Podcasts by Category

Mu Zagaya Duniya

Mu Zagaya Duniya

RFI Hausa

Shirin Mu Zagaya Duniya na duba Wasu Muhimman Labarai da suka ja hankalin Duniya a cikin mako. Ana gabatar da shirin ne a ranar Asabar da safe a kuma maimaita ranar Lahadi da daddare.

470 - Mu zagaya Duniya
0:00 / 0:00
1x
  • 470 - Mu zagaya Duniya

    Shirin mu zagaya Duniyaya yi dubi da yadda zaben Amurka ya gudana. Karibullah Abdulhamid na Madobi ya gabatar.

    Sat, 09 Nov 2024
  • 469 - Mu zagaya Duniya: Yadda katsewar lantarki ta kassara kasuwancin a arewacin Najeriya

    Shirin Mu Zagaya Duniya na wannan mako tare da Ƙaribullah Abdulhamid Namadobi kamar ko yaushe ya yi duba kan muhimman labaran da suka faru a makon da muke shirin bankwana da shi, ciki kuwa har da batun matsalar wutar lantarkin da yankin Arewacin Najeriya ya yi fama da shi, sai kuma shirye-shiryen tunƙarar zaɓen Amurka da ke tafe a makon gobe.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin wanda ya taɓo ɓangarori daban-daban na duniya kama daga Afrika da nahiyar Turai, Asiya da kuma tashe-tashen hankulan da ake fama da su a sassan duniyar musamman gabas ta tsakiya.

    Sat, 02 Nov 2024
  • 468 - Yan t'adda daga Burkina Faso na amfani da wani yanki na kasar Ghana a matsayin mafaka

    Daga cikin labarun da shirin ya waiwaya akwai, korafin da kungiyar direbobin motocin haya a Najeriya ta gabatar da korafi kan tashin hankalin da mabobinta ke fuskanta, inda ta gabatar da kididdigar da ke nuna cewar, akalla direbobi 50 ‘yan ta’adda suka halaka suka kuma suka yi awon gaba da wasu mutanen da dama daga kan hanyar Gusau zuwa Funtua.
    Al’ummar Jamhuriyar Nijar na alhinin rashin da suka yi na tsohon Fira Ministan kasar Hama Amadou, wanda ya rasu a ranar Larabar da ta gabata.

    Sat, 26 Oct 2024
  • 467 - Bitar wasu daga cikin muhimman labarai na al’amuran da suka wakana a makon da ya ƙare

    Yayin da ‘Yan Najeriya da dama ke jin jiki kan matsin rayuwar da suka shiga tun bayan janye tallafin man fetur da kuma fara aiwatar da wasu matakai da sabuwar gwamnatin ƙasar  ta yi, Bankin Duniya yayi gargaɗin cewar, matsalar da ake ciki samin taɓi ce, muddin aka kuskura aka janye ko dakatar da manufofin tattalin arziƙin da shugaba Tinubu ke aiwatarwa.

    Sat, 19 Oct 2024
  • 466 - Bitar Labaran mako:- Najeriya ta sake ƙara farashin man fetur karo na 4 a jere

    Shirin Mu Zagaya duniya tare da Nura Ado Suleiman kamar ko yaushe ya yi bita ne kan muhimman labaran da suka faru a makon da muke bankwana da shi, ciki kuwa har da ƙarin farashin man fetur ta Najeriya ta sake yi karo na 4 cikin watanni 16 duk da matsi da tsadar rayuwa da ta addabi al'ummar ƙasar.

    Sat, 12 Oct 2024
Show More Episodes