Filtrer par genre
- 338 - Tasirin al'adun gargajiya wajen tafiyar da mulki bayan ficewar turawa
Shirin al'adunmu na Gado tare da Abdoulaye Issa kamar yadda ya saba a wannan makon ma ya leƙo wasu daga cikin masarautun Hausawa don jin tarihi da kuma tasirinsu ga al'umma.
A wannan karon shirin ya yi duba kan tasirin al'adun gargajiya a matsayin jigon tafiyar da shugabanci bayan ficewar turawan Mulkin mallaka a Najeriya.
Haka zalika za kuji hira ta musamman da sarkin Keffi a jihar Nassarawa wato Mai martaba Alhaji Shehu Usman Shindo Yamusa.
Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.....
Wed, 06 Nov 2024 - 337 - Yadda bikin baje kolin cibiyar al'adu ta Nike Art Gallery da ke Lagos ya gudana
Shirin al'adunmu na gado a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda aka gudanar da gagarumin biki baje kolin al'adu a jihar Lagos da ke tarayyar Najeriya. An gudanar da bikin ne a fitacciyar cibiyar al'adu ta Nike Art Gallery, wanda ya shahara a duniya, bikin ya tattaro mutane da dama daga sassan fasaha, kasuwanci, siyasa da diflomasiyya.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Aboulaye Issa........
Tue, 29 Oct 2024 - 336 - Yadda al'adar gaɗa ke shirin gushewa a tsakanin al'ummar HausawaTue, 22 Oct 2024
- 335 - Sarkin Damagaram ya naɗa ɗan Najeriya a matsayin Talban masarautarsa
Shirin Al'adu na wannan makon ya duba irin yanda masarautunmu na gargajiya ke kama hanyar zama ƙasa da ƙasa ta yanda sarakunan wasu masarautun ke nada ƴan wasu ƙasashe don basu mukamin a fadodinsu da sunan ƙarfafa zumunci da kyautata rayuwar jama'ar ƙasashen. A baya-bayan nan, mai Martaba Sarkin Damagaram da ke Jamhuriyar Nijar ya naɗa Alhaji Idriss Ousmane Kwado, a matsayin Talban Damagaram, bikin ya samu halartar gwamnonin jahar Zinder da na Katsina da wasu manyan sarakunan Arewacin Nigeria.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.......
Tue, 08 Oct 2024 - 334 - Yadda aka gudanar da bikin Sallar Gani a Najeriya da Nijar
Shirin Al’adun mu na Gado a wannan makon yayi duba ne kan yadda ake gudanar da bikin Sallar Gani. ita dai wannan sallar na daga cikin dadadun al’adar mallam Bahaushe, kuma har yanzu ana gudanar da wannan biki a wasu masarautu a Arewacin Najeriya da kuma Jamhuriyar Nijar.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.......
Tue, 01 Oct 2024 - 333 - Shirye-shirye na musamman kan tarihin zuwan Turawa ƙasar Hausa
Shirin Al’adun mu na Gado a wannan makon ci gaba ne game da jerin shirye-shiryen da muka faro kan zuwan Turawan mulkin mallaka zuwa ƙasar Hausa. Turawan sha mamakin abinda suka tarar, kasancewar sun samu al’ummar Hausawa da cikakkiyar wayewar addini, sarauta, sutura, karatu da rubutu da kuma wayewar kasuwanci da sauran harkoki na rayuwa.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare ta Abdoulaye Issa.......
Tue, 17 Sep 2024 - 332 - Jerin shirye-shirye kan tarihin zaman takewar ƙasar Hausa kafin zuwan TurawaTue, 10 Sep 2024
- 331 - Yaya tsarin tafiyar da mulki yake a ƙasar Hausa kafin zuwan turawaTue, 27 Aug 2024
- 330 - Yadda sana'ar ƙira ke gushewar a al'adar ƙasar Hausa
A yau shirin za ya kai mu Jamhuriyar Nijar, musaman jihar Maradi.
A wannan yankin na Maradi a garin Radi, zamu duba batun kirar gargajiya da ke kan hanyar bacewa, bayan a can baya kira, wanzamci, sun kasance sana’o’i biyu da ake alfahari da su a cikin gari. A dauri, makeri baya noma a irin wannan lokaci na damina, sai dai ya yi ta aikin kera kayan noma da gyaransu idan sun lalace, idan kaka ta yi dukan manoma sai su hada masa dammuna hatsi, irin su dawa ko ma wake da zai kula da iyalinsa.
Tue, 13 Aug 2024 - 329 - Yadda Kabila Berum a Najeriya ke gudanar da bukukuwan su na al'adaTue, 30 Jul 2024
- 328 - Shirin ya mayar da hankali kan Kabilar Gwari a Najeriya
Shirin na wannan mako zai yi duba ne kan Kabilar Gwari da ake samun su a tsakiyar Najeriya.
Kabilar Gwari da bahaushe ke kira da "Gwarawa" na da al'adu daban-daban masu ban mamaki da suka sha banban da sauran kabilun mutanen da ke kewaye da su.
Domin jin cikakken shirin dannan alamar saurare tare da Abdullahi Isa
Tue, 23 Jul 2024 - 327 - Shirin yayi waiwaye kan rayuwar fitaccen makadin gargajiya marigayi Alhaji Ali na Maliki
Shirin al'adun gargajiya na wannan mako ya mayar da hankali ne kan rayuwar fitaccen mawakin gargajiya na jamhuriyar Nijar Alhaji Ali na Maliki
Mawakin haifafffen kauyen Sarkin arewa dake jihar Maradi a Jamhuriyar Nijar ya kwashe shekaru akalla 80 na rayuwar sa yana taka rawa a fagen na raye-raye da kade-kaden gargajiya.
Shirin ya kuma yi waiwaye kan rayuwar mamacin da ya bar yara 23 a duniya, kuma cikin su guda ya gaje shi.
Dannna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Abduoullaye Issa.
Tue, 09 Jul 2024 - 326 - Yadda al'ummar Wemawe na Benin ke shirya bikin al'adunsu a duk shekaraTue, 02 Jul 2024
- 325 - Irin rawar da masarautu ke takawa wajen kawo sauye-sauyen da suka kamata kashi na 2
Shirin al'adun gargajiya na wannan mako ci gaba ne akan na makon daya gabata wanda ya duba muhimancin sarakunan mu da kuma irin rawar da za su iya takawa a wannan lokaci da ake fuskantar sauye-sauye a fanoni da dama. inda shirin ya tattauna da sarakunan masarautun Macina da kuma ta Nupe.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.........
Tue, 11 Jun 2024 - 324 - Irin rawar da ya kamata masarautu su taka wajen kawo sauye-sauyen da suka kamata
Shirin al'adun gargajiya na wannan mako ya yi duba ne a kan muhimancin sarakunan mu da kuma irin rawar da za su iya takawa a wannan lokaci da ake fuskantar sauye-sauye a fanoni da dama. shirin ya tattauna da sarakunan masarautun Macina da kuma ta Nupe.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.........
Tue, 04 Jun 2024 - 323 - Koken Jama'a a kan yadda hukumomi ke yi wa abubuwan tarihi rikon sakainar kashi
Shirin al'adun gargajiya na wannan mako ya yi duba ne a kan yadda Jama'a ke koken game da rikon sakainar kashi da hukumomi ke yi wa abubuwan tarihi, kamar Makon jiya yau ma shirin ya yi tattaki ne har Kanon Dabo da ke tarayyar Najeriya, inda ya tattauna da shugaban kwamitin raya Al'adun Gargajiya na Majalisar dokokin Jihar, Hon. Sarki Aliyu Daneji.
Ku latsa alamar sauti don jin yadda shirin ya kasance....
Tue, 21 May 2024 - 322 - Yadda Maza da Mata suka rungumi sana'ar Rini a Kano da ke Najeriya
Shirin al'adun gargajiya na wannan mako ya yi tattaki ne har Kanon Dabo da ke tarayyar Najeriya, inda ya yi duba a kan yadda Maza da Mata suka rungumi sana'ar Rini a Karofin Kofar Mata wadda ke da dogon Tarihi.
Shirin ya samu zarafin tattauna wa da Baballiya Hamisu, wanda shi ne mai magana da yawun Marinar ta Kofar Mata.
Tue, 14 May 2024 - 321 - Yadda tsadar rayuwa ke barzana ga Maroka da Sankira a Jamhuriyar Nijar
Shirin al'adun gargajiya na wannan mako ya duba yadda jama'a a Maradi suka koma amfani da ruwan randa a maimakon kankara lokacin azumin watan Ramadana, saboda tsadar kankarar.
Akwai mu dauke da yadda Maroka da kuma Sankira ke fuskantar barazana a sakamakon tsadar rayuwa.
Dannan alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Abdullahi Isa.
Tue, 26 Mar 2024 - 320 - Yadda masarautar Hausawan Turai ke gudanar da ayyukantaTue, 19 Mar 2024
- 319 - Tasirin masu sarautar gargajiya wajen inganta tsaro a yankunansu
A sakamakon gyaran da aka yi wa kundin tsarin mulkin Nigeria na 1976, aka tsame hannun sarakunan gargajiya a kasar cikin sha’anin kula da harkokin tsaro da harkokin shari’ah da kuma batun tara haraji a cikin al’ummarsu.
Hakan ne ya sanya Sarakuna duk da kasancewarsu iyayen kasa, suka koma gefe inda suka zamo ‘yan kallo kan wadannan al’amura.
Amma yayinda gwamnatin Nigeria ke tunanin sake damka wa Sarakuna wannan dama, wasu daga cikin su fara bijiro da sabbin matakai da nufin tsare rayuka da dukiyar al’ummarsu daga ‘yan ta’adda.
A baya bayan nan, Mai Martaba Sarkin Ningi a jihar Bauchi, Alhaji Yunusa Muhammad ‘Danyaya, ya samar da wata katafariyar kungiyar tsaro ta ‘yan sa-kai, wacce ke karade sako da lungun yankin don yaki da miyagun iri.
Tue, 05 Mar 2024 - 318 - Yadda kananan kabilu suka samu wakilci a masarautar Katsinar Maradi
Shirin Al'adun Gargajiya na wannan makon ya ziyarci masarautar Katsina Maradi da ke Jamhuriyar Nijar, inda Sultan Ahmed Ali Zaki ya fitar da wani tsari na nada kananan kabilu a mukaman wakilan al’ummarsu, don kara dankon zumunci tsakanin kabilu sannan da raya al’adun gargajiya a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.Baya ga Fulani da Bugaje da ke zama 'yan gida, Sultan ya nada wakilan Adarawa, Zabarmawa da Tubawa.
Masarautar Katsinar Maradi dai yanzu ta zama madubi kuma abin koyi a bangaren hadin kan al'ummar Nijar.
Tue, 27 Feb 2024 - 317 - Shiri na musamman kan marigayi Salissou Hamissou
Shirin "Al'adunmu na gado" a wannan makon na musamman ne, wanda ya yi duba akan irin gudunmuwar da marigayi Salissou Hamissou ya bayar a bangaren al'adu, musamman a lokacin da ya ke gabatar da wannan shiri na Al'adunmu na gado.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.....
Tue, 20 Feb 2024 - 316 - Yadda al'adar auren Zaga ke shudewa tsakanin kabilar Sayawa a Najeriya
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya yi duba kan yadda auren Zaga tsakanin al'ummar Sayawa ke komawa tarihi, salon al'adar da ke bayar da damar gadon mace ko kuma bayar da kyautar ta da sunan aure.
Duk da tarin kabilun da ake da su a cikin jihohin Najeriya, kowace kabila na da irin nau’o’in al’adunta na gargajiya a fannonin rayuwa dabam dabam.
Al’adun kan bambanta ne ta fuskar tsarin zamantakewa, ko ta fuskar auratayya da makamantarsu.
Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.....
Tue, 13 Feb 2024 - 315 - Yadda wasu abincin gargajiya na bahaushe ke barazanar bacewaTue, 12 Dec 2023
Podcasts similaires à Al'adun Gargajiya
- El Partidazo de COPE COPE
- Herrera en COPE COPE
- Tiempo de Juego COPE
- The Dan Bongino Show Cumulus Podcast Network | Dan Bongino
- Es la Mañana de Federico esRadio
- La Noche de Dieter esRadio
- Affaires sensibles France Inter
- La rosa de los vientos OndaCero
- Más de uno OndaCero
- La Zanzara Radio 24
- L'Heure Du Crime RTL
- El Larguero SER Podcast
- Nadie Sabe Nada SER Podcast
- SER Historia SER Podcast
- Todo Concostrina SER Podcast
- 安住紳一郎の日曜天国 TBS RADIO
- TED Talks Daily TED
- The Tucker Carlson Show Tucker Carlson Network
- 辛坊治郎 ズーム そこまで言うか! ニッポン放送
- 飯田浩司のOK! Cozy up! Podcast ニッポン放送
- 武田鉄矢・今朝の三枚おろし 文化放送PodcastQR
Autres podcasts de Actualités et Politique
- Les Grosses Têtes RTL
- Hondelatte Raconte - Christophe Hondelatte Europe 1
- Entrez dans l'Histoire RTL
- C dans l'air France Télévisions
- Laurent Gerra RTL
- L'œil de Philippe Caverivière RTL
- LEGEND Guillaume Pley
- On marche sur la tête Europe1
- Les récits de Stéphane Bern Europe 1
- Hondelatte Raconte - Cote B Europe 1
- L’heure du crime : les archives de Jacques Pradel RTL
- Enquêtes criminelles RTL
- Bercoff dans tous ses états Sud Radio
- La dernière Radio Nova
- Global News Podcast BBC World Service
- TOCSIN PODCAST TOCSIN MÉDIA
- L'Heure des Pros CNEWS
- Pascal Praud et vous Europe 1
- Culture médias - Thomas Isle Europe 1
- C ce soir France Télévisions