Filtrer par genre
- 589 - Kan yadda kamfanoni ke saye amfanin gonar da aka girbe a Najeriya
A Najeriya a yayin da aka fara girbin amfanin gona, rahotanni daga sassan ƙasar sun bayyana yadda hukumomi, kamfanoni da ɗaiɗaikun mutane ke sayen ɗimbim hatsi su na tarawa, lamarin da ya haddasa tsadar su jim kaɗan bayan da farashi ya fara saukowa.
A cewar masu lura da al’amura, wannan lamari zai ta’azzara tsadar kyayyakin abinci, ganin ayyukan ƴan bindiga su ka hana al’ummomi da dama yin noma.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.
Wed, 13 Nov 2024 - 588 - Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa da damaFri, 08 Nov 2024
- 587 - Ko meke haifar da tarnaƙi a tabbatar da tsaro a arewacin Najeriya?
Ra'ayoyin masu saurare na wannan rana ya mayar da hankali kan yadda aka kwashe watanni biyu bayan da shugaban kasa ya umarci hafsoshin tsaro da su tare a jihar Sokoto don tabbatar da tsaro, amma har yanzu 'yan bindiga na ci gaba da kai hare-hare ba kakkautawa.
Shin ko me ke haifar da tarnaki ga kokarin tabbatar da tsaro a arewacin Najeriya?
Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna
Tue, 22 Oct 2024 - 586 - Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa da damaFri, 18 Oct 2024
- 585 - Ra'ayoyi: Najeriya za ta shafe shekara 100 kafin magance talauci
Bankin Duniya, ya ce Najeriya da wasu ƙasashe da dama masu tasowa, za su iya shafe tsawon shekara ɗari a nan gaba kafin su yi nasarar rage kaifin talauci da ke addabar al’ummominsu.
Wannan gargaɗi na Bankin Duniya na zuwa ne a daidai lokacin da bayanai ke cewa kusan a kowace rana ta Allah ana samun karuwar mutanen da suka dogara da malauna ne domin samun abin da za su ci da kuma iyalansu.
Shin, ko yaya za ku bayyana matsayin talauci ko fara a inda ku ke rayuwa?
Ko kun gamsu da irin matakan da hukumomin ƙasashen ke ɗauka domin rage kaifin talauci a tsakanin al’umma?
Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin
Thu, 17 Oct 2024 - 584 - Ra'ayoyin masu saurare kan kaurace wa karawa da Libya da tawagar Najeriya ta yi
Shirin ra'ayoyin masu sauraro na wannan rana ya maida hankali ne kan yadda tawagar kwallon Najeriya Super Eagles ta kaurace wa buga wasa da takwararta ta Libya sakamakon taskun da suka ci karo da shi lokacin isarsu a lasar ta Libya. Tuni gwamnatin Najeriya ta gayyaci jakadan Libya da ke Abuja don bayyana rashin amincewa da yadda aka tozartar da ƴan wasan na Super Eagles, lamarin da ake ganin cewa ya fara daukar sabon salo daga wasanni zuwa siyasa.
Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin........
Tue, 15 Oct 2024 - 583 - Ra'ayoyin masu saurare kan kwace wa mutane 9 shaidar zama ɗan ƙasa a Nijar
Gwamnantin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar ta sanar da ƙwace wa mutane 9 dukanninsu makusanta ga hamɓararren shugaban kasar Mohamed Bazoum shaidar zama ɗan ƙasa saboda zarginsu da shirya wa ƙasa zagon-ƙasa. Tsohon madugun ƴan tawaye Rissa Ag Boula da kuma Janar-Janar biyu na soji na daga cikin waɗanda wannan mataki ya shafa.
Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a
Mon, 14 Oct 2024 - 582 - Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa da damaFri, 11 Oct 2024
- 581 - NNPCL ya sake ƙara farashin man fetur da kashi 15 cikin 100
Najeriya ta yi sabon ƙarin farashin mai da akalla kashi 15%, wanda kuma shi ne karo na 4 a cikin watanni 16 da shugaba Bola Tinubu ya shafe kan karagar mulki.
Babu dai wani dalili da kamfanin NNPCL da ke matsayin wakilin gwamnati a harkar mai ya bayar dangane da wannan farashi, illa kawai jama’a sun gan shi ne haka kwatsam.
Kan wannan batu shirin 'Ra'ayoyin Masu Sauraro' na ranar Alhamis ɗin nan ya bayar da damar tattaunawa akai.
Fri, 11 Oct 2024 - 580 - Ra'ayoyin Masu Saurare kan ribar da bankunan Najeriya ke samu duk da ƙuncin rayuwa
A Najeriya, yayin a ke fama da matsalar tattalin arziki da tsanantar harkokin rayuwa, alkaluma na tabbatar da cewa bankunan ƙasar na ci gaba samun gagarumar riba a kowace rana ta Allah. Shin ko meye dalilin wannan gibi tsakanin bankuna da kuma al’umma? Wane gyara ya kamata ayi domin tabbatar da cewa arzikin kasa na zagayawa a cikin al’umma? Wannan shine maudu'in da masu sauraro suka tattauna akai.
Wed, 09 Oct 2024 - 579 - Ra'ayoyin masu saurare kan ingancin dimokuraɗiyya a Najeriya
A Najeriya, yanzu haka wasu sun fara nuna fargaba a game da yadda tsarin dimokuradiyya ke gudana a kasar, musamman lura da yadda da zarar aka gudanar da zaben kananan hukumomi, to ko shakka babu jam’iyyar da ke rike da kujerar gwamna ce za ta lashe zaben babu tantama.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da aka bai wa kananan hukumomin damar cin gashin kansu.
Abin tambaya anan shi ne, me ya sa a kullum jam’iyya mai rike da mukamin gwamna ce ke lashe zaben kananan hukomomi a Najeriya?
Meye tasirin hakan game da fatan da ake da shi na ganin cewa al’umma ta morewa tsarin dimokuradiyya daga tushe?
Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a
Tue, 08 Oct 2024 - 578 - Ra'ayoyin masu saurare kan rikicin Gaza da ke cika shekara guda
Yau 7 ga watan oktoban shekarar daya kenan da mayakan Hamas suka kaddamar da hare-hare a Isra’ila, inda suka kashe mutane 1 da 200 tare da yin garkuwa da wasu akalla 150.
Wannan ya fusata Isra’ila inda ta mayar da martani ta hanyar kashe sama da mutane kusan dubu 43 a yankin Gaza, tare da yaduwar wannan rikici zuwa kasashen Lebanan da Iran.
Shin me za ku ce a game da wannan lamari da ke kara jefa cikin zaman zullumi?
Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin
Mon, 07 Oct 2024 - 577 - Ra'ayoyin masu saurare kan tsadar farashin litar fetur
Ana iya cewa murna na neman komawa ciki a Najeriya, bayan da aka yi hasashen cewa da zarar Dangote ya fara shigar da tataccen mai a kasuwa zai wadata sannan akan farashi mai rahusa.
To sai dai ranar farko da fara shiga da man na Dangote, sai kamfanin NNPCL ya sanar da ƙara farashin mai a kasar.
Shin ko me za ku ce a game da wannan sabon karin faraashin mai wanda shi ne karo na uku cikin shekara daya a Najeriya?
Ko meye dalili karuwar farashin mai a Najeriya duka da cewa ana hakowa da kuma tace shi ne a cikin gida?
Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a.
Tue, 17 Sep 2024 - 576 - Ra'ayoyin masu saurare kan bikin maulidi
Yanzu haka al’ummar musulmi a sassan duniya na ci gaba da gudanar da bukukuwan Mauludi, domin tunawa da ranar da aka haifi annabi Muhammad mai tsira da amincin Allah.
Shin ko yaya matsayin wannan rana yake a gare ku?
Ta wace fuska ku ke gudanar da bikin tunawa da wannan ranar?
Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a.
Mon, 16 Sep 2024 - 575 - Ra'ayoyi: Belin miliyan 10 kan masu zanga-zangar yunwa a Najeriya
Kotu a Abujan Najeriya, ta bukaci 10 daga cikin ɗimbin mutanen da aka kama suna zanga-zanga domin yunwa, da ya biya Naira milyan 10 a matsayin kuɗin beli kafin sallamar sa daga gidan yari.
Shin ko ta ina wanda ke fama da yunwa zai fito da Naira milyan 10 domin ya beli kansa?
To me zai faru idan har wani ko wasu suka taimaka da waɗanda kuɗade ba beli?
Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a.
Thu, 12 Sep 2024 - 574 - Ra'ayoyin masu saurare kan ambaliyar ruwa a Afrika
Yamai babban birnin Jamhuriyar, ya fara karɓar baƙuncin taron ƙwararru da saurann masu ruwa da tsaki kan matsalar sauyin yanayi da ta shafe yankin yammacin Afrika.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da sassan yankin na Yammacin Afirka da Sahel ke fuskantar Iftila’in Ambaliyar mafi muni da aka taɓa gani cikin aƙalla shekaru 20, kamar yadda aka gani a garin Maiduguri, inda a baya bayan nan saukar ruwan sama ya janyo tumbatsar dam ɗin da ya fashe, lamarin ya haddasa mummunar ambaliyar da ta mamaye sassan birnin da dama.
Wane hali ake ciki a garin na Maiduguri bayan iftila’in da ya auku?
Wadanne dabaru ya dace a bi wajen daƙile sake aukuwar haka, ko kuma rage girman barazanar da aka gani, ta hanyar karkatar da tarin ruwan da ke ambaliya zuwa ga amfanin jama’a?
Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin
Wed, 11 Sep 2024 - 573 - Ra'ayoyin masu saurare kan buƙatar Katsinawa su tashi su kare kansu
Gwamnan jihar Katsina da ke arewacin Najeriya, Malam Dikko Umaru Radda ya yi kira ga al’umma da ta jajirce wajen kare kanta daga hare-haren ƴan bindiga masu garkuwa da mutane, tare da bai wa jami’an tsaro hadin kai don kawo karshen matsalolin tsaro da suka addabi yankin.
Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a.
Tue, 10 Sep 2024 - 572 - Ra'ayoyin masu saurare kan komawa makarantun boko
A Najeriya, yau ake sake buɗe makarantun firamire da sakandare don fara karatu bayan dogon hutu da aka gudanar.
Ana komawa makarantar ne a wannan karo a cikin wani yanayi na matsanciyar tsadar rayuwa wanda ya samo asali daga sabon ƙarin farashin mai fetur da aka yi a kasar.
Shin a wane yanayi yaranku ke komawa makarantar a wannan litinin?
Ko akwai wani sauyi musamman ta fannin farashin kayan karatu da kuma kudin sufuri?
Mon, 09 Sep 2024 - 571 - Ra'ayoyin Masu Saurare kan batutuwa daban dabanFri, 06 Sep 2024
- 570 - Ra'ayoyin masu saurare kan tasirin taron China da Afrika
An fara taron shekara-shekara don kyautata hulɗa tsakanin China da Afirka wanda ya samo asali kimanin shekaru 24 da suka gabata.
Alƙaluma sun tabbatar da cewa China ita ce ƙasar da nahiyar Afirka ta gudanar da hulɗar tattalin arziki da kasuwanci fiye da kowace nahiya, yayin da a ɗaya bangare bashin da China ke bin Afirka ke ci gaba da ninkawa ninkin-ba-ninkin.
Meye ra’ayoyinku a game da kamun lodayin China a fagen tattalin arziki, siyasa da kuma zamantakewa a nahiyar Afirka?
Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Alheri Haruna.
Thu, 05 Sep 2024 - 569 - Yadda batun ci gaba da biyan tallafin mai a Najeriya ya janyo cecekuce
Shirin ra'ayoyin ku masu saurare na wannan mako ya duba yadda ake fama da matsalar karancin main fetur a Najeriya, wasu bayanai na nuni da cewa yanzu haka gwamnatin ƙasar ta ware naira triliyan 6 da bilyan 800 a matsayin kuɗin tallafi mai a ƙasar.
Bayanai sun ce za a yi amfani da kuɗaɗen ne don biyan tallafin tun daga watan agustan bara har zuwa disambar wannan shekara ta 2024 wato wata watanni 17 cur.
Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Aisha Shehu Kabara
Tue, 20 Aug 2024 - 568 - Ra'ayoyin masu saurare kan gudummawar marigayi Issa Hayatou ga kwallon ƙafa
A makon jiya ne Allah ya yiwa tsohon shugaban hukumar kwallon kafar Afirka Issa Hayatou rasuwa, bayan gajeruwar rashin lafiya. Hayatou da ya kwashe kusan shekaru 30 yana jagorancin hukumar, ya taka rawa sosai wajen ci gaban kwallon kafa a nahiyar, musamman bangaren matasa da kuma ganin an kara wa kasashen Afirka gurbi a gasar cin kofin duniya daga gurabe 2 zuwa 5.
Shin kun gamsu da gudumawar da ya bayar?
Kamar da me za ku tuna wannan gwarzo?
Mon, 12 Aug 2024 - 567 - Ra'ayoyin ƴan Najeriya kan jawabin shugaba Tinubu game da zanga-zanga
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci al’ummar ƙasar su jingine zanga-zanga tare da bayyana aniyar tattaunawa don laluɓo masalaha.
A jawabin da ya gabatar sakamakon zanga-zangar tsadar rayuwa da ta ɓarke a akasarin sassan ƙasar, Tinubu ya shaida wa ƴan Najeriya cewa yana jin raɗaɗin da suke ji, kuma tabbas zai samo mafita.
Yaya wannan jawabi nasa ya riske ku?
Ko ya taɓo batutuwan da suke ci wa al’umma tuwo a ƙwarya?
Wace shawara za ku ba wa masu zanga-zanga?
Mon, 05 Aug 2024 - 566 - Ra'ayoyin masu saurare kan shigar iyayen al'umma cikin ayyukan garkuwa da mutane
Shirin ra'ayoyin ku masu saurare na wannan rana ya duba yadda rashin tsrao da kuma garkuwa da mutane ke kara yawaita a arewacin Najeriya, inda a baya-bayan nan kwamishin yan sandan jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya ya sanar da cafke 'dan majalisar dokoki da hakimi tare da tsohon shugaban karamar hukumar Kaurar Namoda bisa zarginsu da hannu dumu dumu cikin ayyukan garkuwa da mutane domin karbar kuɗin fansa.
Wannan al’amari ya sake tabbatar da zargin da ake yi wa wasu daga cikin shugabanni a Najeriya dangane da taka muhimmiyar rawa a matsalolin tsaron da suka addabi al’ummar ƙasar.
Me za ku ce kan wannan lamari?
Wane darasi ya kamata al’umma su koya?
Wace mafita ce mafi dacewa a bi wajen magance matsalolin tsaron dake tagayyara jama’a?
Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin, tare da Nasiruddeen Muhammad
Tue, 30 Jul 2024
Podcasts similaires à Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare
- El Partidazo de COPE COPE
- Herrera en COPE COPE
- Tiempo de Juego COPE
- The Dan Bongino Show Cumulus Podcast Network | Dan Bongino
- Es la Mañana de Federico esRadio
- La Noche de Dieter esRadio
- Affaires sensibles France Inter
- La rosa de los vientos OndaCero
- Más de uno OndaCero
- La Zanzara Radio 24
- L'Heure Du Crime RTL
- El Larguero SER Podcast
- Nadie Sabe Nada SER Podcast
- SER Historia SER Podcast
- Todo Concostrina SER Podcast
- 安住紳一郎の日曜天国 TBS RADIO
- TED Talks Daily TED
- The Tucker Carlson Show Tucker Carlson Network
- 辛坊治郎 ズーム そこまで言うか! ニッポン放送
- 飯田浩司のOK! Cozy up! Podcast ニッポン放送
- 武田鉄矢・今朝の三枚おろし 文化放送PodcastQR
Autres podcasts de Actualités et Politique
- Les Grosses Têtes RTL
- Hondelatte Raconte - Christophe Hondelatte Europe 1
- Entrez dans l'Histoire RTL
- C dans l'air France Télévisions
- Laurent Gerra RTL
- L'œil de Philippe Caverivière RTL
- LEGEND Guillaume Pley
- On marche sur la tête Europe1
- Les récits de Stéphane Bern Europe 1
- Hondelatte Raconte - Cote B Europe 1
- L’heure du crime : les archives de Jacques Pradel RTL
- Enquêtes criminelles RTL
- Bercoff dans tous ses états Sud Radio
- La dernière Radio Nova
- Global News Podcast BBC World Service
- TOCSIN PODCAST TOCSIN MÉDIA
- L'Heure des Pros CNEWS
- Pascal Praud et vous Europe 1
- Culture médias - Thomas Isle Europe 1
- C ce soir France Télévisions