Filtrar por género
- 244 - Kano: Masu ruwa da tsaki sun yi taro don bunƙasa tsarin kiwon dabbobi
Shirin ‘Muhallinka Rayuwarka’ na wannan makon ya yi tattaki zuwa Kano, inda hadin gwiwar Bankin Duniya da Gwamnatin jihar, ya jagoranci taron masu ruwa da tsaki kan kiwon dabbobi, domin inganta fannin ta kyautatawa ko zamanantar da tsarin kiwon dabbobin, samar da abincinsu, da kula da Lafiyarsu, gami da sarrafa madara da naman da suke samarwa.
Sat, 16 Nov 2024 - 243 - Matsalar zaizayewar kasar noma da kiwo a Jamhuriyar NijarSat, 02 Nov 2024
- 242 - Manoman Kamaru sun fara samun tallafin noman dawa mai jure fari
Shirin ‘Muhallinka Rayuwarka’ da ke nazari kan abin da ya shafi muhallli, canjin yanayi, noma da kiwo, ya yi tattaki zuwa Kamaru, inda ya duba shirin tallafa wa manoma wajen noman dawa mai jure fari da kasa mara kyau.
Hukumar kula da samar da albarkatun gona a arewacin Kamaru IRAD ce ke jagorantar aiwatar da shirin na sake fasalin bunkasa noman dawa 'yar rani, wato moskowari.
Sat, 26 Oct 2024 - 241 - Karancin nama da aka shiga a sassa da dama na NajeriyaSat, 19 Oct 2024
- 240 - Babban Taron karawa juna ilimi kan harkokin samar da abinci da bunkasa noma a Jihar Kano
A yau Shirin zai mayar da hankali ne kan wani babban Taron karawa juna ilimi kan harkokin samar da abinci da bunkasa noma a Jihar Kano dake arewacin Najeriya Karkashin kulawar bankin Musulunci da Gidaunaiyar Bill and Melinda da Gidaunaiyar sarki Salman Wanda kungiyar harkokin noma ta SASAKAWA Africa ke jagoranta.
Sat, 12 Oct 2024 - 239 - Kula da lafiyar dabbobi abu mai mahimmanci ga fannin noma da samar da wadataccen abinci
Shirin 'Muhallinka Rayuwarka na wannan makon ya tattauna ne akan yadda gwamnatin jihar Jigawa ta samar da cibiyoyin tafi da gidanka sama da 300, domin kula da lafiyar dabbobi.
Mahukuntan na Jigawa sun kuma samar da wuraren sarrafa nama da kuma madara, matakan da suka sun ɗauka domin bunƙasa harkar kiwo da zummar mayar da shi na zamani.
Sun, 06 Oct 2024 - 238 - Al'adar ''a ci ba daɗi'' na ƙoƙarin kassara manoman Nijar a damunar bana
Shirin Muhallinka rayuwarka tare da Michael Kuduson ya mayar da hankali kan yadda wata al’ada da ake kira ''a ci ba'' dadi da ke zama babbar matsala ga manoma yayin girbin albarkar noma, a cikin wannan shiri za ku ji yadda manoman ke kokawa da yadda wannan al'ada ke kassara su, a wani yanayi da matsi baya ga tsadar kayakin noma ke ci gaba da ta'azzara.
Sat, 28 Sep 2024 - 237 - Dalilan ɓacewar Angulu da Mikiya a kasashe kamar su Jamhuriyar Nijar
Jamhuriyar Nijar inda tsuntsaye irinsu Angulu da Mikiya da ake samu a mayanka da bayan gari, inda ake jefar da gawawwakin dabbobi a yanzu sun zama tarihi. Za mu duba dalilan ɓacewarsu.
Masana a faɗin duniya sun yi ittifakin cewa ɓacewar waɗannan tsuntsaye, musamman ungulu ba karamin koma baya ba ne ga lafiyar muhalli. Kafin mu tafi jihar Maraɗi a Jamhuriyar Nijar, za mu ji ƙarin bayani a game da ungulu da mahimancinsa ga muhalli da lafiyar al’umma, da kuma dalilan da su ka sa su ke ɓacewa daga doron ƙasa, daga bakinmasanin namun daji da abin da ya shafi halayyarsu.
Sat, 14 Sep 2024 - 236 - Mamakon ruwan sama sun haddasa ambaliya a jihar Jigawan Najeriya
Yau shirin zai yada zango a ne a jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin Najeriya, inda mamakon ruwan sama da aka yi a cikin kwanakin da suka gabata ya haddasa ambaliya, lamarin da ya jefa al’umar yankuna da dama cikin halin kaka-ni-ka yi. A bangaren da ya shafi noma kuwa, ambaliyar ta janyo wa manoma ɗimbin asara, wanda ana iya bayyana a matsayin mara misaltuwa, duba da irin halin da suka shiga.
Wed, 11 Sep 2024 - 235 - Yadda feshin magungunan kwari a kayan noma ke yiwa rayuwar bil'adama lahani
Shirin ‘Muhallinka Rayuwarka’ na wannan makon ya mai da hankali ne a kan yadda wani zubin amfani da kayan gona musamman kayan marmari da a kan yi wa feshi ke haddasa matsalolin kamuwa da cututtuka masu lahani ga rayuwar bil'adama, har ma a iya samun rasa rayuka.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Michael Kuduson....
Sun, 01 Sep 2024 - 234 - Gudunmawar da Sarakunan gargajiya ke bai wa ɓangaren Noma a NijarSat, 24 Aug 2024
- 233 - Muhimmancin malaman gona ga manoma a wannan zamani
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan mako ya yi duba ne kan wata hadaka da aka samu tsakanin gwamnatin jihar Kogi da kuma katafaren kamfanin nan na sarrafa amfanin gona a Najeriya Wato OLAM, domin farfado da tsarin aikin Malaman Gona ta hanyar horar da wadanda jihar ke da su tare da kara yawansu a kokarin da bangarorin biyu ke yi na shirya samun ninkin amfanin gonar da za a rinka nomawa a jihar ta Kwara.
Sat, 17 Aug 2024 - 232 - Illar sare itatuwa a wasu yankunan Najeriya,al'amarin a jihar AdamawaSun, 11 Aug 2024
- 231 - Gwamnatin Najeriya ta ɓullo da tsarin biyan haraji kan masu gurbata muhalli
Shirin ‘Muhallinka Rayuwarka’ na wannan mako zai yi dubi ne kan shirin gwamnatin Najeriya na ɓullo da tsarin biyan haraji kan masu gurbata muhalli ta wajen ayyukan da suke gudanarwa, wanda a turance ake kira carbon tax. Kuma ana sa ran wannan harajin zai tursasa wa masana’antu da ke gurbata muhalli yin takatsantsan.
Wannan sabon haraji dai har yanzu ba’a gama tantance jadawalin yadda za’a aiwatar da shi ba, amma kwararru a fannin na ta kira ga jama’a da su yi shirin rungumar sa, bayan da suka ce gwamnati na yin tsare-tsare ne don fito da kowa zai biya haraji daidai da yawan hayaƙi mai gurɓata muhalli da yake fitarwa.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Machael Kuduson.......
Sat, 20 Jul 2024 - 230 - Muhimmancin gandayen daji ga rayuwar jama’a, da ma irin tasirin da suke da shi a rayuwarsu
Allah ya halici wannan duniya tamu da koguna da dazuka wadanda ke taimako ga rayuwar dan Adam ta hanyoyi da dama.
A matakin Nigeria, Allah ya albarkace ta da manyan gandun dazuzzuka da suke da fadi da girma, wadanda suka kunshi nau’o’in tsirrai da mabanbantan dabbobi, wadanda ba a samun su a dazuzzukan da ke wasu yankunan duniya.
Amma wasu daga cikin irin wadannan dazuzzuka kamar Dajin Sambisa a jihar Borno, Dajin Falgore a jihar Kano, da kuma Dajin Birnin Gwari a jihar Kaduna tare da Dajin Kuyambana a jihar Zamfara sai Dajin Zugurma a jihar Neja da kuma Dajin Lame – Burra a cikin jihar Bauchi, a baya sun kasance maboya ga miyagu.
Sat, 06 Jul 2024 - 229 - Rahoton da ya ce an samu hauhawar amfani da makamashi mai gurɓata muhalli a 2023
Shirin wannan zai yi dubi ne kan wani rahoton da ya ce an samu hauhawar amfani da makamashi mai gurɓata muhalli da ma hayaƙin da ke illata muhallai a shekarar 2023. Shirin zai duba tasirin wannan al’amari ga muhalli da ma abin da ake buƙatar ɗan adam ya yi don ci gaba da harkokinsa a cikin wannan sarari na subahana
Wani rahoto a kan makamashi da cibiyar makamashi ta duniya ta fitar ya nuna cewa yawan makamashi mai gurɓata muhalli da aka yi amfani da shi, da kuma hayaƙi mai illa da aka fitar a shekarar 2023 ya kai ƙololuwar da ba a taɓa gani ba, duk kuwa da yadda aka rungumi makamashi mai sabantuwa, mara gurbata muhalli a sassa da dama na duniya.
Sat, 29 Jun 2024 - 228 - An fara samun ci gaba a noman cocoa a Taraba
‘Muhallinka Rayuwarka, shiri ne da ke kawo batutuwan da suka suka shafi muhalli, noma da kiwo, matsalolinsu da kuma masalaha. Duk mako ya ke zuwa muku a wannan tashaa a kuma daidai wannan lokaci, abokinku ne, Michael Kuduson ke muku maraba lale da sauraro.
Yau Shirin namu zai mayar da hankali ne a kan noman koko a tarayyan najeriya.
Sat, 08 Jun 2024 - 227 - A duk shekara Nijar na asarar Eka ko kadadar noma dubu dari sakamakon zaizayewar Ƙasa
‘Muhallinka Rayuwarka’ shiri ne da zai leka Jamhuriyar Nijar, inda wani rahoton ma’aikatar kididdiga ke cewa a duk shekara kasar na asarar Eka ko kadadar noma dubu dari sakamakon zaizayewar Ƙasa da gusowar hamada. Lamarin da ya zama babban koma baya ga ayyukan wadata kasa abinci. Wata matsalar ita ce ta sallacewar kasa da komawarta hako da ba a iya noma a kai.
Sat, 01 Jun 2024 - 226 - Nigeria daya daga cikin kasashe masu noman auguda a nahiyar Afrika da duniya
Shirin a wannan mako zai ba da hankali ne akan noman auduga,
a shekarun baya, Nigeria ta kasance daya daga cikin kasashe masu tinkaho da noman auguda a nahiyar Afrika da duniya baki daya.
Sai dai hankalin mahukuntan kasar ya koma ga bangaren man petur bayanda Allah ya albarkaci kasar da mai.
Jihohin da suka yi fice a noman auduga a kasar, sun hada da Zamfara, Katsina, Kano, Adamawa, Bauchi da kuma Gombe.
Sun, 26 May 2024 - 225 - Matsalar yoyon iskar gas yayi sanadiyyar gurbacewar ruwan sha yankin Delta
Shirin na wannan mako zai yi dubi ne akan yadda al'ummar karamar hukumar Obagi na jihar RIVERS dake yankin NIGER DELTA tarayyar Najeriya suke fama da matsalar yoyon iskar gas sanadiyar fashewar bututun da aka samu tun a watan Yunin shekarar 2023 wanda yayi sanadiyyar gurbacewar ruwan sha, wanda ya sa al'ummar ke kamuwa da cutar amai da gudawa har zuwa wannan lokaci.
Sat, 04 May 2024 - 224 - Matakan da gwamnatin Najeriya ke dauka don magance matsalar tsuntsaye a gonakiSat, 20 Apr 2024
- 223 - Yadda tsananin zafi ya ci karo da lokacin azumin watan Ramadana
Shirin a wannan mako zai ba da hankali ne akan tsananin zafin da ake fama da shi a wasu yankuna na Nahiyar Afirka, a wannan shekarar ya tsananta inda a wasu sassa na tarayyar Najeriya lamarin ya dan wuce misali.
Jihar Sokoto da ke Arewacin Najeriya, jiha ce da tun asali aka sani da tsanantar kowane juyin yanayi na Zafi ko na Sanyin Hunturu ko ma na yawan saukar Ruwan sama.
Sai a latsa alamar sauti domin sauraron shirin.
Sun, 07 Apr 2024 - 222 - Kaddamar da shirin inganta harkokin noma a jihar Niger
Shirin na wanna makon zai yi dubi ne akan katafaren shirin zamanantar da aikin noma da gwamnatin jihar Nejan Najeriya ta kaddamar. Masana na ganin Jihar a matsayin wadda idan aka tattala kasar noma da take da ita, a cikinta kadai za a iya noma abincin da zai iya ciyar da kasar har ma a iya fitarwa zuwa kasashen ketare.
A wannan aikin da aka kaddamar, gwamnatin jihar ta ce ta samar da kayan aikin fasahar noma na zamani tare da tanadar da dabarun noma daga kwararru.
Ku latsa alamar sauti dn sauraron cikakken shirin tare da Nasiru Sani.......
Sun, 31 Mar 2024 - 221 - Najeriya ta kasance kan gaba a fagen noman masara a yankin yammacin Afrika
Shirin wannan mako zai ba da hankali ne a kan yadda Najeriya ta kasance akan gaba a fagen noman masara a daukacin yankin yammacin Afrika, inda kasar ke samar da sama da kashi 48 na masarar da ake nomawa a yankin.
Mafi yawan masarar da ake nomawa a kasar, na fitowa ne daga yankin arewacin kasar, musamman jihohin Bauchi, Kaduna, Borno, Naija da Taraba da kuma wasu ‘yan kalilan din jihohin kudu maso yammacin kasar.
Sat, 23 Mar 2024
Podcasts similares a Muhallinka Rayuwarka
- Al-Quran Al-kareem Al-Quran Al-kareem
- Cakap Masjid Berita Harian Singapura
- Ceramah Habib Novel Alaydrus Ceramah Habib -Novel Alaydrus
- CNN Indonesia CNN Indonesia
- dakwah.me - Ustadz Adi Hidayat dakwahme
- KH ANWAR ZAHID OFFICIAL Dakwah NU
- Riri Cerita Anak Interaktif Educa Studio
- Firanda Andirja Official Firanda Andirja
- Ngaji Bareng Gus Baha Gus Baha
- Hanan Attaki Hanan Attaki
- K.H. ZAINUDDIN MZ K.H. ZAINUDDIN MZ
- Kumpulan Dakwah Islam Lentera Pagi
- Ludruk Cak Kartolo dkk Ludrukan
- Dongeng Kang Ibing Mimin Dongeng
- Murottal Qur'an Terjemahan Audio Indonesia Muslim
- Podcast Dakwah Sunnah podcastdakwahsunnah
- Kumpulan Dakwah Sunnah PodcastSunnah
- M. Quraish Shihab Podcast Quraish Shihab
- Wayang Kulit Indonesia Raden Ontoseno
- Radio Rodja 756 AM Radio Rodja 756AM
- Relaxing Music Relaxing Music
- Spesial Horor Spesial Horor
- Sinau Bareng Cak Nun Telat Cerdas
- Ustad Das'ad Latif Ustad Das'ad Latif
Otros podcasts de Noticias y Politica
- Les Grosses Têtes RTL
- Hondelatte Raconte - Christophe Hondelatte Europe 1
- Entrez dans l'Histoire RTL
- C dans l'air France Télévisions
- Laurent Gerra RTL
- L'œil de Philippe Caverivière RTL
- LEGEND Guillaume Pley
- On marche sur la tête Europe1
- Les récits de Stéphane Bern Europe 1
- Hondelatte Raconte - Cote B Europe 1
- Bercoff dans tous ses états Sud Radio
- L’heure du crime : les archives de Jacques Pradel RTL
- Enquêtes criminelles RTL
- La dernière Radio Nova
- Global News Podcast BBC World Service
- TOCSIN PODCAST TOCSIN MÉDIA
- Culture médias - Thomas Isle Europe 1
- L'Heure des Pros CNEWS
- Pascal Praud et vous Europe 1
- C ce soir France Télévisions