Filtra per genere

Wasanni

Wasanni

RFI Hausa

A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.

600 - Yadda cece-kuce ya mamaye kyautar Ballon d'Or ta 2024
0:00 / 0:00
1x
  • 600 - Yadda cece-kuce ya mamaye kyautar Ballon d'Or ta 2024

    Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan makon ya yi dubi ne akan yadda aka gudanar da bikin bada kyautar Ballon d’Or ta shekarar 2024.

    Mon, 04 Nov 2024
  • 599 - Hukuncin da CAF ta yi kan danbarwar Najeriya da Libya da kuma wasan El-Clasico

    Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon yayi duba ne kan yadda wasan El-Clasico ya gudana da kuma hukuncin da Hukumar Kwallon Ƙafar Afrika CAF tayi kan danbarwar Najeriya da Libya. A ƙarshen mako ne dai kwamin ladaftarwa na hukumar CAF, ya zartar da hukuncin cewa Najeriya ce tayi nasara da ci 3 da nema kan Libya, tare da tarar dala dubu 50.

    Haka nan shirin ya duba yadda wasan El-Clasico ya gudana tsakanin Real Madrid da Barcelona da aka yi a ƙarshen mako.

    Mon, 28 Oct 2024
  • 598 - Danbarwar da ta ɓarke kan wasa tsakanin Najeriya da Libya

    Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci yayi duba ne kan danbarwar da aka samu tsakanin Najeriya da Libya. A makon daya gaba ne dai aka fara kai ruwa rana tsakanin bayan da tawagar Super Eagles ta Najeriya ta yi tattaki zuwa Libya don karawa da takwaransu ta ƙasar a wasa na biyu na neman gurbin zuwa gasar lashe kofin Afrika da za ayi a Morocco a shekara mai zuwa.

    Wannan al’amari dai ya haifar da cece-kuce a duniyar kwallon ƙafar, ganin yadda Super Eagles ta zargi hukumomin kwallon ƙafar Libya da yin watsi da su a filin jirgin sama ba tare da ance kuci kanku ba.

    Ku latsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Khamis Saleh.....

    Mon, 21 Oct 2024
  • 597 - Yadda aka faro kakar gasar Firimiyar Ingila ta bana

    Shirin a wannan makon ya maida hankali ke kan yadda aka faro gasar Firimiyar Ingila, inda akwa yanzu kowace ƙungiya ta samu nasarar buga wasanni 7-7. Tuni gasar ta soma nisa, inda Liverpool take a saman teburi da maki 18, yayinda Arsenal da Manchester City ke biye mata da maki, 17, kowannen su.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh......

    Mon, 14 Oct 2024
  • 596 - Ko komen da Ahmed Musa yayi Kano Pillars zai haifar da ɗa mai ido?

    Shirin Duniyar Wasanni na wannan lokaci yayi duba ne kan komen da Kyaftin din tawagar Najeriya Ahmed Musa ya yi wa tsohon ƙungiyarsa Kano Pillars tare da abokin wasansa Shehu Abdullahi. A karshen makon da muka yi bankwana da shi ne dai ƙungiyar kwallo ƙafa ta Kano Pillars a hukumance ta sanar da kulla yarjejeniyar shekara guda da ƴan wasan.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh......

    Mon, 07 Oct 2024
Mostra altri episodi