma abin tambaya shi ne: mene ne hakikanin dalilinsu na yin haka?Shirin Najeriya A Yau zai yi binciken kwakwaf a k kan ikirarain shugabannin APC cewa amincewa da salon mulkin jam’iyyar ne ya sa al’ummar Jihar Edo suka zabe ta.
Tue, 24 Sep 2024 - 649 - Alkiblar Da Edo Za Ta Fuskanta Bayan Zaben Monday Okpebholo
Send us a textA karshe dai Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ayyana Monday Okpebholo a matsayin zababben Gwamnan Jihar Edo.Ya yi nasarar lashe zaben da aka gudanar ranar Asabar ne dai bayan ya kayar da ’yan Takara 16.To ko me wannan nasara take nufi ga Jihar da al’ummarta?Wannan na cikin tambayoyin da shirin Najeriya a Yau zai amsa a wannan lokacin.
Mon, 23 Sep 2024 - 648 - Turka-Turkar Da Ta Dabaibaye Zaben Jihar Edo
Send us a textMasu fashin baki sun nuna fargabar yiwuwar samun hatsaniya yayin zaben gwamna da za a gudanar a Jahar Edo ranar Asabar. Sai dai kuma al’ummar jIhar sun ce ko ana ha-maza-ha-mata za su fito su kada kuri’a.Shirin Najeriya a Yau zai yi nazari ne a kan irin tanadin da masu ruwa da tsaki ke yi wa wannan zabe
Fri, 20 Sep 2024 - 647 - Matakan Da Wasu Al’ummomi Suke Dauka Don Guje Wa Ambaliyar Ruwa
Send us a textWasu al’ummomi a Najeriya sun fara ɗaukar matakan kauce wa asarar da ambaliyar ruwa ka iya haifar musu idan aka buɗe Madatsar Ruwa ta Lagdo da ke Jamhuriyar Kamaru.A kwanan nan ne dai Hukumar da ke Kula da Albarkatun Ruwa ta Najeriya ta ce yankunan da ke gaɓar Kogin Binuwai a jihohi 11 na fuskantar barazanar ambaliyar.Shirin Najeriya a Yau zai yi nazari a kan wadannan matakai da ma hanyoyin magance matsalar gaba ɗaya.
Thu, 19 Sep 2024 - 646 - ‘Mun Yi Zaton Samun Sauki Da Zuwan Matatar Dangote’
Send us a text‘Yan Najeriya sun yu ta sa ran zuwan matatar Dangote zai samar da saukin wahalhalun man fetur.Sai dai tun ba a je ko ina ba ana ta samun musayar kalamai tsakanin kamfanin NNPCL da Dangote kan batun.Shirin Najeriya a Yau zai tattauna kan yadda farshin man fetur ke ci gaba da karuwa duk da zuwan matatar Dangote
Tue, 17 Sep 2024 - 645 - “Akwai Yiwuwar Kwata Ambaliyar Borno A Wasu Jihohin”
Send us a textRahotanni sun ce al’ummomin wasu yankuna a wasu jihohin Najeriya suna zaman ɗar-ɗar bayan da ruwa ya fara mamaye gonaki da gidajensu.Tun bayan mummunar ambaliyar ruwa a Maiduguri, hukumomi a Najeriya suke kara ankarar da al'ummomin wasu jihohin cewa akwai yiwuwar samun ambaliyar.Shirin Najeriya a Yau zai tattauna kan yadda za a dauki matakan kan-da-garki kan yiwuwar ambaliyar.
Mon, 16 Sep 2024 - 644 - Yadda Mazauna Maiduguri Za Su Kubuta Daga Illolin Ambaliya
Send us a textBayan mummunar ambaliyar ruwar da ta mamaye kusan kashi 70 cikin 100 na Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, masana na bayyana fargaba game da yiwuwar barkewar cututtuka da kuma ta'azzarar manyan larurori ga masu dauke da su. Shirin Najeriya a Yau zai tattauna a kan yadda al'ummar birnin na Maiduguri za su kare kansu kuma su tsira da lafiyarsu.
Fri, 13 Sep 2024 - 643 - Shin Dole Ne Sai An Dauki Tsauraran Matakan Saita Najeriya?
Send us a textDuk da kokawa da Yan Najeriya ke ci gaba da yi kan irin manufofin gwamnati da suka ce suna Kara jefa su cikin kangin rayuwa.Amma, a ko da yaushe Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu Yana kara nanata cewa, tilas ne a dauki tsauraran Matakai na saita tattalin arzikin kasar, idan har ana bukatar Jin dadi a nan gaba.Shirin Najeriya a Yau zai tattauna ne, kan ko tilas ne sai an dauki tsauraran Matakan, kafin saita tattalin arzikin Najeriya?
Thu, 12 Sep 2024 - 642 - Dabarun Magance Matsalolin Najeriya
Send us a textDaga cikin manyan hakkokin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya dorawa shugabanni, shine kirkirar dabarun samarwa Yan kasa saukin tsadar Rayuwa da tabbatar da kasancewar su cikin walwala.Sai dai, a baya-bayan nan, Yan Najeriya na ci gaba da nuna rashin gamsuwa irin dabarun da shugabanninin ke amfani dasu wajen magance matsalolin da kasar ke fuskanta.Shirin Najeriya a Yau ya tattauna ne, kan irin dabarun da suka kamata shugabanninin Najeriya suyi amfani dasu, wajen magance matsalo...
Tue, 10 Sep 2024 - 641 - 'Karin Farashin Mai Ya Fara Tilasta 'Yan Najeriya Ajiye Aiki'
Send us a textKarin farashin man fetur da NNPCL ya yi a baya-bayan nan, na kara jefa 'yan Najeriya cikin kunci da rashin tabbas a rayuwar yau da Kullum.Tsadar kayayyaki musamman na abinci da sufuri, ya fara tilasatawa wasu Ma'aikata ajiye aiyyukan suShirin Najeriya a Yau ya zai yi dubi kan illar yanayin ga wadanda abin ya shafa, da ma tattalin arzikin kasa.
Mon, 09 Sep 2024 - 640 - Mece Ce Illar Zub-Da Kimar Najeriya A Kasashen Ketare?
Send us a textSau da dama, ana yawan batun yadda 'yan Najeriya ke bata wa kasar suna sakamakon ayyukan assha da suke aikata wa a kasashen ketareWasu na alakanta wannan lamari da yadda ake ganin 'yan wasu kasar na yiwa 'yan Najeriyar gani-gani a kasashen nasu.Shirin Najeriya a Yau ya tattauna kan ne, kan wannan batu.
Fri, 06 Sep 2024 - 639 - Hanyoyin Magance Kuncin ‘Yan Najeriya Cikin Gaggawa
Send us a textAna ci gaba da samun koke-koke game da yadda ‘yan kasa ke ji a jikinsu.Masana dai na ganin akwai matakan da in har gwamnati ta dauke su za a iya kawar da matsin tattalin arzikin da ta yi wa talaka dabaibayi.Shirin Najeriya a Yau zai tattauna kan matakan gaggawa da suka kamata gwamnati ta dauka domin kaiwa share hawayen ‘yan kasa.
Thu, 05 Sep 2024 - 638 - Me Zai Faru Idan Aka Kara Kudin Mai A Najeriya?
Send us a textA dai-dai lokacin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da kukan tsadar kayayyaki sakamakon irin manufofin gwamnati, musamman ma cire tallafin man Fetur, kwatsam sai ga wani rahoto ya fito daga kamfanin mai na kasa wato NNPCL dake nuni da yiyuwar karin farashin man fetur din.Shirin Najeriya a Yau, ya kalli yadda wannan batu zai yi tasiri ga rayuwar ’yan Najeriya.
Tue, 03 Sep 2024 - 637 - Kuncin Rayuwar Da Ambaliya Ke Jefa Mutane
Send us a textA duk lokacin da aka samu intila'in ambaliyar ruwa, rayuwar wadannan abin ya shafa kan shiga cikin halin ha'ula'i sakamakon tsananin matsin rayuwa da suke kasancewa a ciki.Irin wadannan mutane sukan rasa abin da zasu ci, da sauran muhimman abubuwan more rayuwa.Shirin Najeriya a Yau, ya kalli irin wannan yanayi da wadanda ambaliyar ruwan ta shafa ke kasancewa a ciki.
Mon, 02 Sep 2024 - 636 - Yadda Ambaliya Ke Raba Dubban ‘Yan Najeriya Da Muhallansu
Send us a textWata Babbar matsala da ambaliyar ruwa ke haifarwa a Najeriya ita ce, yadda dubban mutane ke rasa muhallansu a duk shekara.Alkalumman hukumar bayar da Agajin gaggawa ta NEMA sun nuna cewa kawo yanzu, ambaliyar ta raba kusan mutum dubu 208,655 da muhallansu a jihohi 28.Shirin Najeriya a Yau, ya tattauna kan irin matakan da suka kamata a dauka domin kaucewa matsalar da hakan ka iya haifarwa ga al'umma.
Thu, 29 Aug 2024 - 635 - Yadda Ya Kamata Alaka Ta Kasance Tsakanin 'Yan Sanda Da Al'umma
Send us a textBabban alhakin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya dora wa rundunar Yan Sanda shi ne kare rayuka da dukiyoyin yan kasa.Sai dai a lokuta da dama, akan samu fito-na-fito da 'yan kasa ke yi da 'yan sandan sakamakon zargin wuce gona da iri wajen gudanar da aiyyukan nasu.Shirin Najeriya a Yau ya tattauna kan yadda ya kamata alaka ta kasance tsakanin jami'an 'yan sanda da al'ummar kasa.
Tue, 27 Aug 2024 - 634 - Me Ya Sa 'Yan Siyasa Ke Naɗa Tarin Mataimaka A Gwamnati?
Send us a textGwamnatoci a matakai daban-daban na ta ikirarin rage kashe kudin gwamnatin ko tsuke bakin aljihu.Sai dai masu sharhi na gani wasu masu mukaman siyasa ke nada tarin mataimaka wadanda wasu ma ba lallai sun taba ido biyu da su ba.Shirin Najeriya a Yau zai yi sharhi ne kan rawar da masu taimaka wa ‘yan siyasa da yawa ke taka wa.
Mon, 26 Aug 2024 - 633 - Gudummuwar ‘Yan Najeriya Wajen Cin Hanci Da Rashawa
Send us a textMasana na ganin kaso mafi tsoka na ‘yan Najeriya suna bada gudummuwa wajen cin hanci da rashawa.Ta fuskar addinai ma akwai yadda ake kallon matsayin cin hanci.Shirin Najeriya a Yau zai maida hankali kan irin kallon da al’umma ke yi wa cin hanci da kuma yadda suke bada gudummuwa a kai.
Fri, 23 Aug 2024 - 632 - Shin Har Yanzu Akwai Masu Matsakaicin Karfi A Najeriya?
Send us a textWane mizani kuke amfani da shi wajen auna masu matsakaicin karfi ko wadata ko kuma masu karamin karfi a Najeriya?Shirin Najeriya a Yau zai tattauna kan matsayin da za a iya dora yadda al'umma ke rayuwa.
Thu, 22 Aug 2024 - 631 - Yadda Bacewar Kananan Takardun Naira Ke Shafar Kasuwanci
Send us a textA 'yan kwanakin nan da wuya a ci karo da kanana takardun Naira.Wasu na ta'allaka hakan da rashin abubuwan da za a iya siya a wannan kudade.Shirin Najeriya a Yau ya yi nazari kan bacewar kanana takardun Nairar da yadda haka ke shafar kasuwanci.
Tue, 20 Aug 2024 - 630 - Mece Ce Cutar Kyandar Biri Kuma Me Ke Jawo Ta?
Send us a textAn samu ɓarkewar cutar ƙyandar biri a ƙasashen Afrika, wadda majalisar Ɗinkin Duniya ke ganin cutar za ta iya tsallake Nahiyar. Hukumar yaki da cutuka ta Najeriya ta ce ta samu akalla mutane 39 da suka harbu da cutar daga farkon shekarar nan zuwa yanzu, inda WHO ta ayyana dokar ta baci kan wannan cuta.Shirin Najeriya a Yau zai tattauna kan abubuwan da suka kamata ku sani game da cutar kyandar birin.
Mon, 19 Aug 2024 - 629 - Me Doka Ta Ce Idan Mutum Bai Iya Rera Taken Najeriya Ba?
Send us a textBayan cece-ku-cen da aka yi ta yi game da wani kuduri da majalisa ta so gabatar wa domin hukunta wadanda suka kasa rera taken Najeriya, an jingine batun.Shin wane hurumi taken Najeriya ke da shi a cikin dokar kasa?Abin da shirin Najeriya a Yau zai tattauna a kai kenan.
Fri, 16 Aug 2024 - 628 - Shin Matasa Sun Shirya Karbar Ragamar Shugabanci A Najeriya?
Send us a textMatasa na ta hankoron a ba su dama domin su jagoranci shugabanci da dora shugabanni na gari.Sai dai wasu na ta diga ayar tambaya ko matasan za su iya tabuka abin kirki ba tare da sun bayar da kunya ba.Shirin Najeriya a Yau ya tattauna kan yiwuwar matasan na iya yin abin da ya dace.
Thu, 15 Aug 2024 - 627 - Dabarun Fara Kananan Sana’o’i A Najeriya
Send us a textWata babbar matsala da ke yawan kashe sana’o’i musamman kanana da matsakaita ita ce ta rashin sanin makamar sana’ar kafin shigarta.Shin me ya kamata masu sana’o’in su sani domin tsaya wa daram a kowane hali?Shirin Najeriya a Yau zai tattauna kan abubuwan da ya kamata masu sana’o’in hannu su rike da kyau domin dorewar sana'arsu duk da irin matsin tattalin arzikin da ake ciki.
Tue, 13 Aug 2024 - 626 - Wane Sauyi Zanga-Zangar Tsadar Rayuwa Ta Kawo?
Send us a textKwana 10 masu zanga-zanga tsadar rayuwa suka ware a fadin Najeriya.Sai dai a wasu wuraren ba ta wuce tsawon kwanaki biyu zuwa uku baShirin Najeriya a Yau zai yi fashin baki kan abin da zanga-zangar ta haifar a Najeriya.
Mon, 12 Aug 2024 - 625 - Abin Da Ya Kamata Ku Sani Kafin Siyan Hannu Jari A Banki
Send us a textA ‘yan kwanakin nan bankuna da kansu suke bukatar mutanr su zo don zuba hannun jari ko da kudi kalilan ne.Masana hada-hadar kudi na ganin zuba jari a fannin na da tasiri kuma ana iya a girbar abin da aka shuka idan an daceShirin Najeriya a Yau ya tattauna game da wasu mahimman abubuwa da suka kamata ku sani idan kuka yi kudurin siyan hannun jari a bankuna.
Fri, 09 Aug 2024 - 624 - Tasirin Fitattun ‘Yan Soshiyal Midiya Wajen Sauya Ra’ayin Al’umma
Send us a text A duk lokacin da wani maudu’i ke tashe a soshiyal midiya a kan samu wasu fitattaun mutane a shafukan da ke tsokaci a kai Irin wadannan mutane su ake kira influencers a turance, kuma suna tsokaci kan batutuwan da mutane tattauna wa.Shirin Najeriya a Yau zai tattauna kan yadda fitattun masu amfani da shafukan sada zumunta ke tasiri ga rayuwar al’umma.
Thu, 08 Aug 2024 - 623 - Yadda Zanga-Zanga Ke Durkusar Da Sana’o’i Da Tattalin Arziki
Send us a textWasu jihohi an sanya dokar hana fita yayin da ake ci gaba da zanga-zanga a Najeriya.Masu sana’o’i na ci gaba da korafin yadda hakan ke durkusar da sana’o’insu.Shirin Najeriya a Yau zai yi nazari akan tasirin zanga-zanga ga sana’o’i da tattalin arziki.
Tue, 06 Aug 2024 - 622 - 'Abin Da Ya Sa 'Yan Najeriya Ba Su Gamsu Da Jawabin Tinubu Ba'
Send us a textAna ci gaba da bayyana mabanbantan ra’ayoyi tun bayan jawabin shugaba Tinubu kan tsadar rayuwa.Wasu na ganin kamar bai tabo inda yake musu kaikayi ba, musamman game da batun nan na tallafin man fetur.Shirin Najeriya a Yau zai yi sharhi kan abin da ya sa ‘yan kasar ba su gamsu da jawaban shugaban ba.
Mon, 05 Aug 2024 - 621 - Kuskuren Da Gwamnati Ta Yi Har Aka Fara Zanga-Zanga
Send us a textYadda zanga-zangar tsadar rayuwa ke gudana a Najeriya na cigaba da daukan hankali al'umma.Ana ganin wasu lamuran ba su tafi daidai ba saboda matakan da aka yi ta dauka ba su yi tasiri ba.Shirin Najeriya a Yau ya yi sharhi ne kan abin da gwamnati ta yi sakaci da shi har mutane suka kai ga yi ma ta zanga-zanga.
Fri, 02 Aug 2024 - 620 - A Ina Shinkafar Gwmanatin Tarayya Ta 40,000 Ta Maƙale?
Send us a textMutane na ta tambaya inda shinkafar nan da gwamnatin tarayya ta ce a siyar ga yan kasa kan Naira 40,000 take.Shin ya ake ciki game da shinkafar yayin da wasu gwamnonin jihohi ke cewa har yanzu ba a basu wannan shinkafar mai tallafin ba.Shirin Najeriya a Yau ya tattauna kan wannan batu.
Thu, 01 Aug 2024 - 619 - Yadda Sabon Mafi Karancin Albashi Zai Iya Daidaita Al’amura
Send us a textShugabann Kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan sabon mafi karancin albashi na Naira 70,000.Yayin da ma’aikata ke ganin za su fara shagali, a gefe guda wasu masu kamfanonin da ‘yan kasuwa na ganin kamar an dora musu nauyin da ya fi karfinsu.Shirin Najeriya a Yau ya tattauna kan sauyin da za a iya samu saboda sabon albashin.
Tue, 30 Jul 2024 - 618 - Dalilin Takaddama Kan Rushe Hukumomin Raya Biranen Kaduna
Send us a textMajalisar Dokokin Jihar Kaduna ta soke dokar da ta kirkiri hukumomin raya wasu biranen jihar uku.Wannan mataki dai ya haifar da zazzafar muhawarar a kan nasabarsa da nuna yatsa da ake yi a tsakanin gwamnati mai ci da wadda ta gada.Shirin Najeriya a Yau zai binciki dalilin daukar wannan mataki da yadda zai shafi ci gaban kananan hukumomin da abin ya shafa.
Fri, 26 Jul 2024 - 617 - Shin Zanga-Zanga Na Tasiri A Najeriya?
Send us a textA lokuta da dama idan ran ‘yan kasa ya baci su kan dauki matakin nuna fushinsu ga gwamnati ta hanyar zanga-zanga.Ana yawan kokwantn shin zanga-zangar da ake gudanarwa a Najeriya suna haifar da ɗa mai ido? Ta wace hanya zanga-zanga ta zama silar samar da maslaha?Ku biyo mu cikin Shirin Najeriya a yau.
Thu, 25 Jul 2024 - 616 - Abin Da Masu Zuba Jari Suke Gudu Daga Najeriya
Send us a textMasana na nuna fargaba game da rashin tabbas a harkar zuba jari a Najeriya.Tun a watannin da suka gabata ake ta samun ficewar manyan kamfanoni daga kasar, lamarin da ake alakantawa da wasu tsare-tsaren tattalin arziki.Shirin Najeriya a yau zai tattauna kan yadda hakan zai ci gaba da tasiri a kan tattalin arzikin Najeriya.
Tue, 23 Jul 2024 - 615 - Alaƙar Da Ke Tsakanin Masu Haƙar Ma’adanai Da ‘Yan Bindiga
Send us a textJihohin Zamfara da Neja a Arewacin Najeriya na cikin jihohin da ke fuskantar kalubalen tsaro duk da tarin ma’adanai da suke da su.Sai dai duk da zafin hare-haren da ake samu a wadannan jihohi aikin hakar ma’adanai na ci gaba kamar yadda aka saba.Shin wace alaka ke tsakanin masu hakar ma’adanai da ‘yan bindiga? Wani binciken da Daily Trust ta gudanar ya gano haka, kamar yadda za ku ji a cikin shirin Najeriya a Yau.
Mon, 22 Jul 2024 - 614 - ‘Yadda APC Ke Kokarin Rufe Bakin Masu Sukar Gwamnati’
Send us a textAna musayar yawu kan ’yancin ’yan kasa na fadin albarkacin bakinsu game da manufofin gwamnati mai ci.’Yan adawa na zargin jam’iyar APC mai mulki da kokarin rufe bakin masu yi mata gyara a inda ta yi kuskure.Shirin Najeriya a yau zai tattauna ne a kan abin da ya sa hakan yake faruwa.
Fri, 19 Jul 2024 - 613 - Me Ya Sa Gwamnoni Ke Rige-Rigen Yin Zaben Kananan Hukumomi?
Send us a textGwamnoni da dama a Najeriya sun bayyana aniyarsu ta gudanar da zabukan kananan hukumomi kafin karshen wannan shekarar. Zuwa yanzu jihohi 13 aka lissafa za su gudanar da zabubbukan, lamarin da wasu ke alakantawa da hukuncin Kotun Koli da ya bai wa kananan hukumomin ’yancin cin gashin kai.Shirin Najeriya a yau zai yi bincike ne don gano gaskiyar wannan lamari.
Thu, 18 Jul 2024 - 612 - Abin Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Azumin Tasu’a Da Ashura
Send us a textA yau ne ake kammala azumin Tasu'a da Ashura, wato na kwanakin Tara da Goma cikin watan farko na kalandar Musulunci da Musulmai ke yi.Azumi ne da ake yi cikin watan Muharram, wanda malamai ke cewa yana daya daga cikin watanni hudu mafiya Alfarma a shekarar Musulunci.Shirin Najeriya a Yau ya duba yadda ake azumin Tasu'a da Ashura da muhimmancin shi ga rayuwar Musulmai.
Tue, 16 Jul 2024 - 611 - Yadda Matasa Za Su Gina Rayuwarsu Da Ta Al’umma
Send us a textYau ce Ranar Matasa Masu Sana’a ta Duniya.A wannan shekarar Majalisar Dinkin Duniya, wadda ta ayyana wannan rana, tana son a yi amfani da basirar matasa wajen samar da zaman lafiya da ci gaba.Shirin Najeriya a Yau zai duba yadda wanann buri zai cika.
Mon, 15 Jul 2024 - 610 - Wane Sauyi 'Yancin Cin Gashin Kai Zai Kawo A Kananan Hukumomi?
Send us a textHukuncin kotun koli kan ikon kananan hukumomi ya jefa su cikin farin ciki a fadin Najeriya.Sai dai yanzu abin da ake son ganin ya faru shi ne yaushe wannan tsari zai yi tasiri kuma me ya rage ga kananan hukumomi.Shirin Najeriya a Yau ya yi fashin bakin kan abin da hukuncin ya kunsa da mataki na gaba ga kanana hukumomi.
Fri, 12 Jul 2024 - 609 - Rayuwar Sheikh Dahiru Bauchi Cikin Ƙarni Guda
Send us a textA wannan makon babban malamin Addinin Musulunci Sheikh Dahiru Usman ya samu ni’imar cika shekara 100 a duniya.Malamai da mabiya da al’umma sun jinjina yadda ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidima ga Addini.Shirin Najeriya a Yau zai yi nazari a kan gudummuwar da Shehin Malamin ya bayar a cikin shekara fiye da 70 da ya yi yana karantar da Al-Kur’ani.
Thu, 11 Jul 2024 - 608 - Gaskiyar Magana Kan Bullar Kungiyar Luwadi Da Madigo A Kano
Send us a textLabarin bullar wata kungiyar da ake zargin tana rajin yada akidar auren jinsi a Kano na ci gaba da yamusta hazo.Tuni hukumomi suka bayyana matakin da za su dauka a kan wadannan zarge-zarge duk da yake sun amince cewa sun taba ganawa da kungiyar.Shirin Najeriya a Yau zai bincika yadda aka yi ana zaton wuta a makera, ta tashi a masaka.
Tue, 09 Jul 2024 - 607 - Dalilin Dawowar Layukan Mai A Najeriya
Send us a textJihohi da dama a wannan lokaci sun fada cikin yanayin dogayen layukan mai da kuma karancinsa.Wasu gidajen mai sun kasance a kulle yayin da masu siyarwar kuma farashin sai wanda ya gani, baya ga ‘yan bumburutu da ke cin kasuwarsu a bayan fage.Shirin Najeriya a Yau domin jin dalilin wahalar mai a Najeriya
Mon, 08 Jul 2024 - 606 - Abin Da Ya Sa Ake Ƙara Wa ‘Yan Band A Kuɗin Wutar Lantarki
Send us a textZuwa yanzu masu shan wutar lantarki da ke tsarin Band A sun samu sanarwar kara kudin wutar lantarkiSai dai wasu na ganin ba a iya biyan bukatun da wannan kari ba zai samu muhalli ba Shirin Najeriya a Yau zai tattauna ne kan Dalilin da ya sa ake kara wa masu tsarin Band A kudin lantarki a kai a kai.
Fri, 05 Jul 2024 - 605 - Abin Da Dokar Ta-Baci Kan Man Fetur Ke Nufi
Send us a textAna ta musayar ra’ayin bayan da Kamfanin man fetur na kasa NNPCL ya ayyana dokar ta-ɓaci kan harkokin haƙowa da kuma fitar da ɗanyen mai daga ƙasar.Mutane na neman amsar shin me hakan ke nufi, da muhawarar ko hakan abu mai yiwuwa ne?Shirin Najeriya a Yau nzai tattauna kan abin da dokar ta baci kan man fetur ke nufi.
Thu, 04 Jul 2024 - 604 - Hanyoyin Magance Kuncin Da ‘Yan Najeriya Suke Ciki
Send us a textAna ci gaba da samun koke-koke game da yadda ‘yan kasa ke ji a jikinsu.Masana dai na ganin akwai matakan da in har gwamnati ta dauke su za a iya kawar da matsin tattalin arzikin da ta yi wa talaka dabaibayi.Shirin Najeriya a Yau zai tattauna kan matakan gaggawa da suka kamata gwamnati ta dauka domin kaiwa share hawayen ‘yan kasa.
Tue, 02 Jul 2024 - 603 - Abin Da Ke Sa Mutum Ya Fara Tunanin Kashe Kansa
Send us a textA ‘yan kwanakin nan ana samun rahotannin yadda mutane suke kashe kansu.Wasu dai suna alakanta hakan ne da tsananin damuwa ko matsin rayuwa.Shirin Najeriya a Yau zai yi duba na tsanaki don tantance yadda lamarin yake.
Mon, 01 Jul 2024 - 602 - Dalilin Da ’Yan Najeriya Ba Su Tsaftace Muhalli
Send us a textMasu fafutukar kare muhalli suna cewa yadda ’yan Najeriya suke shakulatin bangaro da tsaftar muhalli abin damuwa ne.Yayin da ake bikin Ranar Kula Da Tsaftar Muhalli Ta Kasa a yau, shirin Najeriya a Yau zai tattauna a kan halin da Najeriya ke ciki da abin da hukumomi suke yi game da tsaftar muhalli.
Fri, 28 Jun 2024 - 601 - Kimar Sarakunan Gargajiya A Idon Al’ummar Arewa
Send us a textA baya-bayan nan ana samun muhawara, wani lokaci ma zazzafa, a kan kimar masarautun gargajiya.Shin yaya al’umma ke kallon sarakunan gargajiya a halin yanzu?Shirin Najeriya a Yau zai tattauna a kan kimar masu rike da masautun gargajiya a wannan zamani.
Thu, 27 Jun 2024 - 600 - 'Taron Tsaro Zai Samar Da Zaman Lafiya a Arewa Maso Yamma'
Send us a textGwamnonin Arewa maso yamma suna wani babban a taron tsaro da nufin lalubo hanyar kawar da matsalar tsaro a yankin.Hukumar Raya Kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya ce ta shirya taron da hadin gwiwar Kungiyar Gwamnonin Arewa maso Yamma domin hada kan gwamnatocin yankin.Shin ta wace hanya gwamnonin za su iya cimma wannan buri? Ku biyo mu a cikin shirin Shirin Najeriya a Yau
Tue, 25 Jun 2024 - 599 - Alamomin Da Suke Nuna Alhaji Ya Yi Hajji Karɓaɓɓe
Send us a textYayin da aka kammala aikin Hajjin bana ana sa ran duk wanda ya je kasa mai tsarki ya yi Hajji karbabbe.Amma ko akwai wasu alamomin da suke nuna cewa Hajjin mutum ya karbu? Shirin Najeriya a Yau na dauke da karin bayani.
Mon, 24 Jun 2024 - 598 - Yadda Za Ku Fahimci Shari’ar Masarautun Kano Dalla-Dalla
Send us a textMasu bibiyar tirka-tirkar masarautun Kano na ci gaba da shiga ruɗani bayan hukuncin Babbar Kotun Tarayya.Ko wane bangare na murnar shi ne yake da nasara, lamarin da ya sa mutane tambayar shin wane ne Sarki?Don fahimtar inda wannan hukuncin ya dosa, ku biyo mu cikin shirin Najeriya a Yau.
Fri, 21 Jun 2024 - 597 - Shin Ko Kalaman Kwankwaso Sun Kaɗa Hantar APC Ne?
Send us a textWasu kalaman da jagoran Kwankwasiyya Rabi’u Musa Kwankwaso ya furta yana zargin Gwamnatin Tarayya suna ci gaba da tayar da kura.Fadar shugaban kasa da jam’iyyar APC a matakin kasa da jihar Kano sun yi kakkausan suka da kiran a yi maza-maza a kama shi.Shin me ya girgiza Jam’iyyar ta APC game da wadannan kalamai? Shirin Najeriya a Yau zai tattauna kan wannan turka-turka.
Thu, 20 Jun 2024 - 596 - Abubuwan Da Ya Kamata A Yi Don Kawo Karshen Tsadar Abinci
Send us a textA kullum farashin kayan abinci kara tashi yake yi a Najeriya.Masu sharhi kuma suna ta kokarin bayar da shawarwari a kan hanyoyin fita daga wannan yanayi.Shirin Najeriya a Yau zai tattauna kan wadannan hanyoyi da tasirin da za su iya yi.
Tue, 18 Jun 2024 - 595 - Hadarin Da Ke Tattare Da Cin Naman Layya Fiye Da Kima
Send us a textWuce gona da iri wajen cin nama ka iya rikita cikin mutum ya yi ta zarya a banɗakiShirin Najeriya a Yau zai tattauna da masana kan abin da ya kamata ku yi domin kauce wa gurbacewar ciki saboda cin nama
Mon, 17 Jun 2024 - 594 - Shin Mutum Zai Iya Cinye Naman Layyarsa Shi Kadai?
Send us a textA lokacin Bikin Babbar Sallah da mutane kan yi layya, ana sa ran wanda bai yi ba ma ya samu ya ci nama.Amma wasu masu karamin karfi kan bayyana yadda makwabtansu da suka yi layya sukan shige da namansu gida su yi tuwo-na-mai-na.Shirin Najeriya a Yau zai duba halalcin yin hakan a Musulunce.
Fri, 14 Jun 2024 - 593 - 'Kananan Hukumomi Na Daf Da Zama Mabarata'
Send us a textGwamnatocin Kananan Hukumomi sun koka cewa za a dora musu nauyi idan har aka amince da N62,000 a matsayin mafi karancin albashi.Sai dai ma’aikatansu na ganin ba su dalilin fadin hakan, ganin yadda suka samu ninkin kudaden shiga bayan cire tallafin man fetur.Ku biyo mu cikin Shirin Najeriya a Yau domin jin yadda za a warware wannan takaddama.
Thu, 13 Jun 2024 - 592 - Yadda Gurɓacewar Iska Ke Shafar Rayuwar ‘Yan Najeriya
Send us a textGurbacewar iska na ci gaba da jan hankalin masu ruwa da tsaki a duniya.Hukumomi sun ce ‘yan Najeriya na amfani da wasu abubuwa da ke bayar da gudummuwa wajen gurbacewar iskar da muke shaka da barazana ga lafiyar dan adam.Shin ya girmar matsalar take a Najeriya? Shirin Najeriya a Yau ya tattauna kan wannan batu.
Tue, 11 Jun 2024 - 591 - Abin Da Ya Sa Tamowa Ke Nema Ta Gagari Kundila A Arewa
Send us a textKiraye-kiraye na karuwa game da matakin da ya kamata a dauka don dakile matsalar karancin abinci mai gina jiki wato tamowa a jikin kanan yaraKungiyar likitoci ta 'Doctors Without Borders' ta ce an samu ƙaruwar yara masu fama da tamowa a jihohi 11 da ke arewacin Najeriya.Shirin Najeriya a Yau zai duba matakan da za ya kamata a dauka don kare kai daga kamuwa da tamowa.
Mon, 10 Jun 2024 - 590 - Me Manoma Suka Shirya Wa Daminar Bana?
Send us a textA yayin da damina ta fara kankama a wasu sassan Najeriya, fatan manoma shi ne samun yabanya mai kyau.Akwai matakan da masana ke ganin ya kamata manoma su dauka duk a lokacin da ruwa ya fara sauka domin kauce wa lalacewar amfanin gona.Shirin Najeriya a Yau ya tattauna kan matakan da suka kamata manoma za su dauka a wannan yanayi.
Fri, 07 Jun 2024 - 589 - Mafi Karancin Albashi: Shin Me Ma’aikata Suke Fatan Samu?
Send us a textYayin da muhawara ta yi zafi a kan mafi ƙarancin albashi, inda kungiyoyin kwadago ke bukatar a biya Naira 494,000, wasu kamfanoni da gwamnati kuma suke ganin a yi karin da hankali zai dauka, me ma’aikata da kansu suke ganin ya fi dacewa? Shirin Najeriya a Yau zai duba wannan domin an ce mai daki shi ya san inda yake yi mishi yoyo.
Thu, 06 Jun 2024 - 588 - Yadda Yajin Aiki Ke Durkusar Da Sana’o’i
Send us a textA duk lokacin da ’yan kwadago suka tsunduma yajin aiki ana cewa suna kassara tattalin arziki.Shirin Najeriya a Yau zai tattauna a kan yadda yajin aiki yake shafar rayuwar al’umma.
Tue, 04 Jun 2024 - 587 - Dalilin Ƙarancin Tumatur Da Sauran Kayan Miya
Send us a textFarashin kayan miya, musamman tumatur, ya yi tashin gwauron zabo a kasuwanni.Lamarin dai ya sa wasu komawa sayen busasshen tumatur domin yin girki. To shin me ya sa ake samun karanci da tsadar tumatur da sauran kayan miya?Shirin Najeriya a Yau ya ziyarci wasu kasuwanni don jin dalili.
Mon, 03 Jun 2024 - 586 - Yadda Aka Shekara 25 Ana Yi Wa Ɓangaren Shari’a Hawan Ƙawara
Send us a textBangaren shari’a yana cikin ginshikai uku na mulkin dimokradiyya.A cikin shekara 25 da aka yi ana mulkin dimokradiyya ba tare da katsewa ba wannan bangare ya fuskanci kalubale da dama.Shirin Najeriya a Yau ya yi duba a kan wannan lamari.
Fri, 31 May 2024 - 585 - Yadda Dawo Da Tsohon Taken Ƙasa Zai Mayar Da Najeriya Baya
Send us a textDawo da tsohon taken Najeriya da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi na shan yabo da suka.Mutane da dama dai na cewa a yanzu talakan Najeriya ba abin da yake bukata ba ke nan.Shirin Najeriya a Yau zai duba alfanun dawo da taken da muhimmancinsa a mizanin bukatun ’yan Najeriya.
Thu, 30 May 2024 - 584 - Matakan Kauce Wa Yaɗuwar Cututtuka Da Damina
Send us a textA yankuna da dama an fara samun ruwan sama, duk da cewa damina ba ta yi karfi ba a wasu wuraren.Bayanai sun nuna cewa a irin wannan lokaci Kwalara ko amai da gudawa da Maleriya da Thypoid da dai sauransu na cikin cututtukan da ke saurin yaduwa.Shirin Najeriya a Yau zai tattauna a kan wasu daga cikin waɗannan cututtuka da matakan kauce musu.
Tue, 28 May 2024 - 583 - Abin Da Ya Haddasa Dambarwar Sarauta A Kano
Send us a textA ‘yan shekarun da suka gabata tsohon gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya sanya hannu a kan wata doka da ta karkasa Masarautar Kano gida biyar, daga bisani kuma ya tsige sarkin Kano na 14 bisa zargin aikata ba daidai ba da rashin da’a.Yanzu kuma gashi shekaru hudu bayan hakan, gwamnan Kano na yanzu Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata dokar da ta soke wadancan matakan da kuma sake tabbatar da Muhammadu Sanusi kan matsayinsa na Sarkin Kano.Shin a nan, mene ne ya bambanta ...
Mon, 27 May 2024 - 582 - Abu Na Gaba Da Zai Faru Da Sarakunan Kano Da Aka Tuɓe
Send us a textBatun cire sarakun da aka faro ta kamar wasa ga shi ta tabbata.Sarki Sanusi shi ne sarkin da ya sake dawowa bayan tube sarakuna biyar na jihar, lamarin da za a iya cewa wasu sun yi hasashen hakan tun da fari.Shin mene ne mataki na gaba da ya rage wa sarakunan? Ya alaka za ta kasance tsakanin wadanna gidajen sarautar. Shirin Najeriya a Yau ya tattauna kan wannan batu.
Fri, 24 May 2024 - 581 - Shin Ganawar Atiku Da Obi Na Kaɗa Hantar APC?
Send us a textAlkiblar siyasa da ke kaɗawa daga ɓangaren ‘yan adawa ta fara daukar hankalin jam’iya mai mulki.Yawaitar ganawar da aka hangi wasu jiga-jigan adawa na yi ta sa ana diga ayar tambaya me ke shirin faruwa, lamarin da jam’iyar APC ta ce 'yan Najeriya za su bude idanunsu kada su yarda da irin mutanen da tace suna kasuwar bukata.Toh shin wannan ganawa na rikita APC ne? Shirin Najeriya a Yau ya yi nazari kan yadda ganawar jam’iyyun adawa ta fara kaɗa guguwar siyasar kasar.
Thu, 23 May 2024 - 580 - Tasirin Auna Hauhawar Farashi A Rayuwar Talaka
Send us a textWata kalma da ’yan Najeriya ke yawan ji ita ce ƙimar hauhawar farashi, wato ‘Inflation rate’ a turance. Sai dai kuma ba kowa ne ya fahimci abin da Kalmar take nufi ba, balle ya san yadda ake auna hauhawar farashin.Shin ta yaya yan kasa za su gane tasirin hakan a rayuwarsu ta yau da kullum? Shirin Najeriya a Yau zai yi kokarin amsa muku wadaannan tambayoyi. Ku biyo mu
Tue, 21 May 2024
Podcasts semelhantes a Najeriya a Yau
- Al-Quran Al-kareem Al-Quran Al-kareem
- DIBACAIN HORROR Angie Ginting
- Cakap Masjid Berita Harian Singapura
- Ceramah Habib Novel Alaydrus Ceramah Habib -Novel Alaydrus
- CNN Indonesia CNN Indonesia
- dakwah.me - Ustadz Adi Hidayat dakwahme
- KH ANWAR ZAHID OFFICIAL Dakwah NU
- Riri Cerita Anak Interaktif Educa Studio
- Ngaji Bareng Gus Baha Gus Baha
- Hanan Attaki Hanan Attaki
- Kajian Ustadz Khalid Basalamah Kajian Islam
- K.H. ZAINUDDIN MZ K.H. ZAINUDDIN MZ
- Kumpulan Dakwah Islam Lentera Pagi
- Ludruk Cak Kartolo dkk Ludrukan
- Murottal Qur'an Terjemahan Audio Indonesia Muslim
- Trio Burulu Nusendra Hanggarawan
- Kumpulan Dakwah Sunnah PodcastSunnah
- M. Quraish Shihab Podcast Quraish Shihab
- Wayang Kulit Indonesia Raden Ontoseno
- Radio Rodja 756 AM Radio Rodja 756AM
- Sandiwara Radio Bahasa Jawa (Javanese-Language Radio Drama) sandiwararadio.diy
- Spesial Horor Spesial Horor
- Sinau Bareng Cak Nun Telat Cerdas
- Ustad Das'ad Latif Ustad Das'ad Latif