Filtrar por gênero
Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-daban na duniya, tare da nazari kan irin ci gaban da aka samu wajen binciken kimiya da fasaha da ke neman saukakawa Dan’adam wajen tafiyar da rayuwarsa a duniya. Shirin kuma zai yi kokarin jin irin bincike da masana ke yi domin inganta rayuwar Bil’adama. Shirin na zo maku ne, a duk ranar Talata a shirye-shiryenmu na safe, a ku maimata ranar Alhamis.
- 382 - Rashin malamai ya tilasta iyaye janye yaransu daga makarantu a kudancin Najeriya
Shirin Ilimi hasken rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda iyaye a yankin kudancin ƙasar ke janye yaransu daga Makarantu saboda ƙarancin makarantu a yankin. Jihar Abia na sahun ƴan gaba gaba da ke fama da wannan matsala inda a baya-bayan nan aka tarin yaran da suka daina zuwa makaranta.
Wed, 06 Nov 2024 - 381 - Gwamnatin Bauchi na shirin mayar da yara fiye da miliyan 1 makarantu
Shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda gwamnatin jihar Bauchi a Najeriya ke yunƙurin mayar da yara fiye da miliyan guda makaranta a wani yanayi da ake ganin ƙaruwar yaran da basa zuwa makaranta a yankin arewacin kasar.
Tuni masu ruwa da tsaki a wannan yanki suka yi maraba da matakin gwamnatin ta Bauchi, lura da yadda yunƙurin zai taimaka matuƙa wajen rage ɗimbin yaran da ke gararamba ba tare da zuwa makaranta ba a Arewacin na Najeriya.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin...
Tue, 29 Oct 2024 - 380 - Ɓanagrorin ilimi sun koka da matakin JAMB na durkusar da harshen Faransanci
Sannu a hankali darussan nazarin harshen faransanci na kara karbuwa a manyan makarantun Nigeria, sai dai kuma, wani matakin da hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu ta JAMB a Nigeria, ta aiwatar, na cire takardar shaidar share fagen shiga jami’a ta karatun harshen faransanci, daga cikin darussan da hukumar ta JAMB ke bayar da guraben karatunsu a manyan makarantu ya daga hankalin masu ruwa da tsaki.
Thu, 24 Oct 2024 - 379 - Yadda wasu gwamnoni a Najeriya ke biris da yaran talakawa da suka tura karatu wasu kasasheTue, 15 Oct 2024
- 378 - Yadda jami’o’i a Najeriya ke neman tallafin inganta ƙirƙirarriyar fasaha ta AI
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya duba yadda wasu manyan jami’o’i a Najeriya ke neman tallafin ƙasashen da suka ci gaba kan yadda za a inganta ƙirƙirarriyar fasaha ta AI. Tuni kuma suka gabatar da wannan buƙata tasu a wajen taron da ƙungiyar bunkasa ilimi ta ƙasashen Turai kan shirya duk shekara, inda a wannan shekara Faransa ta karbi baƙuncin irin wannan taro da ya samu halartar jami'oi 6 da aka zabo daga Najeriya.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.......
Tue, 08 Oct 2024 - 377 - Yadda ake ƙara samun yawaitar masu karatun yaƙi da jahilci a Adamawa
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya tattauna ne akan yadda makarantun manya ko kuma na yaƙi da jahilci kamar yadda akan kira su, ke fuskantar ƙalubalen ɗauka ko ilimantar da ɗaliban da yawansu ke ƙaruwa a kullum, adadin da ya zarta na makarantun manyan da ake da su.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Aisha Shehu Kabara......
Tue, 01 Oct 2024 - 376 - Hukumar JAMB ta shirya taro kan bai wa naƙasassu dama
Shirin namu na wannan mako zai yi dubi ne kan yadda hukumar kula da harkar jarabawan shiga jami’o’i a Najeriya wato JAMB da hadin guiwan kungiyar zabiya na kasa ta shirya taron nahiyar Afrika na farko kan baiwa nakasassu ko masu larura ta musamman dangane da harkar ilimi kamar kowani dan adam.
Taron an shirya shi ne dai la’akari da irin kalubalen da masu larura ta musamman ke fama da ita a kasashe masu tasowa kamar Najeriya,kama daga kyama,nuna musu banbanci da dai sauransu.
Tue, 24 Sep 2024 - 375 - Fannin ilimi a Najeriya na fuskantar barazana sakamon matsin tattalin arziki
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya yi duba ne a kan yadda matsin tattalin arziki da kuma tsare-tsaren gwamnati suka kassara fannin ilimi a tarayyar Najeriya. Daga ɓangaren mahukunta jami'o'in suna ganin tsare-tsaren da gwamnati ta bullo da su a fannin ilimi sune suka sanya a wannan lokaci ko da gyare-gyare a jami'o'in basa iya aiwatarwa.
Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin tare da Aisha Shehu Kabara........
Tue, 17 Sep 2024 - 374 - Har yanzu tsarin jagoranci da bada shawarwari na tasiri a makarantu?Tue, 27 Aug 2024
- 373 - Tsarin ilimin Sakandire kyauta a Ghana ya ƙarfafa gwiwar dubban ɗalibai
Shirin ilimi hasken rayuwa tare da Aisha Shehu Kabara a wannan makon ya mayar da hankali kan tsarin bayar da ilimin Sakandiren kyauta a Ghana, wanda ya taimaka matuka wajen ƙara yawan Ɗaliban da ke halarta karatu a wannan mataki.
Duk da cewa shirin ya laƙume kuɗaɗe masu tarin yawa amma gwamnatin ƙasar ta Ghana ta ce ko shakka babu kwalliya ta biya kuɗin sabulu cikin shekaru 5 da fara tsarin.
Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shiri.
Tue, 20 Aug 2024 - 371 - Yadda tsarin koyo da koyarwa a karni na 21 ke saukakawa wurin fahimtar karatu
A wannan mako, shirin ya yi duba ne a kan tsarin dabarun koyo da koyarwa a ƙarni na 21 da ake kira da 21st Century Learning Skills a turance.Tsarin dabarun koyo da koyarwa na ƙarni na 21, an soma amfani da shi tun a shekarar 2001 domin zamanantar da tsarin yadda ake koyarwa ta hanyar samar da dabarun zamani da za su taimaka wa malamai wurin fahimtar da ɗalibai, sannan ɗalibai su ma su ji sauƙin fahimtar abin da ake koyar da su a aji.
A wannan mako, mun dubi yadda tsarin yake aiki tare yadda ya sauƙaƙa wa malamai da ɗalibai wurin fahimtar karatu a wannan zamani musamman a ƙasashe masu tasowa irin Najeriya.
Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraren shirin....
Tue, 30 Jul 2024 - 370 - Karuwar matasan da basa zuwa makaranta a Ghana
Shirin na wannan mako ya mayar da hankali ne kan karuwar matasan da basa zuwa makaranta a Ghana.
Hukumar kididdiga ta kasar GSS ta gano cewa kusan matasa miliyan biyu ne ba sa karatun Boko ko aikin yi ko kuma samun horon sana'o'in dogaro da kai.
Ku danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Abdulkadeer Haladu Kiyawa.
Tue, 23 Jul 2024 - 369 - Yadda tsadar lantarki ke kassara harkokin karatun manyan makarantun Najeriya
A wannan mako, shirin ya mayar da hankali ne kan yadda tsadar kuɗin wutar lantarki ke gurgunta harkokin karatu a manyan makarantun Najeriya.
Kamar yadda aka sani, harkokin gudanarwar yau da kullum na manyan makarantu ba za su taɓa yiwu wa yadda ya kamata ba, muddin babu ingantacciyar wutar lantarki.
To sai dai, baya ga rashin tsayayyiyar wutar a kusan manyan makarantun Najeriya, wata matsalar kuma ita ce ta tsadar wutar a sakamakon ƙarin farashin kuɗin wutar lantarki da gwamnatin ƙasar ta yi.
Wannan dalili ne ya sanya ƙungiyar shugabannin jami’o’in Najeriya, ta yi kashedin cewa jami’o’in tarayyar ƙasar aƙalla 52 ka iya durƙushewa nan ba da jimawa ba, a sakamakon tsadar kuɗin wutar.
Shugabannin Jami’o’in na Najeriya, sun yi wannan gargaɗi ne bayan wani sabon ƙari na kashi 300 da aka yi musu a kwanakin baya.
Kuna iya latsa alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin...
Tue, 16 Jul 2024 - 368 - Dalilan mummunar faduwar jarabawa da daliban jamhuriyar Nijar suka yi a banaTue, 09 Jul 2024
- 367 - Yadda ayyukan ƴan ta'adda suka kassara harkokin Ilimi a Arewacin Najeriya
A wannan mako, shirin ya yi duba ne a kan yadda hare-haren ‘yan ta’adda suka kassara harkokin ilimi a arewacin Najeriya, shekara 10 kenan da 'yan ta'adda suka fara kai hari kan makarantu a Najeriya, lamarin da ya fara faruwa a shekarar 2014 a makarantar sakandaren ‘yan mata ta garin Chibok da ke jihar Borno a Arewa maso gabashin kasar.
Bincike ya nuna cewa, tun bayan harin na 2014, 'yan ta'adda sun ci gaba da kai makamancinsa a kimanin makarantu 17, waɗanda suka haɗa da makarantun Firamare da sakandare da ma manyan makarantun gaba da sakandare, inda suka yi garkuwa da dalibai da dama, an sako wasu bayan biyan kuɗin fansa, wasu kuwa suna rike a hannunsu har zuwa yanzu.
Cikin shekaru goma da fara ƙaddamar da irin wannan ta'addanci kan makarantu da ɗalibai, masana sun bayyana shakku kan gwamnatin Najeriya tare da zarginta da nuna halin ko in kula kan ilimi tare da rayukan al'ummar kasar musamman ɗalibai.
Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin...
Tue, 02 Jul 2024 - 366 - Tasirin sabuwar hanyar koyarwa a duniya
A wannan mako, shirin ya yi duba ne a kan sabuwar hanyar koyarwa, da kuma tasirin da ta ke da shi a harkar ilimi a faɗin duniya, wato Innovative Teaching Method a turance.
Ita dai sabuwar hanyar koyarwa wato Innovative Teaching Method, hanya ce da ta sha bambam da hanyoyin koyarwa da aka saba gani a lokutan baya, domin ita ana koyar da ɗalibai ne bisa doron buƙatarsu ta koyo, ta hanyar amfani da hanyoyin sadarwa na zamani da kuma na’urori, batare da malami ya zama shi ne ruwa kuma shi ne langa ba.
Tue, 25 Jun 2024 - 365 - Yadda jaddawalin karatun Najeriya ke haifar ga koma-baya a Fannin Ilimin KasarTue, 18 Jun 2024
- 364 - Ban-bancin da ke da shi wajen karatun Ilimin kimiyya da fasaha a kasashen Duniya
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako, ya yi duba ne a kan tsarin ilimin kimiyya da fasaha tsantsa hadi da lissafi, wato STEM Education a turance. Mafi yawancin kasashen Duniya da suka ci gaba, na bawa wannan tsari na Ilimin Kimiyya da fasaha tsantsa hadi da Lissafi fifiko a makarantunsu, la’akhari da yadda kimiyya da fasaha a wannan zamani suka zama ginshinkin ci gaba a sararin wannan duniyar.
Kuna iya latsa alamar sauti domin jin cikakken shirin......
Tue, 11 Jun 2024 - 363 - Jami'ar Umaru Musa ta yaye sama da dalibai dubu goma a wannan shekarar
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako ya yi duba ne kan yadda ake ci gaba da samun ci gaba a bangaren daliban da ke zuwa makaranta a yankin Arewacin Najeriya. Jami'ar Umaru Musa 'Yar Adu'a da ke jihar Katsina ta samu nasarar yaye sama da dalibai dubu 10 a wannan shekarar.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin ta re da Abdulkadir Haladu Kiyawa........
Tue, 04 Jun 2024 - 362 - Yadda Jami'o'in Najeriya suka fara mayar da hankali kan karatun koyon sana'aTue, 21 May 2024
- 361 - Yadda Dalibai ke bada gudunmawa wajen sarrafa sinadaran da basa gurbata muhalliTue, 14 May 2024
- 360 - Yadda matasa ke dukufa wajen amfani da Internet don dogaro da kaiTue, 07 May 2024
- 359 - Karuwar masu mallakar takardun kammala karatu na bogi a Najeriya, na barazana ga karewar kwararru
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako ya duba yadda mallakar takardun kammala karatu na bogi a Najeriya ke barzana ga karewar kwararru a fannoni da dama.
Ana fargabar idan har wannan dabi'a ta ci gaba a haka, tabbas za'a rasa kwararru musamman a fannin lafiya, kimiyya da sauransu.
Danna Alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.
Tue, 26 Mar 2024 - 358 - An samar da cibiyar sadarwa a jahar Bauchi don saukakawa dalibai wajen bincike
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa a wannan lokacin ya yi duba ne kan yadda wasu kungiyoyi karkashin cibiyar fasahar sadarwa da ci gaban al’umma wato CITAD suka samar da wata katafariyar cibiyar sadarwa da aka yiwa lakabi da HELLO HOPE a jahar Bauchi. Shirin ya kasance wani bangare na yunkurin saukakawa mazauna karkara hanyoyin samun sadarwa ta internet musamman wuraren da babu irin wannan ci gaba ko kuma wuraren da suke da shi amma bashi da karfi, wanda jama’are ke cikin wannan rukuni.
Kungiyoyin da sun sha alwashin samar da irin wannan cibiyar sadarwa guda 20 a shiyoyin Najeriya shida zuwa karshen wannan shekara domin samar da internet a yankunan karkara.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna........
Tue, 19 Mar 2024
Podcasts semelhantes a Ilimi Hasken Rayuwa
- Global News Podcast BBC World Service
- Kriminálka Český rozhlas
- El Partidazo de COPE COPE
- Herrera en COPE COPE
- The Dan Bongino Show Cumulus Podcast Network | Dan Bongino
- Es la Mañana de Federico esRadio
- La Noche de Dieter esRadio
- Hondelatte Raconte - Christophe Hondelatte Europe 1
- Affaires sensibles France Inter
- La rosa de los vientos OndaCero
- Más de uno OndaCero
- La Zanzara Radio 24
- Espacio en blanco Radio Nacional
- Les Grosses Têtes RTL
- L'Heure Du Crime RTL
- El Larguero SER Podcast
- Nadie Sabe Nada SER Podcast
- SER Historia SER Podcast
- Todo Concostrina SER Podcast
- 安住紳一郎の日曜天国 TBS RADIO
- The Tucker Carlson Show Tucker Carlson Network
- 辛坊治郎 ズーム そこまで言うか! ニッポン放送
- 飯田浩司のOK! Cozy up! Podcast ニッポン放送
- 武田鉄矢・今朝の三枚おろし 文化放送PodcastQR
Outros Podcasts de Educação
- Franck Ferrand raconte... Radio Classique
- Entrez dans l'Histoire RTL
- Au Cœur de l'Histoire Europe 1
- Choses à Savoir - Culture générale Choses à Savoir
- Choses à Savoir HISTOIRE Choses à Savoir
- Les récits de Stéphane Bern Europe 1
- 6 Minute English BBC Radio
- Les Cours du Collège de France France Culture
- Au coeur de l’histoire - Stéphane Bern - l’intégrale Europe 1
- Learning English Conversations BBC Radio
- TED Talks Daily TED
- Histoire criminelle, les enquêtes de Scotland Yard RTBF
- Les salauds de l'histoire RTL
- Histoire Islam Histoire Islam
- Méthode de langues : Anglais Editions Larousse
- Histoires du soir : podcast pour enfants / les plus belles histoires pour enfants Engle
- Entre mystères & secrets : la fascinante histoire des OVNIS RTBF
- Histoire des Gangsters Profession Gangster
- Au Cœur de l'Histoire - Stéphane Bern Europe1
- History Extra podcast Immediate Media