Nach Genre filtern

Ilimi Hasken Rayuwa

Ilimi Hasken Rayuwa

RFI Hausa

Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-daban na duniya, tare da nazari kan irin ci gaban da aka samu wajen binciken kimiya da fasaha da ke neman saukakawa Dan’adam wajen tafiyar da rayuwarsa a duniya. Shirin kuma zai yi kokarin jin irin bincike da masana ke yi domin inganta rayuwar Bil’adama. Shirin na zo maku ne, a duk ranar Talata a shirye-shiryenmu na safe, a ku maimata ranar Alhamis.

382 - Rashin malamai ya tilasta iyaye janye yaransu daga makarantu a kudancin Najeriya
0:00 / 0:00
1x
  • 382 - Rashin malamai ya tilasta iyaye janye yaransu daga makarantu a kudancin Najeriya

    Shirin Ilimi hasken rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda iyaye a yankin kudancin ƙasar ke janye yaransu daga Makarantu saboda ƙarancin makarantu a yankin. Jihar Abia na sahun ƴan gaba gaba da ke fama da wannan matsala inda a baya-bayan nan aka tarin yaran da suka daina zuwa makaranta.

    Wed, 06 Nov 2024
  • 381 - Gwamnatin Bauchi na shirin mayar da yara fiye da miliyan 1 makarantu

    Shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda gwamnatin jihar Bauchi a Najeriya ke yunƙurin mayar da yara fiye da miliyan guda makaranta a wani yanayi da ake ganin ƙaruwar yaran da basa zuwa makaranta a yankin arewacin kasar.

    Tuni masu ruwa da tsaki a wannan yanki suka yi maraba da matakin gwamnatin ta Bauchi, lura da yadda yunƙurin zai taimaka matuƙa wajen rage ɗimbin yaran da ke gararamba ba tare da zuwa makaranta ba a Arewacin na Najeriya.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin...

    Tue, 29 Oct 2024
  • 380 - Ɓanagrorin ilimi sun koka da matakin JAMB na durkusar da harshen Faransanci

    Sannu a hankali darussan nazarin harshen faransanci na kara karbuwa a manyan makarantun Nigeria, sai dai kuma, wani matakin da hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu ta JAMB a Nigeria, ta aiwatar, na cire takardar shaidar share fagen shiga jami’a ta karatun  harshen faransanci, daga cikin darussan da hukumar ta JAMB ke bayar da guraben karatunsu a manyan makarantu ya daga hankalin masu ruwa da tsaki.

    Thu, 24 Oct 2024
  • 379 - Yadda wasu gwamnoni a Najeriya ke biris da yaran talakawa da suka tura karatu wasu kasashe

    Shirin na wannan rana ya duba yadda wasu gwamnonin a Najeriya ke daukar alhakin tura yaran talakawa wasu kasashe domin karatu amma kuma daga bisani sai gwamnatin ta yi biris da sha'aninsu.

    Tue, 15 Oct 2024
  • 378 - Yadda jami’o’i a Najeriya ke neman tallafin inganta ƙirƙirarriyar fasaha ta AI

    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya duba yadda wasu manyan jami’o’i a Najeriya ke neman tallafin ƙasashen da suka ci gaba kan yadda za a inganta ƙirƙirarriyar fasaha ta AI. Tuni kuma suka gabatar da wannan buƙata tasu a wajen taron da ƙungiyar bunkasa ilimi ta ƙasashen Turai kan shirya duk shekara, inda a wannan shekara Faransa ta karbi baƙuncin irin wannan taro da ya samu halartar jami'oi 6 da aka zabo daga Najeriya.
     

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.......

    Tue, 08 Oct 2024
Weitere Folgen anzeigen