Filtrar por género

Kasuwanci

Kasuwanci

RFI Hausa

Shirin yakan duba yadda kasuwanci da tattalin arizikin kasashen duniya ke ciki. Kana yakan ji sabbin dubaru da hanyoyin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin 'Yan kasuwa da Masana’antu dangane da halin da suke ciki.

339 - Bankin duniya ya ayyana Najeriya a matsayin ƙasa ta uku wajen cin bashi a duniy
0:00 / 0:00
1x
  • 339 - Bankin duniya ya ayyana Najeriya a matsayin ƙasa ta uku wajen cin bashi a duniy

    Wani rahoton Bankin Duniya ya nuna cewa Najeriya ce ƙasa ta uku a yawan basususun kasashen ketare, bayan da ta ƙarbi sama da dalar Amurka biliyan 16.5 kwankwacin naira Triliyan 27 da biliyan 700.

    Da wannan matsayi Najeriya ta na biye ne da ƙasashen Bangladesh mai matsayi na ɗaya da Pakistan ta biyu a yawan basussuka a duniya.

    Sabon rance

    Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da majalisar dattawan najeriyar ta sahalewa shugaba Tinubu karbo sabon rancen naira Tiriliyan 1 da biliyan 700, duk da ikirarin ƙasar na samun ƙudin haraji mai yawa daga hukumar kwastom da sauransu.

    Yawan basussuka

    Bayaga bankin duniya duniya, jummular basussukan da Najeriya ta ƙarbo ya kai naira triliyan 138, wanda hasashe ma ke cewa zai kai dala biliyan 45 kafin karshen wannan shekara ta 2024.

    Wed, 27 Nov 2024
  • 338 - Faɗuwar darajar Naira na shafar kasuwancin dabbobi a iyakar Najeriya da Nijar

    'Shirin Kasuwa A kai Miki Dole' na wannan makon tare da Ahmed Abba ya duba yadda harkokin kasuwanci ke tafiya a kasuwar dabbobi ta ƙasa da ƙasa da ke Maigatari ta Jihar Jigawa, wato kan iyakar Najeriya da Nijar, da kuma jin irin ƙalubalen da kasuwar ke fuskanta.

    Kasuwar ta Maigatari wadda ke iyakar Najeriya da Nijar na daya daga cikin manyan kasuwannin dabbobi a yankin arewacin Najeriya, domin ana sayar da nau'ikan dabbobi da suka hadar da shanu, raƙuma, dawaki, tumaki, awaki da jakkai sama da miliyan biyu a ranakun Alhamis din ko wanne mako, kuma yan kasuwa daga sassan Najeriya, Nijar da kuma Mali na zuwa a duk mako.

    Thu, 07 Nov 2024
  • 337 - Yadda ta kaya a taron bunkasa tattalin arziki ta kafofin internet a Najeriya

    Shirin kasuwa a kai miki dole na wanna mako ya yi tattaki zuwa taron masu ruwa da tsaki ne a fannin bunkasa tattalin arziki ta kafofin internet wadda a turance ake kira digital economic wanda aka gabatar a jihar Lagos a tarayyar Najeriya.

    Wed, 16 Oct 2024
  • 336 - Yadda ƴan kasuwa tsakanin Najeriya da Kamaru ke fuskantar kalubalen rashin hanya

    Shirin Kasuwa Akai Miki Dole na wannan makon ya maida hankali ne kan hada-hadar kasuwaci tsakanin Najeriya da makwabciyarta Kamaru, da irin kalubalen da ƴan kasuwar Kamaru da diribobi daga ƙasashen biyu ke fadi tashi a kan iyakokin ƙasashen biyu. Ƴan kasuwar ƙasashen biyu na amfana da juna, a wasu manyan hanyoyin 10 da a hukumance aka san da su da suka hada na mota da kuma ruwa.

     

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba......

    Wed, 09 Oct 2024
  • 335 - Najeriya: Yadda ambaliyar ruwa ta kassara tattalin arzikin al'ummar Maiduduri

    Shirin 'Kasuwa A kai Miki Dole' na wannan makon tare da Ahmed Abba ya leka ne jihar Barno da ke arewa maso gabashin Najeriya, inda ya mayar da hankali kan tasarin tattalin arziki da ambaliyar baya-bayan nan ya haifarwa jihar da ma al'ummarta.

    Makonni biyu kenan tun bayan mummunar ambaliyar ruwa da ta afkawa wasu anguwannin birinin maiduguri na jihar Borno da kewaye, a ranar 10 ga wannan watan Satumba, iftila'in da ya haifar da asarar rayuwa da dukiyoyi mai tarin yawa, tare da lalata gidaje da kasuwanni, inda mutane da yawa suke nemi mafaka a wasu sansanonin yan gudun hijara na wucin gadi, yayin da wasu ke gararamba a kan tituna.

    Wed, 25 Sep 2024
Mostrar más episodios