Filtra per genere

Muhallinka Rayuwarka

Muhallinka Rayuwarka

RFI Hausa

Wayar da kan jama’a da ilmantar da su, game da sha’anin da ya shafi Noma da muhalli da canjin yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanayi tare da dumamarsa (Yanayi).

243 - Matsalar zaizayewar kasar noma da kiwo a Jamhuriyar Nijar
0:00 / 0:00
1x
  • 243 - Matsalar zaizayewar kasar noma da kiwo a Jamhuriyar Nijar

    A yau shirin zai leka Jamhuriyar Nijar don duba matsalar zaizayewar kasar noma da kiwo da ta jawo yaduwar sakaran gari ko tumbin jaki, wata kalar ciyawa dake mamaye filayen noma da kiwo, kuma dabbobi sam ba sa cin ta, haka ba ta da wani amfani da aka sani ga al’umma.

    Sat, 02 Nov 2024
  • 242 - Manoman Kamaru sun fara samun tallafin noman dawa mai jure fari

    Shirin ‘Muhallinka Rayuwarka’ da ke nazari kan abin da ya shafi muhallli, canjin yanayi, noma da kiwo, ya yi tattaki zuwa Kamaru, inda ya duba shirin tallafa wa manoma wajen noman dawa mai jure fari da kasa mara kyau.

    Hukumar kula da samar da albarkatun gona a arewacin Kamaru IRAD ce ke jagorantar aiwatar da shirin na sake fasalin bunkasa noman dawa 'yar rani, wato moskowari.

    Sat, 26 Oct 2024
  • 241 - Karancin nama da aka shiga a sassa da dama na Najeriya

    Shirin ‘Muhallinka Rayuwarka’ na wannan makon zai mayar da hankali ne a kan matsalar karancin nama da aka shiga a sassa da dama na Najeriya, inda za mu je jihar Adamawa a arewa maso gabashin kasar don jin yadda ake ciki da kuma inda matsalar ta ke.

    Sat, 19 Oct 2024
  • 240 - Babban Taron karawa juna ilimi kan harkokin samar da abinci da bunkasa noma a Jihar Kano

    A yau Shirin zai mayar da hankali ne kan wani babban Taron karawa juna ilimi kan harkokin samar da abinci da bunkasa noma a Jihar Kano dake arewacin Najeriya Karkashin kulawar bankin Musulunci da Gidaunaiyar Bill and Melinda da Gidaunaiyar sarki Salman  Wanda kungiyar harkokin noma ta SASAKAWA Africa ke jagoranta.

    Sat, 12 Oct 2024
  • 239 - Kula da lafiyar dabbobi abu mai mahimmanci ga fannin noma da samar da wadataccen abinci

    Shirin 'Muhallinka Rayuwarka na wannan makon ya tattauna ne akan yadda gwamnatin jihar Jigawa ta samar da cibiyoyin tafi da gidanka sama da 300, domin kula da lafiyar dabbobi.

    Mahukuntan na Jigawa sun kuma samar da wuraren sarrafa nama da kuma madara, matakan da suka sun ɗauka domin bunƙasa harkar kiwo da zummar mayar da shi na zamani.

    Sun, 06 Oct 2024
Mostra altri episodi