Filtrer par genre
- 470 - Mu zagaya DuniyaSat, 09 Nov 2024
- 469 - Mu zagaya Duniya: Yadda katsewar lantarki ta kassara kasuwancin a arewacin Najeriya
Shirin Mu Zagaya Duniya na wannan mako tare da Ƙaribullah Abdulhamid Namadobi kamar ko yaushe ya yi duba kan muhimman labaran da suka faru a makon da muke shirin bankwana da shi, ciki kuwa har da batun matsalar wutar lantarkin da yankin Arewacin Najeriya ya yi fama da shi, sai kuma shirye-shiryen tunƙarar zaɓen Amurka da ke tafe a makon gobe.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin wanda ya taɓo ɓangarori daban-daban na duniya kama daga Afrika da nahiyar Turai, Asiya da kuma tashe-tashen hankulan da ake fama da su a sassan duniyar musamman gabas ta tsakiya.
Sat, 02 Nov 2024 - 468 - Yan t'adda daga Burkina Faso na amfani da wani yanki na kasar Ghana a matsayin mafaka
Daga cikin labarun da shirin ya waiwaya akwai, korafin da kungiyar direbobin motocin haya a Najeriya ta gabatar da korafi kan tashin hankalin da mabobinta ke fuskanta, inda ta gabatar da kididdigar da ke nuna cewar, akalla direbobi 50 ‘yan ta’adda suka halaka suka kuma suka yi awon gaba da wasu mutanen da dama daga kan hanyar Gusau zuwa Funtua.
Al’ummar Jamhuriyar Nijar na alhinin rashin da suka yi na tsohon Fira Ministan kasar Hama Amadou, wanda ya rasu a ranar Larabar da ta gabata.Sat, 26 Oct 2024 - 467 - Bitar wasu daga cikin muhimman labarai na al’amuran da suka wakana a makon da ya ƙare
Yayin da ‘Yan Najeriya da dama ke jin jiki kan matsin rayuwar da suka shiga tun bayan janye tallafin man fetur da kuma fara aiwatar da wasu matakai da sabuwar gwamnatin ƙasar ta yi, Bankin Duniya yayi gargaɗin cewar, matsalar da ake ciki samin taɓi ce, muddin aka kuskura aka janye ko dakatar da manufofin tattalin arziƙin da shugaba Tinubu ke aiwatarwa.
Sat, 19 Oct 2024 - 466 - Bitar Labaran mako:- Najeriya ta sake ƙara farashin man fetur karo na 4 a jereSat, 12 Oct 2024
- 465 - Kisan shugaban Hezbollah ya janyo wa Isra'ila ɗimbim hare-hare daga Iran
Daga cikin Labarun da suka fi ɗaukar hankali a makon da ya ƙare akwai jerin makamai masu linzamin da Iran ta kai wa Isra’ila hari da su, a yayin da ita kuma Isra’ilar ta karkatar da hare-haren da take kai wa a Gaza zuwa Kudancin Lebanon, h da zummar murkushe mayakan Hezbolla
A Najeriya kuwa ɗimbin Iyallai ne suka shiga alhinin rashin da suka yi, biyo bayan nuutsewar da wani jirgin ruwa yayi ɗauki da fasinjoji sama da 300 da ke ƙoƙarin tsallaka kogin Kwara domin zuwa taron Maulidi.
Sat, 05 Oct 2024 - 464 - Yadda babban taron zauren Majalisar Ɗinkin Duniya ya gudana
Daga cikin labarun da shirin Mu Zagaya Duniya na wannan makon ya waiwaya, akwai yadda babban taron zauren Majalisar Ɗinkin Duniya ya gudana, haka nan akwai bitar rahoton maƙudan ƙuɗaɗen da ECOWAS ta ware don samar da wutar lantarki a makarantu da cibiyoyin kiwon lafiya, a wasu ƙasashen da ke ƙarƙashinta ciki har da Najeriya, haka nan shirin ya waiwari halin da ake ciki game da rikicin Isra'ila da Hezbollah a Lebanon.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Suleiman.......
Sat, 28 Sep 2024 - 463 - Tsuguni bata kare ba tsakanin kamfanin Dangote da kamfanin NNPC a Najeriya
Har yanzu tsuguni bata kare ba tsakanin kamfanin Dangote da kamfanin NNPC dangane da gabatar da man fetur da yake tacewa a cikin gida. A cikin wannan shirin, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Kasum Kurfi, masanin tattalin arziki da kuma Abdulkarim Ibrahim dangane da kalubale da kuma mafita dangane da wannan al'amari.
Sat, 21 Sep 2024 - 462 - Halin da aka shiga bayan iftila'in ambaliyar ruwa a Maiduguri
Daga cikin labarun da shirin makon nan ya waiwaya akwai iftila’in ambaliyar ruwan da ya afka wa garin Maiduguri babban birnin jihar Borno da kuma halin da aka shiga bayan aukuwar lamarin.
A fannin tsaro kuwa, dakarun sojin Najeriya ne suka samu nasarar halaka ɗaya daga cikin manyan jagororin ‘yan ta’addan da suka addabi al’ummar yankin arewa maso yammacin ƙasar.
Sat, 14 Sep 2024 - 461 - Abdulaziz Abdulaziz ''Gwamnatin shugaba Tinubu na iya bakin kokarin''
Matsalar tsaro na ci gaba da ta'azzara a yankin arewa maso yammacin Najeriya, musamman a yan makwannin da suka gabata, inda 'yan bindiga ke kai hare hare suna kashewa ba tare da kaukauatawa ba. Gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu tace tana iya bakin kokarin ta amma kuma jama'a na cewar har yanzu da sauran aiki.
Sat, 07 Sep 2024 - 460 - Bitar labaran mako: Yadda sabon farashin man fetir ya shafi ƴan NajeriyaSat, 07 Sep 2024
- 459 - Yadda ƙasashen Najeriya da Nijar suka dawo da alakarsu
Shirin Mu Zagaya Duniya na wannan makon ya taɓo batun sake dawo da alaka da aka yi tsakanin Najeriya da Nijar, da yadda aka samu karuwan basukan da kasashen Afrika ke ciwowa daga China da kuma batun neman sanyawa wasu ministocin Isra'ila takunkumi da ƙungiyar tarayyar Turai ta nema mambobinta su yi.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh....
Sun, 01 Sep 2024 - 458 - Bitar labaran mako: Yadda ambaliyar ruwa ke ci gaba da ɓarna a arewacin NajeriyaSat, 17 Aug 2024
- 457 - Shirin ya duba manyan labaran da suka faru a wannan makoSat, 10 Aug 2024
- 456 - Zanga-zangar lumana kan tsadar rayuwa ta rikiɗe zuwa tarzoma a sassan Najeriya
Mu Zagaya Duniya, shiri ne da ya saba tacewa gami da zaɓo wasu daga cikin muhimman labarun lamurran da suka wakana a makon da ya ƙare domin bitarsu tare da Nura Ado Suleiman.
Shirin wannan makon ya fi mayar da hankali ne wajen bitar yadda zanga-zanga kan tsadar rayuwa da kuma neman shugabanci nagari ta gudana a sassan Najeriya, inda a wasu sassa zanga-zangar ta lumana ta rikiɗe zuwa tashin hankalin da ya kai ga hasarar rayuka da kuma ɗimbin dukiya.
'Mu Zagaya Duniya' zai kuma leka Mali, inda dakarun kasar da dama gami da sojojin hayar Rasha na Kamfanin Wagner suka rasa rayukansu, bayan ƙazamin artabun da suka yi da mayakan Abzinawan da suka samu taimakon masu tayar da kayar bayan dake ikirarin jihadi.
Sat, 03 Aug 2024 - 455 - Wasu daga cikin muhimman labarun lamurran da suka wakana a makon da ya ƙare daga Rfi
A ranar Alhamis da ta gabata, shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da naira dubu 70 a matsayin mafi ƙarancin albashi a ƙasar, inda yayi alƙawarin sake nazari kan yiwuwar wani ƙarin a duk bayan shekaru uku, a cikin shirin mu Zagaya Duniya ,Nura Ado Suleiman ya zaɓo wasu daga cikin muhimman labarun lamurran da suka wakana a makon da ya ƙare domin bitarsu.
Sat, 20 Jul 2024 - 454 - Najeriya za ta bayar da damar shigar da kayan abinci ba tare da haraji ba
Shirin duniya kamar yadda aka saba na duba manyan labaran da suka faru a sassan duniya
A cikin shirin zaku ji cewa..............
Gwamnatin Najeriya ta sanar da shirin janye biyan kudaden haraji kan wasu muhimman kayayyakin abinci da ta dage haramcin shigar da su kasar, don saƙaƙawa jama’a raɗaɗin tsadar raywar da suke ciki.
Matakin sojojin da suka yi juyin mulkin a Nijar, Mali da kuma Burkina Faso na tabbatar da ballaewarsu daga ECOWAS ya tayar da hankalin kungiyar kasashen ta yammacin Afirka, a yayin da kwararru ke cigaba da bajakolin ra’ayoyinsu kan matakin.
A Kenya kuwa, shugaban ƙasar William Ruto ne ya kori rankatakaf din ministocinsa sai fa ƙwaya biyu rak da ya bari, ‘yan kwanaki bayan zanga-zanga kan tsadar rayuwa da dubban matsasan kasar suka gudanar.
Danna alamar saurare don jin gundarin shirin tare da Nura Ado Sulaiman.
Sat, 13 Jul 2024 - 453 - Tattaunawa kan wasu daga cikin tarin matsaloli da suka hadabi Najeriya a fanoni daban-dabanSat, 06 Jul 2024
- 452 - Rikicin masarautar Kano ya ɗauki sabon salo
Wasu daga cikin labarun da shirin makon nan ya waiwaya sun haɗa da yadda rikicin masarautar Kano ya ɗauki sabon Salo,, bayan da Gwamnatin jihar ta bada umarnin rushe fadar Sarki dake unguwar Nasarawa, inda Aminu Ado Bayero ya ke, matakin da ya zo sa’o’i kaɗan bayan da babbar Kotun Tarayya da ke jihar ta yanke hukuncin rashin amincewa da sabuwar dokar masarautar
Sat, 22 Jun 2024 - 451 - Gwamnatin sojin Nijar ta kwaɓe wa Bazoum rigar kariya
Daga cikin Labarun da shirin ya waiwaya a wannan mako akwai matakin mahukuntan sojin Jamhuriyar Nijar na cirewa hamabararren shugaban ƙasar Bazoum Muhd rigar kariyar, abinda ya bude kofar samun damar gurfanar da shi gaban kotu.
A Najeriya kuwa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce zai ci gaba da yi wa tattalin arzikin ƙasar garambawul duk kuwa da yadda hakan ke ta’azzara wahlhalun da al’ummar kasar ke sha.
Sai Kuma Senegal inda shugaban kasar Basirou Diomaye Faye ya sassauta farashin kayayyakin masarufi don saukaka wa jama’a tsadar rayuwar da suke ciki.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta sanar da ƙaruwar mutanen da rikici ke tilastawa barin matsugunansu a sassan duniya, adadin da zuwa yanzu ya kai mutum miliyan 120.
Sat, 15 Jun 2024 - 450 - Bitar labaran makon da ya gabata ta cikin shirin "Mu zagaya Duniya"
Shirin Mu zagaya duniya bisa al'ada kan yi bitar muhimman labaran da suka gudana a makon jiya, a wannan makon shirin tare da Nasrudden Muhammad, ya duba kan dambarwar yajin aikin NLC a Najeriya sai kuma yadda Jam'iyyar ANC a Afrika ta kudu ke laluben kafa gwamnatin haɗaka.
Duk dai a cikin shirin za kuma kuji yadda ta ke ci gaba da kayawa a Gaza, bayan da Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare sassan Rafah ciki har da makarantar da ke ƙarƙashin kulawar Majalisar Ɗinkin Duniya.
Waɗannan da ma sauran muhimman labarai na ƙunshe a cikin shirin.
Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin..
Sat, 08 Jun 2024 - 449 - Cikar shugaban shugaban Najeriya Bola Tinubu shekara guda akan karagar mulki
A cikin shirin Mu Zagaya Duniya akwai cikar shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu shekara guda a kan karagar Mulki.
sai kuma yadda asusun Tallafawa Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, yayi A wadai da KARUWAR cin zarafi da take hakkin kananan yara a kasashen Mali da Burkina Faso da kuma Nijar a dalilin ta’azzarar ayyukan kungiyoyin ‘yan ta’adda. da kuma sauran rahotanni da ke biye dasu.
Sat, 01 Jun 2024 - 448 - Gwamna Abba Yusuf ya mayar da Sarki Muhammadu Sunusi kan mukaminsa
Gwamnan Kano Abba Yusuf ya rattaba hannu a wata doka mai rusa ga baki daya masarautun Kano inda ya mayar da Sarki Muhammadu Sunusi kan mukaminsa.
Bashir Ibrahim Idris dangane da wannan mataki ya tattauna da Abdoulkarim Ibrahim da Nura Ado Suleiman a cikin shirin Duniyar mu a yau daga nan sashen hausa na Rfi.
Sat, 25 May 2024 - 447 - Bitar labaran mako: Bikin cika shekaru 17 da kafuwar Sashin Hausa na RFI
Daga cikin labarun da shirin na Muzagaya Duniya ya sake waiwaya akwai cikar Sashin Hausa na RFI shekaru 17 cif da kafuwa. Sai kuma matakin rushe sabbin masarautun da ya baiwa gwmna Abba Kabir Yusuf damar sake naɗa Sarki Muhammadu Sunusi na II a matsayin Sarkin Kano na 16.
A Guinea kuwa, gwamnatin sojin da ke jagorantar ƙasar ce ta rufe wasu kafafen yaɗa labarai da suka hada da gidan talabijin da kuma gidajen radio da dama.
Kotun Duniya ta baiwa Isra’ila Umarnin Dakatar da hare-haren da ta kaiwa a Rafah.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Suleiman.....
Sat, 25 May 2024
Podcasts similaires à Mu Zagaya Duniya
- El Partidazo de COPE COPE
- Herrera en COPE COPE
- The Dan Bongino Show Cumulus Podcast Network | Dan Bongino
- Es la Mañana de Federico esRadio
- La Noche de Dieter esRadio
- Affaires sensibles France Inter
- La rosa de los vientos OndaCero
- Más de uno OndaCero
- La Zanzara Radio 24
- Espacio en blanco Radio Nacional
- L'Heure Du Crime RTL
- El Larguero SER Podcast
- Nadie Sabe Nada SER Podcast
- SER Historia SER Podcast
- Todo Concostrina SER Podcast
- 安住紳一郎の日曜天国 TBS RADIO
- TED Talks Daily TED
- The Tucker Carlson Show Tucker Carlson Network
- 辛坊治郎 ズーム そこまで言うか! ニッポン放送
- 飯田浩司のOK! Cozy up! Podcast ニッポン放送
- 武田鉄矢・今朝の三枚おろし 文化放送PodcastQR
Autres podcasts de Actualités et Politique
- Les Grosses Têtes RTL
- Hondelatte Raconte - Christophe Hondelatte Europe 1
- Entrez dans l'Histoire RTL
- C dans l'air France Télévisions
- Laurent Gerra RTL
- L'œil de Philippe Caverivière RTL
- LEGEND Guillaume Pley
- On marche sur la tête Europe1
- Les récits de Stéphane Bern Europe 1
- Hondelatte Raconte - Cote B Europe 1
- Bercoff dans tous ses états Sud Radio
- L’heure du crime : les archives de Jacques Pradel RTL
- Enquêtes criminelles RTL
- La dernière Radio Nova
- Global News Podcast BBC World Service
- TOCSIN PODCAST TOCSIN MÉDIA
- Culture médias - Thomas Isle Europe 1
- L'Heure des Pros CNEWS
- Pascal Praud et vous Europe 1
- C ce soir France Télévisions